HAƘƘIN MALLAKA
August 6, 2019
JINI YA TSAGA....! 👭
©BY 😘OUM_NASS 🏇🏽
®NAGARTA WRI. ASSOCIATION
_*Wannan shafin Sadaukarwa ne gareki MARYAMERH ABDUL KWAISEH*_
page 6
Ido Umma ta lumshe tana cilla tunaninta a shekarar da ta sabunta labarinta, ta raba tsakaninta da yaranta.
25,Mayu 2001
"Salamatu, yau ba zan sakaya na kiraki da sunan da ba wanda iyayenki suka raɗa miki ba.
Dan kina matsayin uwar gidan Alhaji hakan ba yana nuna zaki na mulkarmu bane. Daga rana mai kamar ta yau, bana buƙatar ki sanya kasafin abincinki da ni."Ɗagowa Salamatu tayi fuskarta ƙunshe da murmushi ta kalli mai maganar "Wanan ra'ayinki ne ai Kandala, amma ni ba'a min iyaka akan hana wata abinci da kuma bawa wata ba.
Zan sauƙe nauyin da yake kaina kawai."Tsaki Kandala tayi da ƙarfi tana kyaɓe baki "Andai faɗi ba nauyi, idan kin haifu a cikin tsoho da tsohuwa masu dattin hula kada ki ƙara yin kasafin abinci da ni.
Idan kuma tsintacciya daga sama ce zanga zahiri daga lokacin da na shigo cikin ƙidayar lissafin ki."
Ɗagowa Salamatu tayi idanuwanta sun rine da kalar ja, wanda yake nuna tsan-tsar ɓacin ranta a bayyane.
"Ni kuma zan tabbatar miki da cewar na haifu a cikin iyayena.
Daga yanzu na haramta ma kaina yin abinci da ke da yaranki."
Tana gama faɗar haka ta jefa mata ƙatuwar kular da ake zuba mata abinci ita da yara.Guɗa Kandala tayi tana kiran "Tafi nono fari." Ta ɗauki abarta ta ƙara gaba.
Da ido Salamatu ta bita da kallo. Tabbas Kandala fitinanniya ce, haka kuma mace ce mai iya sharri da ƙwarewa a kaidi irin na mungwagen mata.
Sai dai tana roƙon Allah da ya mata tsari da ko wani kaidi irin nata.BAYAN SA'A BAKWAI
Lokaci ne da Alhaji malam yake zama suna taɗi da iyalansa, anan kuma yake fuskantar matsalar da yaransa suke ciki da matansa dan a warware ta.
Bayan an gabatar masa da abincinsa, kafin yayi tunanin fara ci yaran Kandala da su uku suka kewaye shi suna kiran "Alhaji muma zamu ci"
Da mamaki ya kallesu kafin ya ɗora da tambayar su "Ba kun ci naku abincin ba?"
Kai suka girgiza kafin ƙaramar cikinsu da bata fi shekara huɗu ba tace "Yau duka bamu ci abinci ba. Umma taƙi bamu."
Jin ta kira sunan Umma yasan cewar Salamatu ce tayi girkin ranar. Amma yaushe Salamatu ta rabu da kyawawan ɗabi'un da ya santa da su, har take yima yara ƙanana horon yunwa? Abin da ba tayi a lokacin ƙuruciyarta ba shine yanzu zatayi.
"Bazan juri hakanba ko kaɗan."
Ya faɗa a fili yana tura ma yaran abincin gabansa.
Abin tausayi ganin sun shiga ci hannu baka hannu ƙwarya, kai kace sun shekara da yunwa, kafin ya gama mamaki yaran sun cinye abincin tass.
"Ruwa ALHAJI." ƙaramar yarinyar ta faɗa, miƙa mata yayi yana jinjina ƙoƙarin cin da tayi ba tare da ta nemi ruwan ba."Salamatu! Kandala! Abu! " sunayen matansa kenan da yake ƙwala musu kira.
Cikin sauri suka fito suna zama, dan basu taɓa jin sautin Alhaji irin haka ba.
"Lafiya malam da ƙwala kira haka?" Kandala ta faɗa tana dai-daita tsayuwarta.Harara ya wurga mata yana maida kallonsa ga yaran, ya nuna mata su "Kina ina kika bar min yara da yunwa a duka yinin yau? Kuma a haka kina a matsayin uwa a garesu."
YOU ARE READING
JINI YA TSAGA
ActionBa son ko wano uba bane samun balagurbi acikin ahalinsa, sai dai sau da dama ALLAH kan jarrabi bayinsa ta hanyoyi da dama. Duk da kasancewarsa babban Malami agarin hakan bai hana ya samu ta waya wajan gaza daqusar da mutum ɗaya tilo acikin ahalin sa...