GOMA SHA BIYAR

279 36 6
                                    

March 23, 2020

JINI YA TSAGA......👭

®NWA

Haƙƙin mallakata
(OUM-NASS)

Free book 💃

PAGE 15

Ga masu buƙatar wannan littafin akan lokaci, za su iya shiga wanan link ɗin. Please idan kin san ba zaki yi cmnts a kansa ba dan Allah ki zauna a inda kike. Littafina kyauta ne cmnts ɗinku shine yiyuwar ɗorewar sa.

https://chat.whatsapp.com/IqPTmfV5sPQ3OsQtvitSEm

Girmamawa.

🌷🌹🌷🌹🌷

Ya ɗauki lokaci mai tsawo yana zaune yana maida numfashi, kafin daga baya ya tashi yana riƙe da mararsa da ta ƙulle tun bayan zagaye masa fuskar da Hafsat ta ke yi.

A hankali ya shiga ɗakinsa ya kwanta a kan gado, jin zuffa na jiƙa ƙara tsattsafo masa daga jikinsa ya sha ya shiga toilet ya sakawar kansa ruwa. Ajiyar zuciya ya sauƙe mai ƙarfi, jin ruwan na huda ko wata ƙofa ta jikinsa.

Murmushi ya yi a lokacin da idanuwansa suka shiga hasko masa abin da ya faru tsakaninsa da Hafsa 'Hafsa rigima.' Ya faɗa a ƙasan laɓɓansa yana shafa sajen fuskarsa.

Shi har mamakinta ya ke yi, da ace ba shi ne ya ɓareta gal a leda ba da babu abin da zai hana shi ya yi tunanin ta yi zama da gogaggu mata fitinannun da ba sa jin magana.
Sai dai ya riga da ya san ko ita wacece da kuma gidan da ya ɗauko ta.

A hankali ya fito daga toilet daga shi sai farin tawul da ke sarƙafe a ƙugunsa, farar jallabiya ya sa a jikinsa sanan ya mayar da tawul ɗin ma'ajiyarsa sannan ya dawo ya shimfiɗa sallaya ya gabatar da sallah nafila kafin ya kwanta.

Bayan ya idar ya fara karatu daga kan abin sallar barci ya ɗauke shi, barci mai ciki da takura da mafarkai marasa kan gado.

*****
Washe gari kiran sallahr assalatu ne ya farkar da shi, hakan ya sa ya tashi, yayi mamakin ganin in da ya kwana ko ina na jikinsa yana masa ciwo.
A gaggauce ya shiga toilet ya yi wanka sannan ya ɗaura alwala ya fita masallaci, ya so tsayawa a ƙofar ɗakin Hafsat amma yasan zai iya ɓata lokacinsa ne a iska har shima ya makara.
Kasancewar shine limamin masallacin unguwar yana zuwa ya jagoranci sallah.
Bayan ya idar sai da ya tsaya ya musu wa'azi akan abin da ya shafi rayuwa kamar yanda ya saba yi musu.
Ƙarfe shida da rabi aka shafa fatiha kowa ya kama gabansa, shima ya taho gida, yana taku zuciyarsa na bugawa, saboda tunanin wata kalar sabuwar masifar kuma yau zai tadda.

Sai dai da mamakinsa tun daga falon nasu ya ke jiyo sautin karatun Alqur'ani mai girma, da wata zazzaƙar muryar da yake jin tana amsa ko wani sashe na jikinsa.
"Ya Allah! Wannan wani sauti ne mai daɗin gaske haka?" Ya samu faɗa a ƙasan laɓɓansa, a hankali kuma ya fara cira takunsa yana nufar inda ya ke jin sautin na ta shi.
Ɗakin Hafsat ya nufa da ya ke jin sautin na ta shi, murɗa ƙofar ɗakin ya yi cikin sa'a ƙofar ta buɗe hakan ya sa ya cusa kan sa ɗakin.

Tsayawa ya yi yana wara idanuwansa, ganin Hafsat ce zaune akan abin sallah idanuwanta a lumshe ta jingina da jikin gado tana zazzaga ƙira'ar karatun ba tare da ta buɗe alqur'anin ba.

Idonsa ya murza da tafukan hannunsa ya ƙara ganin tabbas dai HAFSA ɗin ce ke hadda da ka. Ajiyar zuciya ya sauƙe a karo na farko mai sanyi, yana jin wani abu na ɗarsuwa tun daga yatsan ƙafarsa har zuwa kansa.
"Alhamdulillah ala kullu halin! Masha Allah!" Su ne kalmomin da ya shiga mai-maitawa, yana ɗaga ƙafarsa da matsowa kusa da ita.
A jikinta ta ji cewar ana kallonta, ƙamshin turarensa kuma ya sanar da ita shi ɗin ne dai ya dawo.
A hankali ta buɗe idanuwanta tana ɗora su a kansa, ganin ya ƙura mata ido yana murmushi da kuma lumshe idanuwansa a kai-akai ya sata ambaton "Sadaƙallahul Azim."

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now