March 31, 2020
JINI YA TSAGA......👭
®NWA
Haƙƙin Mallakata
(OUM-NASS)PAGE 17
Ga masu buƙatar wannan littafin akan lokaci, za su iya shiga wanan link ɗin. Please idan kin san ba zaki yi cmnts a kansa ba dan Allah ki zauna a inda kike. Littafina kyauta ne cmnts ɗinku shine yiyuwar ɗorewar sa.
https://chat.whatsapp.com/IqPTmfV5sPQ3OsQtvitSEm
***
"Yaushe kika zama malamar halayyar ɗan Adam Adda Halima? Asanina dai da ke, ke matar Sayyadi Ƙasim ce ban sani ba ko kin koma ..."
"Hafsa ba fa shirme na ke magana a kai ba. Ko ma ya nake kin sani ni ce mace mafi kusanci da ke, da kuma sanin halayyarki." Adda Halima ta faɗa tana matse fuska da kafe Hafsan da idanuwanta.
Murmushi Hafsa ta yi, sannan ta ɗauki hannun Adda Halima ta haɗe da nata tana matsawa "A cikin ko wata rayuwa ta ɗan Adam akwai sauye-sauye na warwarar zaren da ke cure ga labarinsa.
Wani kan zama sauyi mai kyau da samar da kyakkyawar rayuwa ta har abada ga wannan mutumin. Wata kuma takan warware masa munanan burukan da ke danƙare a cikin duhuwar zuciyarsa.
Gaskiya kan yi kokawa da zama mai nasara a lokacin da take fatattakar ƙarya, gaskiyar da kan sa idanuwa su buɗe, zuciya ta karɓeta a lokacin da ta bata shirya ba."
Murmushi ta yi tana sauƙe ajiyar zuciya a kare na biyu "Kun daɗe kuna faɗa min Hafsa kin yi sa'a kin auri miji ɗaya da ɗaya. A lokacin ban ji hakan a raina ba, ban yarda cewa Abdul ya kai mijin da zan iya shimfiɗa rayuwata a tare da shi ba, har yanzu ina jin kuma hakan a zuciyata.
Sai dai na sani, babu inda hakan zai kai ni, babu nasarar da zan cimma ga hakan face faɗuwa. Tun ina ƙarama ake karantar da ni akan ƙaddara, hakan ya sa na fara rubutu akan yanda ƙaddarata zata same ni.
Zan zauna da Abdul, zan zauna da shi har sai kun ji a ranku na zauna da shi. Zan wadata fuskata da murmushi koda ace a zuciyata akwai ƙuna. Zan sa shi ya yi dariya har sautin dariyarsa ya ratsa kunnuwan da ke kusa da shi.
Sai dai ban san kuma mai gobe zata haifar ba, ban san ko hakan zai tabbata har ƙarshen rayuwa ba. Amma zan yi abin da zan iya yi Adda Halima."
Ta ƙarasa maganar tana zame hannunta daga na Adda Haliman, a karo na biyu tana murza gashin girarta da shimfiɗa murmushi akan fuskarta.
Kallonta Adda Halima ta yi, a yayin da take haɗa maganarta tana mai-maita su a zuciyarta, da kuma son ajiye ko wacce a muhallinta da ya dace.
Ta riga da ta san wacece Hafsa, bata buƙatar a faɗa mata ko me a game da ita, ta san me wannan sosa girar ke nufi, duk lokacin da ta taɓa girarta zata yi haƙo mai zurfin da zai zurma wanda ke kusa da ita.
Murmushi ta yi tana girgiza kanta, kafin ta yi magan Khadija suka shigo ɗakin da Anty Lubabatu "Lokaci ya tafi Adda Halima, ya kamata mu tafi gida mu fata haɗa na mu komatsan mu koma tamu nahiyar." Khadija ta faɗa tana kallon su da yawata idanuwanta a ɗakin."Oh ni Khadija, ashe akwai ranar da zan shigo ɗakin Hafcy naji ƙamshi na tashi ta ko ina?"
"Kin dai san dama baki taɓa tarar da nawa ɗakin da dattiba ko a lokacin da nake gida ne Anty K." Ta yi maganar tana ƙarfafa K ɗin.Kanne ido ɗaya Khadija ta yi "Wato ba zaki raba kanki da kirana da wanan sunan ba ko Hafsa? Ni na rasa inda ma aka yi kika raina ni wallahi."
Kai Hafsa ta risina tana haɗe hannu "Allah ya huci zuciyar babbar yaya, matar Dakta Suraj Sayyid."
Duka ta kai mata ta yi saurin zamewa suna sa dariya a tare.
"Ba zaki sauya ba sam Hafsa." Anty Lubabatu ta faɗa tana dariya.
"Zan sauya Anty Lubbie! Har sai da kanku kun ce Anya wannan Hafsan Umma ce."
"Ban ga wannan ranar ba sam." Khadija ta faɗa tana taɓe baki da sake kallon agogon hannunta.
"Adda Halima mu tafi ko?" Ta yi maganar tana kwantar da kanta.
Tashi Adda Haliman ta yi tana kallon Hafsa "To ƙanwa mu zamu tafi, za mu tafi da fatan alkhairai masu yawa a gareki, zamu tafi da tabbacin mun barki da kyakkyawan murmushi akan fuskarki.
Za mu bada labarin abin da idanuwanmu suka gane mana, sai dai.."
Ta yi shuru kafin ta tausasa muryarta a hankali yanda ita kaɗai zata ji "Ba zan yi hasashen abin da kike shiryawa ba, domin kina haƙa ne ki binne ba tare da idanuwa sun ankare da hakan ba.
Sai dai akwai ban-banci da tazara mai yawa tsakanin wancan haƙar da kika saba yi. Wannan idan kika yi ƙurar zata bibiyi rayuwarki ne har abada, zata yi ta buɗeki a yayin da hazonta zai gallabi rayuwarki.
Ki yi abin da kike son yi, amma kada ki yi wanda zai zame miki tambarin shahara marar alƙibila."
Ta yi magana tana shafa gefen fuskarta da kuma rungumeta "Allah ya miki albarka ya kare rayuwarki."
Tana gama faɗar haka ta zame jikinta ta yi gaba ba tare da ta waiwayo ba. Tana jin taruwar hawaye a idanuwanta, hawayen da bata san ko na me ye ba, sai dai tana jin wani tsoro na huda zuciyarta.
Itama Hafsat da kallo ta bi su, tana jin maganar Adda Halima na mata yawo a rai da zuciyarta 'Me yasa kowa ya ke cewa ta yi Abin da ta ke so?' A hankali ta cira ƙafarta zuwa gaban mudubin da ke ɗakin, tana ƙarewa fuskarta kallo, ganin zata ɓata lokaci ta ɗebi kayan kwalliya da turaruka ta fita a ƙofar gida ta samu wasu wasunsu na zauren gidan.
Aysha ta kira ta miƙa mata kayan kwalliyar.
"Na gode sosai. Allah ya ƙara zumunci." Ta faɗa da shimfiɗaɗɗen murmushi tana ɗaga musu hannu.
Har zuwa lokacin da suka ɓace a kan idanunta.
YOU ARE READING
JINI YA TSAGA
AksiBa son ko wano uba bane samun balagurbi acikin ahalinsa, sai dai sau da dama ALLAH kan jarrabi bayinsa ta hanyoyi da dama. Duk da kasancewarsa babban Malami agarin hakan bai hana ya samu ta waya wajan gaza daqusar da mutum ɗaya tilo acikin ahalin sa...