March 25, 2020
JINI YA TSAGA......👭
®NWA
Haƙƙin Mallakata
(OUM-NASS)PAGE 16
Ga masu buƙatar wannan littafin akan lokaci, za su iya shiga wanan link ɗin. Please idan kin san ba zaki yi cmnts a kansa ba dan Allah ki zauna a inda kike. Littafina kyauta ne cmnts ɗinku shine yiyuwar ɗorewar sa.
https://chat.whatsapp.com/IqPTmfV5sPQ3OsQtvitSEm
***
Ajiyar zuciya ya sauƙe yana a hankali, yana ƙoƙarin dai-daita zamansa a kan kujerar.
"Na gode Matata!" Ya samu bakinsa da faɗar hakan a hankali, har a lokacin yana jin wani abu na yawo a kansa.
"Baka gajiya da gode min ne?" Ta tambaye shi a lokacin da ta ke zuba masa soyayyan dankali da ƙwai a file ɗin da ta ajiye a gabansa."Kin taɓa ganin mutum ya gaji da da jin sautin bugawar zuciyarsa?"
Murmushi ta yi bayan ta haɗa masa shayin ta kurɓa, ta ji zafin ya yi dai-dai kana ta ajiye masa.
Zama ta yi akan kujerar kusa da shi, sanan ta sa cokali ta ɗauki dankalin da kwai ta kai bakinta, sai da ta haɗiye ta ƙara ɗiban wani.
Sannan ta ajiye masa cokalin "Bismillah Ya sayyadi!""Na ɗauka za ki ba ni ne a baki ai!" Ya yi maganar yana lumshe idanuwansa da sauƙe shi a kan fuskarta.
Dariya ta yi mai sauti wanda ta sa ya ƙura mata ido, yana jin sautin zuciyarsa na ƙara bugawa, yana jin wani farin ciki na lulluɓai shi.
Bai san lokacin da ya yi murmushi ba "Kina da kyau a lokacin da kike dariya Nahna!"Fuskarta ta tsuke, sai dai har a lokacin da murmushi a fuskarta "Ko me nawa yana da kyau a tare da ni Abdul-Mannan. Shi yasa na ke ta musamman."
Kai ya girgiza sannan ya ɗebi abinci ya kai bakinsa "Wannan fa alfahari ne da yawa, kuma kin san babu kyau."Kai ta girgiza tana taɓe bakinta "Ni'imar da aka min dai na ke yabawa, na ke kuma magana a kanta. Kamar dai yanda Allah s.w.a ya ce mu bada labarin ni'imar da ya mana."
"Ta ki ya wuce labari Nahna! Ji da kai ne."
Idanuwanta ta wara tana wurga su gefe "To idan ban ji da kai na ba, da wa zan ji?""Ki ji da ni kawai!" Ya yi maganar yana ƙoƙarin gimtse dariyarsa.
"Hehehe! Wai almara kenan! Adadin wani lokaci kake so na ji da kai Abdul?"Ta yi maganar tana ɗora hannunta a kan nasa "Har ƙarshen rayuwa!" Yayi maganar yana ɗora idonsa a kanta, janye idanuwanta ta yi daga nasa, domin tana jin kaifinsu na ƙoƙarin yi mata illa. Akwai abin da ta ke so, akwai abin da ta ke shiryawa.
"Zan baka shekaru huɗu na rayuwata! Zan ƙawata ma ka su da baka ko wata kulawa a cikinsu! Bayan su kuma?"
"Me ya sa ba zai zama har abada ba! Me yasa shekaru huɗu kawai Nahna?"
Ya yi maganar yana ture filet ɗin daga gabansa, yana kafeta da idanuwansa, da ruwa ya taru a cikinsa.Murmushi ta yi tana sosa girarta da babban yatsanta, daga bisani kuma ta ɗauko hanunta ta ɗora a tafin hannunta sanan ta sake ɗora nata hannun a kansa. Ya zama nasa hannun na tsakiyar ta sa.
"Su ne adadin lokacin da nake da tabbaci akanka. Akwai ƙaddara da kan yi rubutu ga rayuwar kowa, ta iyu ƙaddararka ta zama mai ƙarfi. Ni kuma ina ƙoƙarin rubuta labarina a cikin taka ƙaddarar.
Shekaru huɗu sun min yawa akan tanadin da nake da shi, daga baya kuma na fahimci cikar burinka zai taimakawa alƙalamina wajen yin rubutun da babu gargada.
Ni mallakinka ce da dukkanin abin da kake so a tare da ni. Har zuwa wannan lokacin zan zama magijin da makunnarsa ke riƙe a hannunka. Ba zan ce komi ba, ba zan ƙi komi ba, muddum kai zaka so shi, kamar yanda zaka faɗa."
![](https://img.wattpad.com/cover/182867269-288-k153520.jpg)
YOU ARE READING
JINI YA TSAGA
ActionBa son ko wano uba bane samun balagurbi acikin ahalinsa, sai dai sau da dama ALLAH kan jarrabi bayinsa ta hanyoyi da dama. Duk da kasancewarsa babban Malami agarin hakan bai hana ya samu ta waya wajan gaza daqusar da mutum ɗaya tilo acikin ahalin sa...