PART 1

121 3 0
                                    

            *_HAƘURI BA YA ƁACI_*

                 *LITTAFIN*
    *NAFISAT ALIYU FUNTUA*
          *(UMMUHFA'DIMA)*     

*_Labari me bantau sayi da Al'ajabi Me cike da sadaukarwa_*

       
Bismillahir Rahamanir Raheem!

       _Masoyana ina mebaku Hak'uri akan rashin jin Cigaban *INDO AISHA* Hakan yafarune, Asanadin rasa wayata danayi, amma insha Allahu da zaran nasamu last, Pege d'in danayi zakujini da k'arashen shi, Insha Allahu dafatan zaku tayani nema. Nagode UMMUHFA'DIMAR kuce✋_

             *_Sadaukarwa ga dikkanku masoyana ngd da addu'o'inku agareni_*


BABI NA 1️⃣➖2️⃣

Falmata! Falmata! Falmata! Wata kakkaurar matace tsaye, ak'ofar wani d'an k'aramin d'aki Sai faman cika takeyi tana batsewa, Babu alamar rahama atare da ita. Wani yarone yafito daga cikin d'akin d'an kimanin Shekara biyu da rabi, yana kuka.
       Kai dan iska ina uwarka take? kota tafi yawon gantalin data saba zuwane, a'a tana kwance batada lafiya! Kambala'i yauga tsinanniyar mace yaukuma da wannan makircin kika tashi to wallahi saikim fito kinyimin aikin gida, Daga taimako asheni bansani ba bala'i na d'aukarwa kaina ba, ta idasa maganar tana bankad'a d'akin ta Shiga, kina ina fito.

       Wadda aka kira da Falmata tana duk'ushe, Ak'asa tanata faman juye-juye, Hhhhhhhhhhh yau garibar gantali tazo shegiya wallahi nibaruwana da wata nak'udarki dole kije ki had'amin wuta kisharemin gidana sannan kiwankemin kwanoni na kafin mutane sufara taruwa inrasa kwano
da zan zuba, Musu abinci.
       Wayyoh! Hajiya dan girman Allah kiyi Hak'uri wallahi bayana yarik'e ki taimaka min zammutuuuuuh!
      Ta idasa maganar da kyar alamar tanajin ciwo ajikinta, mitssssss nifa ba tausayinki nakejiba kinganni nan tunda harmugun halinki yasa Mijinki ma yagudu yabarki, wani irin zazzafan hawayene! Yazubawa Falmata saboda tsananin zafin da maganar tayi mata arai duk da ba yau tafara jin wannan, kalmar ba daga bakunan mutane.

       Yunk'urawa tayi da kyar ta mik'e tana takawa, Da kyar.
    Abun gwanin ban tausayi, tsohon cikine ajikinta wanda gaba d'aya yayi k'asa alamar yana gab da fitowa duniya, bako alamar tausayi afuskar wannan mata haka ta tasota waje.
       Kitchen d'in gidan ta nufa  wanda aka zagayeshi da langa-langa, tana dafe da cikin jikinta ta hau jera itatuwa awuta da kyar wutan yakama, tajawo babbar tukunya Number talatin ta d'ora akan wutar.
       Rijiya ta nufa taringa jawo ruwa tana zubawa atukunyar, da kyar! Kwanonin wanke-wanken tafara had'awa yaron ta Kamal yana taimaka mata k'arfin hali kawai takeyi, sannu-sannu hartasamu tagama uban wanke-wankennan, dama tanayi tana duba wutar, Bayan tagama kitchen d'inta koma tagan shinkafar da tazuba har yatsane tsab.

       Fitowa tayi ta duk'a da nufin ta dauki babbar kular da zata kwashe shinkafar aciki, wani murd'awa da cikinta yayi bayanta yarik'e, wash! Allahna bayana, ta idasa kai k'asa da kyar tanakiran sunan Allah wani ruwa nabin k'afafunta.

         Kai-kai meye haka shegiya me mugun hali sokikeyi kikashemin kasuwa kamar yadda mugun halinki yasa mijinki ya gudu yabarki, kainide nashiga ukuna wallahi nide Sale yabarmin masifa agida" zakibarnan ko saina hankad'aki k'azamar banza da wofi.

      Ta idasa maganar tana fisge kularta ahannun Falmatar, wanda yasa har saida ta bugu da k'arfen barandar kitchen d'in, Kamal ne ya yarda tsin tsinyar hannun shi yayo kanta da sauri kamata yayi ta mik'e da kyar ta shiga d'aki da taimakon Kamal.

     Aiciwo kamar jira yakeyi tashiga d'akin yayo mata gangami, sai juye-juye takeyi cikin ikon Allah ko mintin sha biyar batayi da shiga d'akinba Allah yasauketa lafiya, ta haifo kyakykyawar 'yarta 'yar nafad'owa uwar matabiyo, wani dogon numfashi taja tasauke tare dayin hamdala ga ubangiji da yarabata da cikin jikinta Lafiya.

      Idanuwa ta zubawa 'yarta bayanta yanke mata cibi, idanuwanta suka kawo k'wallah Allah sarki Menat d'ina kinzo shigo cikin duniya mecike da mutane iri-iri masu mabanbantan halaye, wa'inda dayawansu kansu kawai suka sani kuma masu manta alkhairi, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarku keda d'an uwanki da dukkan 'ya'yan musulmi, ya Allah ga yarayana Allah kadube mu katallafa man ya Allah kabayyana min mahaifinsu, alfarmar Annabinka d'angatanka wanda kayi duniya da lahira dominshi ameen Mama Kamal ya amsa mata wanda shigowarshi kenan d'akin.

     Mama wai Abban mu yagudu? Da sauri ta d'ago kanta takslleshi tana me zubar da hawaye! A'a Kamal _Mahaifinku ba Guduwa Yayi ba_ toyana ina nima bansaniba Allah kad'ai yasani amma nasan bazai gudu yabarmu ba, aduk inda yake nasan hankalinshi yana kammu mucigaba da addu'a har Allah yabayyana manashi kaji d'an kirkir karkasake fad'ar haka kaji, ta idasa maganar tajawoshi jikinta.

     Gyara 'yarta tayi sannan itama ta gyara jikinta tsab ta nad'e kayan da ta'bata, kwantawa tayi kan yabu d'add'ar tabarmar d'akin tana sauke numfashi.

     Sannu mama yawwa Kamal kagan kanwarka ko yana dariya yace mama naganta itace Menat d'immu dakikace tana nan zuwa ko?
     Eh itace zaka kula da ita ko? Eh mama zankula da ita bazan bar Iowa yadaketa ba, yawwa d'an albarka kobayan raina karka barta tayi kukan rashin Mahaifa kaji? To mama sannan kafad'a mata wallahi _Mahaifinku ba Guduwa yayi ba_ kaji to mama zangaya mata yana amsawa cike da yarinta da wani babbane yaji wannan maganar dole jikinshi yayi sanyi abun kamar mebarin wasiyya amma haukar k'uruciya bata barshi ya fahimta ba hankalin shi yanakan Menat wadda ketafaman wawure-wawuren neman abincinta.-------------✍🏻

*_Bari umbarku haka naga ko zaisamu kar'buwa awajenku sai mud'ora nabarku Lafiya UMMUHFA'DIMAR kuce_*

Read & Share & Comments

VOTE#
VOTE#
VOTE#

HAƘURI BA YA ƁACIWhere stories live. Discover now