October 19, 2020
JINI YA TSAGA......👭
®NWA
Haƙƙin Mallakata
(OUM-NASS)PAGE 12
Har ya je sallah ya dawo yana tunanin maganar da suka yi da Hafsa, yana hango ta janye da jaka a matsayin wadda zata bar gidansa.
Kwana ɗaya tal da yin aure ace amaryarsa ta shiga duniya? Wannan magana ce da zata karaɗe duniya ba ma iya garinsu ba.A haka ya bama ɗalibansa haƙuri da suke jiran ya basu karatu, duk da dama tun farko sun ɗauke masa nauyin karatun nasu har zuwa mako biyu, amma shi ya ce zai iya musu karatu, a cewarsa aure ba zai hana ya musu karatu ba.
Sai gashi Hafsa ta watsa masa ƙasa a ido, wannan abun kunya har ina, kasa jurewa ya yi, sai da ya biya ma manya a cikinsu karatu, sannan yace su ɗaurama wanda suke ƙasa da su.
Ƙirjinsa kuwa na ta luguden bugawa dan bai san me zai je ya tarar a gidan ba. Tun daga ƙofar gida ya fara jiyo sautin kiɗa na tashi a cikin gidan, abun sai ya zame masa wani banbarakwai, da sauri ya ƙarasa cikin gidan tsayawa ya yi cak kamar magijin da baya aiki, domin ganin abun da idanuwansa suke.
Hafsa ya gani cikin ƙananun kaya riga da wando wanda suka ɗameta, tana faman tiƙar rawa da juyawa, gefe guda kuma wasu yara ne maza da mata wanda za su kai su shida suma sai tsalle suke da alama suna ƙoƙarin koyan rawar ne."Hasbunallahu wa ni imal wakil!" Ya faɗa yana dafe kansa 'Kiɗa yau a gidana?' Ya faɗa a zuciyarsa da neman inda sautin ya ke futa. Ya yi sa'a ya hango wata Sifika da sautin ke tashi a cikinta, ƙarasawa ya yi ya ɗauke ta, bai tsaya duba ta ba ya bugata da ƙasa, nan take ta yi filla-filla da ita sautin kiɗan ya ɗauke.
Tuni yaran suka fara rige-rigen fucewa dan ba su taɓa ganin ɓacin ransa irin na yau ba."Taɓɗijam! Mp ɗin nawa ka fasa min? Wallahi sai ka biya ni a bata!" Ta yi maganar da ƙarfi jikinta har rawa yake saboda tsananin futunar da ke cinta.
"Ki yi duk abin da kike son yi Hafsa a gidan nan, zan baki ko wata dama a matsayinki na matar aure da take da cikekken 'yanci, amma ba zan yarda ki mai da min gida ya koma na 'yan gala ba. Wannan shine kuskure mafi girma da za ki aikata min."
Ya ƙarasa maganar da buɗaɗɗiyar muryarsa, idanuwansa duk sun sauya kala zuwa ja, alamun dai ransa ya kai maƙura wajen ɓaci.
"Hehehe! Abun dariya Malam! Wato nishaɗi a gidanka ya zama kuskure, amma kai baka taɓa tunanin aurena da kayi shine mafi girman kuskuren da ka tafka a rayuwarka ba? Bayan rashin cika alƙawalin da ka yi na cewar zaka dawo ka mana abinci, shine ka datse min abin da ya ke ɗebe min kewa ta? Nikam wani laifi na aikata a rayuwata da ƙaddara ta haɗa ni zaman aure da kai?" Ta ƙarasa maganar tana dafe kanta da zama akan kujera.Jikinsa ne ya yi sanyi ganin hawaye na sauƙa akan kyakkyawan fuskarta, hakan ya sa ya risina a kusa da ita.
"Babu wani abun Nishaɗi a wannan rayuwar Hafsat, face shagala da kuma sawa mu manta abin da ya kawo mu. Duk abun da zaki kira da nishaɗi mutuƙar ba ambaton Allah ba ne a cikinsa to shagala ce da kuma naƙasu a gare mu.
Kina da sani sosai, kin kuma san illar abin da kika aikata, babu buƙatar da zai sa ki zauna da girmanki da iliminki kina ta tiƙar rawa a gaban yara kamar wata 'yar bori.
Ki kama kanki kafin ki samu a girmamaki."
Harararsa ta yi daga inda ta ke, tana ji kamar ta kwaɗa masa mari.
"Wato rawar da nake ce ta yi kama da ta 'yan bori? Indai zan yi rawar 'yan bori na tabbata kai kanka sai na shigo da kai dandalin rawar."Murmushi ya yi sannan ya fara share mata hawayensa "Ni a tunanin duk wanda yake kaɗa jiki da tsalle da sunan rawa yake to inaga rawar bori yake ƙoƙarin kwaikwaya."
Bige masa hannunsa ta yi daga kan fuskarsa, sannan ta haɗe hannayenta biyu wajen yin tagumi.
"Ina ƙoƙarin korar yunwar da ke tare da ni ne! Ina ƙoƙarin samarwa kaina abin da zai sa na manta da wa nake tare da shi ne! Har yanzu da kake zaune a gabana ban ga alamun zaka bani abincin da zai mantar da hautsinewar da cikina ya ke ba."
Dafe kansa ya yi sannan ya ruƙo hannunta "Zo mu je a gabanki zan yi girkin ma yau."Tirjewa ta yi sannan ta kalli Mp ɗinta shima ya mayar da kallonsa kanta "Nifa na yi rantsuwa akan sai ka biyani." Ta yi maganar tana ƙara haɗe fuskarta.
Hannunsa ya zura a aljihunsa ya ɗebo kuɗin da bai san nawa ba ne ya bata "Gashi amma bana buƙatar wata irinta."
Kuɗin ta amsa "Da dama dai! Inaga ka yi girkin ba sai ina gani ba, hakan zai fi birge ni akan ace a gabana ka yi."
Kai ya gyaɗa mata yana murmushi sannan ya shiga kitchen ɗin, ta bishi da rakiyar harara, tana kwanciya akan doguwar kujerar da ke palon.
Daga kwancen da take ta fara jiyo ƙamshin girkin nasa, ido ta lumshe sannan ta fara haɗiyar yawu.
"Allah dai yasa girkin nan ya yi daɗi kamar yanda yake tashin ƙamshi."Tana kwance ta hango shi yana jera kayan abincin a daining sannan ya koma kitchen ɗin, bata san me ya yi ba, sai gani ta yi ya sake futowa ya shige ɗakinsa.
Mintuna goma ta gaji da jiran ya zo ya ce ta taso an gama ta miƙe a lokacin ta ga ya futo sanye da jallabiya a jikinsa, hakan ya ankarar da ita wanka ya yi."Masha Allah! Kin tashi ashe? Ina niyar na zo na tada ki."
"Yunwa dai ta tayar da ni, ace mutum tun abincin safe bai ci komi ba har yanzu wajen ƙarfe uku. Gaskiya ba abu mai wahala da kasada a rayuwa kamar auren riƙeƙƙen ustazu."
Ta ƙarasa maganar tana ɗingisa ƙafarta "Daɗinta ma dai daga hannun aka futo."
"Amma kuwa ba irin naka ba Abdu. Domin mu ba'a mana iyaka da abin da za mu ci ko sha."
Kujera ya ja mata ta zauna sannan ya ɗauko filet ya ajiye a gabanta "Anan ɗinma ba'a miki iyaka da komi ba, kawai lalacinki ne ya sa kika tsaya a sarrafa a baki.""Bayan ka farkani kake kirana da malalaciya Abdul? Da tunaninka bayan ɗaukarka da nayi zan amfana wajen cika maka tumbinka na baka damar sake mai-maita mun abin da ka yi? Ashe ma kanwa na kawo garin."
Dariya ce ta suɓuce masa sai dai bai bari yayi mai yawa ba yayi murmushi ya fara zuba mata farar shinkafa.
Sannan ya ɗauko miyar jajjage da naman kaza ya zuba mata.
"Gaskiya kam, bai ci ace duk wannan abun da ya faru a same ki a gaban tukunya ba. Zai fi dacewa dai ki kasance riƙe da cokali a hannunki." Ya tura mata abincin gabanta."A ido dai ya yi kyau. Farar shinkafa da miyar kaji, Allah yasa babu ƙarninsu." Ta faɗa tana kaiwa bakinta.
Ido ta lumshe saboda abincin ya mata daɗi sosai, ta tabbata ko ita bata isa ta yi irin miyar ba, amma saboda rigima ta yamutsa fuska."Shinkafar ta yi tauri da yawa, kamar tafasa ɗaya aka mata aka tsame, miyar kuma dai babu ɗanɗano mai tashi." Ta yi maganar har a lokacin tana yamutsa fuska.
Zuba nasa ya yi shima ya zauna yana ci, dan yasan neman magana ne kawai irin na ta.
YOU ARE READING
JINI YA TSAGA
ActionBa son ko wano uba bane samun balagurbi acikin ahalinsa, sai dai sau da dama ALLAH kan jarrabi bayinsa ta hanyoyi da dama. Duk da kasancewarsa babban Malami agarin hakan bai hana ya samu ta waya wajan gaza daqusar da mutum ɗaya tilo acikin ahalin sa...