Da dariya yabi bayanta har ta kulle k'ofar, ko ince har ta bugo k'ofar, kamal ya dad'e yana kallan wurin da ta b'ace, fuskarshi d'auke da murmushin da baima san yana yi ba, ba abinda yake kauna wani sa'in irin ya ganta a haka, yaga ya k'ular da ita, ya dad'e yana kallon k'ofa sannan can ya juya ya d'auke intercom d'in kusa da shi dan kiran nurse ya nemi sallama, yasan halin matar shi, yasan abunda yayi mata yau ba zai k'ara sawa ta dawo asibitin ba, shi kuma gaskiya bazai iya zama ba in bar bata nan, daman basan jinyar shi take ba yayi mamaki da ta ma daure ta zauna dashi har na kusan tsawan kwana biyu.
Shamsu ne wani yaran shi a office yazo d'aukan shi dan maida shi gida, da kyar suka yarda suka bashi sallama dan aciwar su bai gama warkewa ba, amma sam kamal yak'i jinsu, sai da yayi da gaske har da kiran baban asibitin gaba d'aya sannan suka yarda suka sallame shi, wajan k'arfe tara na dare bayan sun cika shi da magunguna.
Bayan mallam isyaku ya bud'e gate sun shiga, kamal ya fito a hankali, ka ganin shi ya rame amma sai ramar da k'ara mishi wani kyau da kuma sakar fuskar shi itama ramewa, a sanadiyar haka manyan idanunshi suka k'ara fitowa, dogon hancin shi ma haka, ga sajin shi bak'i mai laushi da shima ya k'ara cika fuskar shi, ya k'ara yin haske saboda rashin fitar da bayayi kwana biyu.
Murmushi ya saki wanda duka dimples dinshi sai da suka fito da yaga motar shi a pake a harabar gidan, alamun matar gidan na ciki, a hankali ya fara takwa yana tafiyar kasaitar nan tashi ya bar mallam iskyaku da kwaso kaya, dan already ya sallami shamsu.
Har zai danna doorbell, wata zuciyar tace kawai ya saka key dinshi ya bud'e, kada yaje tana bacci ya tashe ta dan yanzu goma ta wuce, haka ya rarumo key ya saka a wurin muku'lli, ya bud'e a hankali ya shiga tare da yin sallama.
Bayan, ya kullo k'ofar, ya ajiye key d'inshi akan stand d'in dake d'an k'ramin corridor d'in sannan yayi hanyar parlor, yana shiga ya tsaya cak, ko taku uku baiyi ba a cikin parlon, yaji gaban shi yayi wani irin mummunar fad'uwa, zuciayr shi ta fara bugawa kamar zata tsage daga k'irjin shi, bin abinda ke gaban shi yayi da kallo, matar shi ce a tsaye, cikin bum short da wata half vest, gashin kanta me yawa na pake a tsakiyar kanta, remote d'in tv a hannunta d'aya wani bowl mai d'auke da popcorn a hannunta d'aya, ya dad'e yana k'are mata kallo sai can yayi suarin lumshe manyan idanun shi da suka fara komawa jajaye, ganinta da yayi a haka ya fara harda sa mishi jin abubuwa daban, surar jikinta da ta bayyana sanadiyar kayan da ke jikinta ya saka hankalin shi na neman tashi, sai da ya nustu sosai ya bud'e idanunshi.
Itama tana tsaya, kwayar idanunta cikin nashi, manyan idanunta ta ta zaro waje, ya kasa ganewa, mamakin ganin shi take ko kuma tsoron yarda ya ganta a yanayin da take.
Ta d'anyi y'an sakwani a haka, sai kuma can a hankali ta mai da idanunta kan jikinta, ta k'ara ganin yarda take, a hankali ta k'ar d'auke su daga jikinta ta maida kan kamal, wanda yanzu murmushi na d'auke akan fuskar dan yarda tayi a wurin ya kusa saka shi tuntsirewa da dariya.
Sakeena gaba d'aya ta saki abun hannunta sannan da mahaukacin gudu tayi cikin d'akin ta, tare da banko k'ofa da saka muk'ulli, dariyar da bayan sanyi ya saki baima san lokacin ba, tare da bin k'ofar da kallo.
Ya dad'e baiga me saka shi cikin nishad'i ba kamar ta, gaskiya ta cire cuta, dan kusan kullum sai ta fito da wani side d'inshi da baima san yana dashi ba, yau ta saka shi fushi yaji kamar yayi hauka, gobe da saka shi cikin nishad'i da jin dad'i, ya dad'e yana bin k'ofar d'akinta da kallo sannan can ya girgiza kanshi tare da yin hanyar nashi bedroom d'in.
Sai da ya had'a ruwan wanka mai zafi sannan ya kwara a jikinshi domin gasa jikinshi, dan ko
Ina ciwo yake mishi sanadiyar rashin lafiyar shi, yana gama abinda ya zaman mishi al'ada ya fad'a kan gado, danyin bacci, ya dad'e bai rintsa ba, a sanadiyar tunanin da suka yi mishi yawa, baban abinda ya hardasa mishi tunanin ba bai wuce matar shi ba da take a d'akin kusa da shi, ji yayi kawai yana san ya jita a kusa dashi, ji yayi a lokacin bazai iya bacci ba in har bai jita k'ank'ame a jikinshi ba, lumshe manyan idanunshi yayi da wani b'ari na zuciyar shi ya shawarce shi da ya tashi yaje wurin ta, ya tabbata ya biye ma zuciyar shi a lokacin sai yi abunda zai saki shi yin dana sani, kamal da kyar ya iya samun bacci har sai dan da asuba.
ESTÁS LEYENDO
ZAFIN RABO ✔️
RomanceLabari ne da ya k'unshi tsana, k'iyayyaya, mugunta, da uwa uba soyayya. Ku biyo ni kuji me zai faru a littafin //Zafin Rabo//