Bakwai

439 54 8
                                    

HAƘƘIN MALLAKATA
 
  August 8, 2020

JINI YA TSAGA....! 👭

Oum-Nass

page 7

Numfashi Ummah ta ja tana share hawayen da ya gangaro akan fuskarta "Ya Allah ka tausasa zuciyar Hafsa ta koma mai sanyi a gidan mijinta. Ka rabata da wanan mummunan ɗabi'ar da take ƙoƙarin ɗaukanta." Ta faɗa tana ɗaga hannayenta sama.

Sanan ta tashi ta futo tsakar gidan, a haka aka ci gaba da gudanar da shagalin biki, kowa na musu murna da barka da arziqi akan mijin da Hafsa ɗin ta samu, wanda da yawa 'yan mata ke burin ace su ne suka same shi a matsayin mijinsu.

Ka sancewar Alhaji Malam baya son wada bidi'a tun a daren ya kira Hafsa ya mata nasiha mai ratsa jiki sai dai yanda nasihar take shiga haka take fita kamar kaɗawar iska a kunnuwanta.
Har ya gama surutunsa da take ganin kamar surkulle ya ke mata ta kaɗai jikinta ta tashi "Nagode Alhaji da zaɓa min miji na gari da kowa ke faɗa. Amma ina fatan ka faɗa masa labarin ko wa ka aura masa, dan ni ban yarda da kalmar nan ta mace tayi haƙuri namiji ya cuceta ba." Tana gama faɗar haka ta share hawayen fuskarta ta fuce tabar ɗakin.

Baki buɗe Alhaji Malam ya ke kallonta har ta ɓacema idonuwansa, ya kasa tunanin matsaya guda ɗaya, kamar yanda fargaba da tsoro ya cika zuciyarsa. "Ya Allah kada ka jarrabe ni da abun da yafi ƙarfina." Ya faɗa cikin rawar muryarsa.

Acan kuwa Hafsa tana futa ta shige motar ɗaukan amarya, idanuwanta fes babu alamun hawaye a cikinsa, sai dai wani ƙunci da ke ziyartar zuciyarta.
Tasha ji ana cewa mace gajeriyar rayuwa ke da ita, ba zata sake ta wala yanda take so ba, sai a ƙarƙashin kulawar namiji. Sai dai a gareta ta musanta hakan, ita zata sabunta wanan labarin, domin ba kamar sauran mata ba ce ita, asalima tana da dogon buri. Burin yin rayuwa mai cike da armashi, ba wai ta ƙare rayuwarta a ƙarƙashin namiji ba. Tana da sabon karatun da zata koyar da maza su fahimci ko wacece mace.

Har aka kawota gidan tana saƙa da warwara, sai da gwaggonta ta buɗe mata ƙofa ta ruƙo hannunta sanan ta fahimci sun zo gidan, ba laifi tun a ƙofar gidan zaka fahimci gidan na zamani ne, domin yasha fantin da kalar milk da cofee a ƙofar gidan.
"Ki shiga da bismillah sanan kiyi addu'ar kauda sharri a cikin gidan kamar yanda musulunci ya koyar da mu." Gwaggonta ta faɗa mata tana riƙe da hannayenta da kuma tsayawa a ƙofar gidan alamun jira ta ke ta yi addu'ar kafin ta shigar da ita gidan.

Murmushi tayi tana kallon ƙofar gidan "Gwaggo ai nice sharrin, me zai sa na kori kaina bayan na bayyana?" Ta faɗa tana kallon Gwaggon da itama take kallonta baki a buɗe.
"Ke ban son shashanci, ki yi addu'a mu shiga gida."
Kawar da kanta tayi daga kallon Gwaggon nata, a hankali ta buɗe bakinta ta fara yin addu'ar.
Hafsa tana da ilimi sosai, duk a gidan Alhaji Malam itace macen da ta amsa sunanta, ko malam da kansa zai bugi ƙirji akan Hafsa zakaran gwajin dafi ce a fannin karatu.

Bayan ta gama addu'ar ta zura ƙafarta ta dama ta shige gidan, hakan yasa sauran masu take mata baya suka bita.
Har gaban gadonta Gwaggo ta kaita "Ki zauna da amincin Allah. Allah ya albarkaci rayuwar aurenki, ya kaɗai fitina a cikinsa.
Dan Allah ki zama mai haƙuri da ladabi da biyayya a gidan aurenki Hafsa, nasan kina da ilimin addini, shi kaɗai ya isheki ki samu nutsuwa a cikin rayuwar aurenki.
Mijinki masani ne kamar mahaifinki, Allah ya zaɓeki ya fidda ke daga hannu mai kyau, ya mayar da ke cikin mafi kyau. Ki cika gidanki da ƙamshin aminci, ki kunna futular hasken da zata haska zuciyar mijinki."
Kai ta gyaɗa murmushi na sauƙa akan fuskarta "Nagode Gwaggo." Ta faɗa cikin sunkuyar da kanta a ƙasa.
Daga haka Gwaggo ta tattara 'yan rakiyar amarya suka fara tafiya da shiga motar ɗakin amarya.
Ruƙe hannun Gwaggon tayi wani munafukin hawaye ya gangaro akan idanuwan Hafsat "Gwaggo dan Allah kada ku tafi ku barni ni kaɗai anan."
"Ki yi haƙuri Hafsatu kowa da haka ya girma, ina amfanin mu zauna goɗai-goɗai a gidan surikinmu? Wanan shine girman ai Hafsatu."

"Ni bana son wanan girman Gwaggo, dan Allah ku maida ni gida."
"Ba kya so gobe mu dawo mu ganki kenan?"
"Ina so Gwaggo."
"To ki barmu mu tafi, na miki alƙawarin gobe zaki ganmu harda wasu ma da baki zaci zuwansu ba."
Sakin hannun gwaggon tayi ba tare da ta mata magana ba, ganin hakan yasa Gwaggon ta juya da sauri ta fice a ɗakin nata.

Murmushi Hafsa ta yi tana share hawayen kan fuskar ta "Haba yaushe zan ɓata hawayen kan fuskata akan wani aure. Dama lamfo nayi kada akai ni gaba ace banyi kuka ba da aka kawo ni gida."
Ta ƙarasa maganar tana sakin wata dariya mai sauti.

Ta ɗauki tsawon lokaci a haka kafin ta miƙe ta fara zagaye ɗakin, wani zafi da ƙunci take ji yana sauƙa a zuciyarta.
Dai-dai lokacin kuma ta fara jiyo sautin maganar maza, hakanne yasa ta yi sauri ta zauna a tsakiyar gado ta lulluɓai kanta da mayafi.
Can bayan wani lokacin kuma taji an murɗa ƙofar ɗakin nata, a hankali take jin takun takalminsa da kuma ƙamshin turarensa na cika mata hancinta.
"Amaryata bakya laifi." Ya faɗa cikin tattausar muryarsa.

Zama yayi a kusa da ita, yana ƙoƙarin ɗage mayafin da ke kan fuskarta, saurin riƙe hannunsa ta yi ba tare da ta ɗago ba "Kafin ka samu ganin wanan fuskar akwai buƙatar ka biya kuɗin ganinta."
Murmushi Abdul-mannan yayi "Duk sadakin da na biya har sai na sake biyan wani Kuɗin na ganin Fuska Hafsat? Ai komi da ke gareki ya halatta a gareni tun lokacin da na biya sadakinki shedu kuma suka sheda da hakan."
"Sadakin da ka biya na ƙulla alaƙa tsakanina da kai ne, amma ba na kallon fuskata kullum ba."
Murmushi yayi yana tashi akan ƙafafuwansa da tuƙo hannayenta "Ki zo muje falo ga su Yasir na jiranmu dan mana nasiha."
Sauƙowa tayi daga kan gadon "Matsalata da auren malami kullum cikin nasiha. Duk kalar wa'azin da aka sauƙe min a wanan auren bai wadace ku ba har sai kun sake min wani."

Juyowa yayi yana kallon Hafsan maganar da zai yi ma ya kasa, kasancewarsa mutum mai shuru-shuru da haƙuri.
"Kema ina da labarin malamarce ai, kinga kenan zamu yi haɗaka wajen yin abu ɗaya."
A haka suka futo falon. Yasir ya fara magana "Kai kuma daga kiran amarya sai ka shanya mu? Gashi har kun cinye mana lokacin namu."

"Ayi haƙuri, kunsan aamarya akwai sarauta." Abdul-mannan ya faɗa yana haɗe hannayensa waje ɗaya.
"To ya zamu yi ai dole mu yi haƙuri. To a gurguje dai nasihar da zamu muku kun riga da kun santa, amma duk da haka zamu ƙara muku da nasiha akan kuyi haƙuri da juna. Haka kuma ku kare sirrin junanku, dan a yanzu babu wani wanda ya kaiku kusanci da junanku.
Lallai duk abu mai kyau yana farawa ne daga tushensa na asali, kenan zaku gina rayuwar aurenku da nagarta da kuma yakanah a cikinta.
A ƙarshe muna ƙara muku nasiha da kuji tsoron Allah a zaman takewar aurenku, Allah ya amintar da ku da samun kyakkyawar rayuwa, da kuma albarkar aure."
"Ameen ya rabb." Sauran abokanan nasu suka faɗa, daga nan Yasir ya rufe musu da addu'a bayan ya tambaye su ba mai magana suka amsa masa da babu.

Daga haka suka fice suna tsokanarsa bayan ya musu rakiya zuwa ƙofar gida,daga bisani kuma ya rufe ƙofar ya dawo gida fuskarsa ɗauke da fara'a.
Sai dai abun da ya bashi mamaki ganin Hafsat zaune ta cire mayafin da ke kanta, ta janyo ledar kaxar da ke gabanta ta fara ci "Me yasa baka zaɓo min kazar da ta fi wanan girma ba? Tun yanzu ka fara nuna min tsumulmular da zaka fara min a gidanka."

Tsayawa yayi cak ba tare da yayi magana ba yana kallonta.....

🌷🌷🌷🌷
#JiniYaTsaga
#NWA
#Cmnts,Vote, share.
#Girmamawa.

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now