BIYU

1K 90 0
                                    

JINI YA TSAGA....! 👭

®NWA

©by 😘Um_Nass🏇

SADAUKARWA GA *_RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)_*

PAGE 2

Da kallo kowa dake wajen ya bishi, zuciyar su ta riga data gama tsinkewa da tausayin sa.
Wasu da yawa kuma suna jinjina butulci da rashin kirki irin na Hafsa, duk ɗiyar da zata yima mahaifinta haka to babu wanda ba zata yima fiye da haka ba.

Kallonta Ado yayi ya share hawayen dake Zuba akan fuskar sa, wanda babu makawa na tausayin Mahaifin nasu ne "Kiga yanda Alhajin mu yake kuka saboda ke Hafsa! Kiga hawayen takaicinki na sauƙa akan fuskar mahafinki daya zama tsani na kowani farin ciki arayuwar ki! Kinji haushin kanki Hafsa. Kin gayyaci sheɗan zama aboki na kusa agareki, kin kuma ruƙo hannun ruɗun duniya dan suyi ƙawance dake acikin tafiyar ki. Ki shirya tarban munanan ranakun da zasu riskeki, ki kuma tanadi makeken abin goge hawaye atare da ke, ki kuma shirya fuskantar nadamarar da ke ɗago miki hannu alokacin da bata da amfani."
Kallon sa tayi ta yatsina fuska, duk da kalaman da Alhajinsu ya faɗa agareta sun sauƙar da mummunan rauni da tsoro agare ta. Amma ko kaɗan ba zata bari suga karayar ta ba, ba zata nuna raunin ta akan gaskiyar da take cikin abin da take shirin aikatawa ba, mutanen da suke kewaye da su sun isa bata cikakkiyar gaskiya da jajircewar ta amatsayinta na mace guda ɗaya tilo da zata iya fito-na-fito da ko wani Namiji.

"Uhmm yaya Ado kenan! Ko yaushe maganar maza akan abu ɗaya ne, basa fahimtar ƙunci da raunin dake zuciyar mace. Amma na tabbata wata rana zaku fahimci abin da nake son ganar da ku. Shi kansa Alhajinmu zai san soyayyar da nake masa ta gaskiya ce, zai fahimci kunyar dake cikin duniya aikin banza ce. Nagode Allah da Umman mu bata gidan nan da labarin zai fi haka muni a idonun duniya da ku kanku." tana gama faɗar haka ta raɓa ta kusa da shi ta shige gidan.

"Ya Allah Allah!" ya faɗa yana runtse ido hawaye na zuba akan idon sa. 'Lallai duk wanda yayi nisa baya jin kira, idan kuma Allah bai shiryar da kai ba to babu mai iya shiryar da kai' maganar da yaƙe aƙasan zuciyarsa kenan.

Daga nan sauran mutanen da suka taru awajan kowa ya fashe ya kama gaban sa.

Shiga gidan yaya Ado yayi dan riskar Mahaifinsu ya ƙara tausarsa da bashi baki akan abin da Hafsa ta aikata agareshi.

Dai-dai lokacin da Hafsa ta ɗauko jakar kayanta tana riƙe da hannun Ummi ɗiyarta mai shekara bakwai aduniya, bayanta kuma da goyon Bunayya.
Leƙa kanta tayi falon Alh. Kamaludden tana murmushi "Alhajinmu ni na tafi, Allah ya baka ikon adalci akan matayenka, ya rabaka da tashi da shanyayyan jiki aranar lahira."

Idonsa ya buɗe ya kalleta sai ya rufe yana girgiza kai ba tare da ya ƙara ce mata komi ba.
Baki buɗe Ado ya tashi yana ƙoƙarin dukan ta "A'a fa Ado! Nace ka ƙyaleta ko?"

Ganin fusatar da Ado yayi yasa ta ja hannun Ummi suka bar gidan ba tare data ƙara bi ta kan sauran mutanen gidan ba, ko sallamar kirki batayi da su ba. Agare su kam murna suke suna kiran asauƙa lafiya, zama da Hafsa yafi zama da Annobar bala'i. Su atakure yaransu atakure.

Harara Ado ya aika mata da rakiyar ta, kana yasa hannu abakin sa yana cizawa na takaicin halayyar ƴar uwar sa da hanashi kilarta da Alhajin yayi "Wallahi Abba da badan agida Umman mu ta haifi Hafsa ba da sai nace musauya mana ita akayi. Da kuma babu kamar da ke gudana tsakanin ta da mu da kai to wallahi da nace haure tayi ta cikin rufa-rufa ta zama ƙarƙashin ahalin ka."

Ido Alh. Kamaludden ya wara yana kallon Ado, kafin yayi murmushi wanda da ganinsa na ciwo ne da takaicin Hafsa "Ko kaɗan kada ka ƙara wanan tunanin Ado. Acikin ko wani gida akan iya samun mai kyau da kuma gurɓataccan cikin sa. Allah ya sani ban ragi Hafsa da wani abu na jin daɗi kama daga ilimi zuwa tarbiyya ba wanda har ta iya aikata min rashin kirkin ta. Nasan bata da kirki bata da haƙuri amma ban san abin nata ya girmi sani na ba, ban kuma san halin ta ya wuce tunani na ba. Amma babu komi ga duniya nan zata koya mata darrusan rayuwa, taje ko ina take son zuwa amma banda gida na."

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now