GOMA SHA TAKWAS

363 45 7
                                        

May 2

JINI YA TSAGA....👭

®NWA

©OUM-NASS

*Assalama alaikum! Barkanmu da wannan lokacin ƴan uwa, fatan mun yi sallah lafiya. Allah ya karɓi ibadunmu yasa mai lada muka yi. To gamu dai mun sake waiwayowa ina fatan wannan waiwayen da na yi zai kai ni gaci ga ƙarƙare labarin ba tare da jinkiri ko tsaiko ba*
_*Na yaba ina kuma ƙara jinjinawa da girmamawa ga duk wanda yake bibiyar wannan rubutun nawa. Hakan yasa na tilastawa kaina ajiye kalmar girmamawata a gareku a cikin ko wani shafi. Na gode.*_

PAGE 18

Tun bayan tafiyar su Adda Halima take zaune a falonta, kanta ta jingine a saman kujera kalaman Adda Halima na dawo mata kamar a lokacin take faɗa mata.
Ta sani a duk duniya babu wanda ke da kusanci da ita da sanin halayyarta sama da Adda Halima, kamar yanda ita kaɗai ce zata bigi ƙirji tace tana mata tsananin so na mutuwa.
'Ki yi abin da kike so!' Maganarta ta sake dukan kunnuwanta kamar a lokacin take faɗa mata.
_'Ba zan yi hasashen abin da kike shiryawa ba, domin kina haƙa ne ki binne ba tare da idanuwa sun ankare da hakan ba._
_Sai dai akwai ban-banci da tazara mai yawa tsakanin wancan haƙar da kika saba yi. Wannan idan kika yi ƙurar zata bibiyi rayuwarki ne har abada, zata yi ta buɗeki a yayin da hazonta zai gallabi rayuwarki._
_Ki yi abin da kike son yi, amma kada ki yi wanda zai zame miki tambarin shahara marar alƙibila.'_

Maganar Adda Haliman ta sake dawowa kunnenta, maganarta ta ƙarshe da ta faɗa mata.
Ƙananun idanuwanta ta sake buɗewa tana yalawata su a falon, kafin ta yi murmushi mai zurfi.
"Babu ƙurar da zata dawo ta buɗeni Adda Halima, zan yi rayuwar da na tsarawa kaina, zan kuma yi nasara a kan hakan.
Bana son Abdul baku saurare ni ba, dan haka zan gasa zuciyarsa cikin sauƙi, ba iya shi kaɗai ba har da duk wanda ke tare da shi."
Ta ƙarasa maganar tana ƙara yalwata murmushi a kan fuskarta.

Daga bisani ta tashi ta shiga kitchen dan gabatar musu da abincin dare. ta daɗe tana nazarin abin da zata girka, itafa ƴar gargajiyace tana son ta ci tuwo a duk daren duniya, tuwon ma na laushi da miyar bushasshiyar kuɓewa ko kuma kuka.
Sai dai babu garin masara da na gero, gashi lokaci ya tafi. Ganin semovita yasa ta sauƙe ajiyar zuciya.
"Da dama dai, wai a dole sai an mayarka ɗan gayu." Ta yi maganar tana murmushi sannan ta yi girkin.
Bayan ta yi haɗin lemon kan-kana wadda ta haɗa mata ƙarin madara da sugar a kai, sai lemon tsamin da ta zuba kaɗan.
Ta jefa ƙanƙara sannan ta saka shi a firji. Sai da ta gyara komi da ta ɓata sannan ta share gidan da sa turaren ƙamshi. Ta shige toilet ta yi wanka, yau kam ta ɓata lokaci a gaban madubi tana ƙyale-ƙyalen fuskarta.
Wajen zaɓen kaya ma sai da ta ɗauki lokaci tana neman wanda zata sa, kafin ta ɗauki wani material baƙi mai zanen fulawoyi farare. Kasancewarta fara sai kayan ya amsheta sosai ta daɗe tana juyawa a gaban mudubi sannan ta feshe jikinta da turaruka masu yawa.
A hankali ta lumshe idonta ta sake buɗe su, sai kuma ta jiyo da zummar barin ɗakin idanuwanta suka sauƙa akan na Abdulmannan ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallonta da murmushi a kan fuskarsa.
Ƙananun idonta ta shiga wurgawa tana ƙara takunta da ƙawata shi ta hanyar rausaya jikin a ko ina. Ko wani taku da ta yi sai jikinta ya yi rawa.
Ido Abdul ya lumshe yana buɗewa a kanta, hakan ya zama wata ɗabi'a a gareshi, har ta zo kusa da shi yana kallonta.
Juyawa ta shiga yi a gabansa, tana wara hannunta da kuma ɗorasu a ƙugunta, tana karkacewa daga tsaye.
"Ya kaga kwalliyar tawa?"
Murmushi ya yi yana sauƙe hannunsa daga harɗesun da ya yi "Masha Allah ta yi kyau."
Ya faɗa yana jinjina hannunsa.
ƙananun idonta ta kanne ciki "Ta yi kyau kace fa? Ba ma ni ce na yi kyau ɗin ba?"

"Kwalliyar kika tambaye ni ba ke ba ai!" Ya yi maganar yana lumshe idanuwansa.
"Ina jin yunwa." Ya yi maganar yana shafa cikinsa da juyawa da zummar barin ɗakin.

Gabansa ta sha tana yamutsa fuskarta da sosa girarta guda, tana murmushi "Faɗa min gaskiya dai Sayyadi Abdul! Idanuwanka na rawa da yawa kamar yanda ƙafafuwanka suke yi. Mafi girman al'amarin jirkicewar idanuwanka daga launinsu." Ta yi maganar tana kanne idonta ɗaya, daga bisani ta matso da bakinta saitin idonsa ta hura masa iskar bakinta.
Idon ya lumshe a karo na ba adadi, yana murmushi sai dai kafin ya yi magana ya tsinkayi yatsanta ɗaya tana zagaya ƙwayar idon nasa.
'Ya Allah!' Ya faɗa a ƙasan zuciyarsa yana jin wani abu na harbawa tun daga kansa har zuwa yatsansa.
Riƙe hannun nata ya yi yana buɗe idonsa a hankali wanda ya sake faɗawa ciki.
"Rigimarki tana da yawa Nahna!" Ya samu bakinsa da faɗar hakan.
"Na sani Sayyadi, bana so ka na ɓoye zahirinka ne, ka faɗi abin da kake son faɗa kawai." Ta yi maganar har a lokacin hannunta na zagaye da fuskarsa tana zagaya sajensa.
"Ina son wannan zagayayyen gashin da ke fuskarka."
Ɗaukanta ya yi ciɗak ya tafi da kan gadon ya ajiyeta.
"Me zaka yi Abdul? Ba dai kwalliyar tawa zaka ɓata min ba?" Ta samu kanta da faɗa.

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now