UKU

853 75 0
                                    

JINI YA TSAGA.....! 👭

©By 😘UmNass🏇

PAGE 3

"Turƙashi! Tsugunno bai ƙare min ba kenan." Hafsa ta faɗa tana bin bayan Umman su da kallo, kafin nan ta taɓe baki ta ɗaga kafaɗa wanda yake nuna hakan ko ajikin ta.

Can kuma sai ta tuntsure da dariya "Wato ita Umma har gida ta samu na aure da take iƙirarin zan kashe mata aure. Adai wanan gidan mai cike da ihun yara da tarkace banga amfanin zama ba, dan da alama ko barcin safe ba'a samu ayi balle a rintsa." ita kaɗai take magana tana jijjiga kai.
Tashi tayi ta gyara zaman hijabinta tana ƙokarin jan jakarta, sai ga ɗaya daga cikin abokan zaman Umma ta kawo musu abinci da abin sha.

"A'a Maman Bunayya ya naga kina shirin tafiya? Kaddai kice min yanzu zaki juya?"
Murmushi ta sauƙar akan fuskarta wanda shike ɓoye ko wani mugun hali da tugunta "Aikuwa dai tafiya Zanyi Mama, dama ahanya nake na raɓo tanan mu gaisa, bana son dare yamin kuma ahanya."

"Banda abinki dare ai ya riga daya gama yi miki, yanzu zakiga an fara kiran sallahr almuru. Da dai zaki bi shawarata da kinyi haƙuri kin kwana Allah basshi gobe sai ki tafi da safe. Ga abinci da ruwa kuci."

Kallon abincin tayi ta fara yamutsa fuska, itafa dama ba zuwa garin nan ba, tarkacan abokanan zaman Umman ta da suke da ɗan banzan shisshigi wadda take ganin ta kamar Kissa ce, daɗin daɗawa ba girki suka iya mai ɗan-ɗano ba, duk sanda tazo idan ba Umma keda girki ba to haka take ƙare yininta ta koma gida, su kuma kamar kansu ya toshe da rashin ganin hakan, dan naci kullum sai sun kawo mata.

"Nikam aƙoshe nake Mama, dan ahanya naci abinci, daga Jega nake kinga tazarar babu yawa balle asamu gajiya da yunwa atare dani." ta ƙarasa maganar cikin fara'a da duba agogon dake wayar ta.

"Duk da haka yaranki zasu buƙaci hakan, musamman Ummi."

"Ya Allah!" ta faɗa aƙasan maƙoshin ta.

"Ki bar ɓata lokacinki Maman yara akan Hafsa, tunda ta miƙe tsaye ba zata zauna ba." Umma ta faɗa tana ɗan murmushi akan fuskarta.

"Aifa nasan halin har yanzu yana nan ashe?"
"Ai babu fashi." Umma ta bata amsa tana murmushin da ganinsa na yaƙe ne.
Daga haka Maman yara ta tattara abincin ta koma da shi.
Sai alokacin Mama ta kalli Hafsa cikin tamke fuska "Kibar Sadiya anan ke sai ki tafi yawon duniyar taki."

Kallon Umma tayi kana ta kai kallonta ga Ummi wanda ainihin sunanta Sadiya kasancewar sunan Adda Halima gareta shi yasa aka mata alkunya da sunan Ummi kasancewar ta babbar yaya mariƙiyar ta wadda tasu tafi zuwa ɗaya aduk gidansu.

"A ina zan barta Umma?" ta aika tambayar cikin mamaki.

"Anan waje nah mana, ina zaki tafi da yara kina gararamba agari."

Dariya tayi mai sauti cikin muryar ta ta shaƙiyanci ta fara magana "Haba Umma! Kema da araɓike kike agidan taya zan bar ɗiyata tayi zaman agolanci agidan wani, wanin ma ba da Uwarta ba da kakarta, ai agolanci ya kai ƙololuwa. Indai zan barta anan to na kaita wajan ubanta mana, inda iyaka abata kashi amma baza'a mata gorin agolanci ba. Ke ɗin dai Umma ki zauna abinki cikin gidan auren da bazaki fita ba bazaki koka ba."
Tana gama faɗar haka ta ja hannun Ummi suka fice aɗakin, rasa abin da Umma zata faɗa mata tayi sai kai data girgiza tana nema mata Addu'ar shariya awajan Allah.
"Halayyarki sai ke Hafsa, kulum sabbin shafika kike buɗewa waɗanda suke marasa alfanu da amfanarwa. Allah ya shiryeki ya ganar dake gaskiya." maganar da tayi tana share hawayen da yake sauƙa akan fuskar ta.

Wannan itace Jarrabawarsu itace kuma ƙuncinsu arayuwa. Jarrabawa mai wahala akan yara da kuma soyayyarsu ga iyaye.

*****
Tana fita bata zarce ko inaba sai tasha kai tsaye motar SOKOTO ta shiga.

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now