Ɗaya

1.3K 118 3
                                    

JINI YA TSAGA.....! 👭

©Um_Nass 🏇

بسم الله الرحمن الرحيم.

Alhamdulillah dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah s.w.a wanda ya bani ikon fara rubuta wanan labarin, ina kuma roƙon Allah yasa duk abin da zan rubuta ya zama alkhairi ne agaremu baki ɗaya.

*_Sai dai fa labarin awanan karon yasha ban-ban da sauran labarin dana saba kawo muku, wanan tafe yake da ababan ban haushi da ban tausayi. Kalma ɗaya tak ke tafiya acikin labarin, wanda take daƙusar da ko wani karsashi da ƙumajin daƙusar da jarumar labarin, JINI YA TSAGA... ! Haka kowa ke faɗa mata, haka kowa ke dannarta acikin tafiyar._*

    SADAUKARWA GA *_RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)_*

Page 1

BIRNIN KEBBI
JEGA L.G

Gidan Alh. Kamaludden.

Gida ne babba wanda yake ɗauke da matan aure guda uku, biyu daga cikin su suna da yara aƙallah zasu kai tara, sai ɗayar da take sabuwar amarya atsakanin su, dan aƙalla aurenta da mai gidan bazai haura wata biyu ba.

Durƙushe take agaban murhu tana faman soya kaji, sauran yaran gidan sai kai-kawo suke awajan ta.

Gefe kuma sauran matan gidan su biyu ne suke hira atsakanin su, wanda bata wuce ta abin daya shafi rayuwar yau da kullum.
Akwai zaman lafiya sosai ashimfiɗe agidan, kasancewar maigidan ya tsaya tsayin daka amatsayin sa na namijin duniya, wanda bai ragesu da komi ba na rayuwa.

Fitowa tayi daga ɗakin da yake mallakin ta, tun bayan mutuwar auren ta data dawo, aka bata shi amatsayin ɗakinta da zatayi zawarci. Kyakkyawar mace mai ɗauke da farar fata, da faffaɗar fuska, wadda ko yaushe take sake da fara'a, hancin ta amiƙe yake ziyat har yana ranƙwafawa, sai bakinta ɗan ƙarami mai ɗauke da jerararrun haƙora farare, idanuwanta basu da girma sosai, asalima ko yaushe suna maƙale alungu, idan baka sani ba sai ka ɗauka harara take aika maka da shi, wanda hakan ɗabi'a ce agareta. Shekarunta bazasu haura 30 ba aduniya.

Ƙarasawa tayi kusa da mata biyun da suke zaune, wanda tana zama tajiyo sautin kukan ɗiyarta itama ta tashi "Abdul maza ɗauko min Bunayya ta tashi abarci." ta faɗama wani yaro da yake ta faman izawa Amaryar wuta ita kuma tana tsame kajin da suka soyu daga cikin kasko.
Tashi yayi da sauri sanin halin Anty Hafsa da yayi, yanzu tana iya kai masa duka ko bugu idan baiyi hanzari ba.

Juyawa tayi ta kalli matan, ta kwaɓe fuska "Wallahi ku kam kun rako mata duniya, duk da kasancewarku matan mahaifina amma hakan bazai hanani faɗa muku gaskiya ba. Tun da nazo gidan nan ranar girkin Asma'u amarya kaɗai ake cin cima mai daɗi agidan nan. Haka kuma ranar da take girki ne kawai ake samun damar yin dumu-dumu da kaji ayi wadaƙa da su kamar ba da kuɗi ake siyan su ba, amma ku kun miƙe ƙafa cikin mutuwar zuciya da karaya kuna jira agama asan muku."

Kallonta sukayi cikin mamaki da alhinin maganar ta "Mi kike son faɗa mana Hafsa? Ina duk ɗaya ne ko muyi ko ita tayi, kason data samu shi zamu samu muma. Asalima mu muna finta da kaso mai yawa kasancewar muke da yara agidan nan." Wadda take amatsayin uwargida ta faɗa tana kai kallonta ga ta kusa da ita.

"Ƙwarai kuwa Yaya Abu ni banga abin nuna jin haushi ko kuma takaici acikin wanan ba, abin wahala da sa aiki." Rabi'atu ta faɗa tana ƙarasa maganar da murmushi.

Harara ta aika musu da ita, kafin tayi magana Abdul ya miƙo mata da Bunayya ya koma wajan Asma'u yana fifita mata wuta.

"Mtsss! Ya tabbata kun rako mata duniya wallahi, to ko kunyi haƙuri saboda zuciyarku ta gama mutuwa da yadda akan ɗa namiji ni bazanyi shuru na zura ido ina ganin Mahaifina na aikata haramun ba, bazan bari gefen mahaifina ɗaya ya rinjayi ɗaya ba, idan har babu wanda zai bashi shawara yaji ya gyara, ai akwai Hukuma ita kuma doka bata kowa bace bata kuma ƙyale kowa ba, ni nan zan bada sheda na kuma tsaya muku akan rashin adalcin da Mahaifina yakeyi muku."

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now