March 21, 2020
JINI YA TSAGA......👭
®NWA
Haƙƙin mallakata
(OUM-NASS)Free book 💃
PAGE 14
Ya daɗe zaune a wajen yana jin bugun zuciyarsa har a lokacin na tsananta. Bai taɓa tsammanin zata iya fassara kalamansa irin haka ba, duk da ya san wace Hafsat da kuma gidan da ya aurota.
Kamar yanda ta zama zaƙwaƙwari ta farko wajen ilimi haka ta zama zakka ga rashin jinta.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil!" Ya shiga mai-maitawa a ƙasan laɓɓansa, kafin ya ji bugun zuciyarsa ya dai-daita.
Hakan ya sa ya janyo litattafan da ya fara dubawa yana nazartar su. Sai dai rabin hankalinsa na kan Hafsat, bai sake jin motsinta ba.
Ganin baya fahimtar komi ya sa ya rufe littafin ya fice a ɗakin ya nufi ɗakin Hafsat.
Bai ji motsinta ba hakan ya sa ya murɗa ƙofar ɗakin ya yi sa'a ƙofar a buɗe ta ke.
Ajiyar zuciya ya sauƙe ganinta zaune akan abin sallah da littafin hisnul muslim a hannunta.
A hankali ya fara ta ko ƙafafuwansa har zuwa kusa da ita, ya zauna a gabanta kana ta tanƙwara ƙafafuwansa kamar mai shirin cin abinci.
Juyo da kanta ta yi ta kalle shi, sai ta yi murmushi sannan ta mayar da kallonta ga littafin.
A hankali ya sauƙe sassanyar ajiyar zuciya sannan ya buɗe bakinsa ya fara magana cikin sanyin muryarsa.
"Na gode Allah da na same ki a haka. Na kuma ji daɗi ƙwarai da naga fuskarki ɗauke da murmushi.
Nagartarki ta futo a cikin shigar kamalarki, hasken fatarki ya haskaka kamar yanda idanuwanki suka rabauta da samun kyakkyawan gani.
Zan so na ci gaba da ganinki a haka, zan so sautin muryarki ya ci gaba da fita da neman kusanci ga ambaton Allah (S.W.A)."Rufe littafin ta yi tana shafa addu'o'in ba tare da ta yi magana ba ta tashi tana naɗe abin sallar ta ajiye shi a ma'ajiyarsa sannan ta mayar da kallonta ga Abdul-Mannan da har a lokacin idanuwansa na kanta.
"Ka ce wani abu ne Abdul?"
Tashi yayi tsayen shima ya matso kusa da ita har suna jin hucin numfashin juna. Idanuwansa fes a kanta kamar yanda itama take kallonsa babu ƙiftawa.
Kawar da idonsa yayi yana murmushi da kallon hijabin da ke sanye a jikinta.
"Abubuwa da yawa na ce Malama Hafsat! Da wanne kike so na fara mai-maita miki dan naji hakan ya miki daɗi sosai?"
Ɗora hannunta ta yi akan kafaɗarsa, tana yalwata murmushi akan fuskarta, sannan ta sa ɗaya hannun nata tana zagaye sajen da ke kwance akan luf a kan fuskarsa.Idanuwansa ya lumshe jin wani abu na yawo a jikinsa, yana jin tsikar jikinsa na zubawa. Yayin da bugun zuciyarsa ke ƙaruwa kamar zata fito daga maɗaukarta.
Jin hucin numfashinta a kusa da kunnensa ya sa shi saurin waro idanuwansa wa je.
"Maganarka mai kyau ce da son a jita, kamar dai yanda ka kasance mai kyau Abdul. Sai dai ni a ko mi na rayuwata ina adawa da abu mai kyan da ya zarta ni. Kamar yanda na tsani shisshigi da tankawa ga duk abin da aka ga a tare da ni." Ta ƙarasa maganar tana hura masa iskar bakinta a kunnensa.
Hakan ya sa ya sake wara idonsa. Yana jin jikinsa na rawa kamar mazari.Janye jikinta ta yi daga nasa tana murmushin ganin halin da ya shiga, ta ruƙo hannunsa kamar raƙumi da akala haka ya shiga binta har suka fito falon, ta saki hannunsa.
"Ka tsaya a iya matsayinka na mijina. Ka daina saurin aika yabo a gare ni, domin kada wata rana ka gaza yafewa zuciyarka." Tana gama faɗa ta koma ɗakinta da rufo masa ƙofa da ƙarfi.
Wanda hakan ya sa shi rufe idonsa.
Zama yayi shirum a kan kujera yana maida numfashi da kallon yanda jikinsa ya jiƙe da gumi.🌷🌷🌷
Hhhh da babu gara ba daɗi dai ko, ku rage Zango.
Ga masu Buƙatar wannan labarin za su iya shiga wannan grp ɗin, amma idan har kin san ba za ki yi cmnts ba to please ki xauna a inda kike dan Allah.
https://chat.whatsapp.com/IqPTmfV5sPQ3OsQtvitSEm
Girmamawa.
YOU ARE READING
JINI YA TSAGA
ActionBa son ko wano uba bane samun balagurbi acikin ahalinsa, sai dai sau da dama ALLAH kan jarrabi bayinsa ta hanyoyi da dama. Duk da kasancewarsa babban Malami agarin hakan bai hana ya samu ta waya wajan gaza daqusar da mutum ɗaya tilo acikin ahalin sa...