💞💞 *_HAK'URI BA YA 'BACI_* 💞💞
*_Labari me bantau sayi da Al'ajabi Me cike da sadaukarwa_*
*LITTAFIN*
*_NAFISAT ALIYU FUNTUA_*
*_(UMMUHFA'ƊIMA)_**_{MAGA YAƘ'IN KAINUWA⚔️⚔️}_*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Bismillahir Rahamanir Raheem!
'''INA YIWA ƊAUKACIN MUSLIMI BARKA DA SALLAH ALLAH YA MAI_MAITA MANA UBANGIJI ALLAH YA KARƁI IBADUMMU ALLAH YASA MUNA CIKIN BAYIN ALLAH ƳANTATTU MASOYIYARKU ƳAR MUTAN FUNTUA CE KE MUKU FATAN ALKHAIRI UMMUHFAƊIMA.'''
BABI NA 15~16Ɗagowa Kabir yayi ya kalleni, sannan yasakar min wani sassanyan murmushi, yace "insha Allahu nayi miki alƙawarin idan kika haihu lafiya zamuje inkaiki har gaban iyayenki kuma intayaki roƙon gafararsu" bansan sanda wani ƙarfi yazo min ba na faɗa jikinshi ina murna, da sauri ya riƙeni "haba Fatima meye haka kibi ahankali mana" sakinshi nayi ina dariya nace "wallahi bakasan irin daɗin danaji ba da ka amince zamuje inga Harɗo da Inna da Hammana nagode mijina" murmushi shima yayi yace "karki damu Fatima iyayenki ai iyayena ne kuma damani burina ako yaushe inganki acikin farin cikin nayi miki alƙawarin inde ina raye cikin hankalina bazan taɓa barinki acikin damuwa ba insha Allahu" "nasani mijina Allah yabarni da kai har ƙarshen rayuwata Allah karka kawo mana wata ƙaddarar dazata rabamu da juna" ameen ya Allah my wife.
Aranar akasallame muka dawo gida, tunda muka dawo gida ya hanani yin aikin komi kulawa ta duniya babu irin wanda bansamu daga mijina, saide abinda na lura da shi kamar suna takun saƙa da Hakiya Laure, amma idan na tambayeshi sai yade ya waske narasa abinda ke faruwa atsakaninsu bazan manta ba ranar wata juma'a da yamma lokacin cikina yashiga wata na tara, kasan cewar ranar dawwuri suke dawowa daga makaranta, yayi shirin masallaci dama yace min idan yaje massalaci bazai dawo dawwuri ba zai biya wani guri.
Ina zaune a ɗaki bayan na idar da sallar la'asar saina fito tsakar gidammu domin insha iska saboda zafin da akeyi, kujera ƴar tsugunno wadda akecewa tayani gulma ita na ɗauka nasa daga gefen kitching ɗimmu na zauna, banjima da zama ba sai na dingajin kamar tashin magana acikin zaure saboda dama kitching ɗimmu jikin zauren gidan yake.
"Waike wacce irin sheɗaniyar macce cene? Nifa ba haka nake ba kije chan kine mi irinki amma nide kam bazaki taɓa samun abinda kike buƙata daga gareni ba akullum ina neman tsari agurin Allah daga sharrinki" hhhhhhhhhhhhhhhh sautin dariya ya biyo bayan maganar kabir "kai yaro wallahi nafi ƙarfin indinga binka akan abinda bani kaɗai zan amfana ba saboda idan ka yarda dukkammu amfanuwar kammuce don haka ko kayarda da arziƙi ko karka yarda wallahi saina cimma burina akank.............. ƙarar marice ta katse maganar da sauri na miƙe nayi cikin zauren Hajiya Laure ce riƙe da kuncinta ga Kabir tsaye agefe yanata faman huci idanuwannan nashi sunkaɗa sunyi jawur kamar garwashin wuta.
Da sauri na ƙarasa garesu "subuhanallahi me yake faruwane?" Hajiya Laure tayi charaf ta amsa da "yawwa Fatima gwara da Allah yakawoki kika ganewa idonki abinda mijinki yayi min" tana magarne cikin shashshekar kuka gurinta nayi nariƙo hannunta nace "please kiyimin bayani me ya haɗaku ne?" kallon kallo naga sunayi atsakaninsu mitssssssssss kabir yaja wani dogon tsaki sannan yabar wurin.
Da kallo muka bishi mudukammu, saida yaɓacewa ganinmu hannuna Hajiya laure takamo tana cigaba da kuka tace " kinga wulaƙancin da mijinki yayi min ko Fatima kan naroƙi alfarma agurinshi" wacce irin alfarma kike nema agurinshi? "rancen kuɗi nace yabani inƙara ajarina saboda yanzu komi yayi tsada gashi mutane duk sun riƙe min kuɗina banida wani wadataccen jari shine fa yaketa wulaƙantani yanzuma abinda yasa natareshi anan danaga dawowarshi shine nace idama bazai bani aron ba to yabani akuɗin hayar ɗakinku idan lokacin biya yayi shikenan ba saikun biya ba shinefa ya kwaɗa min mari kamar Kabir ɗan cikina ace shine zai mareni" ta idasa maganar tana sheshshekar kuka hagga Allah ba wai nayarda da wannan dalilin bane zaisa Kabir ya mari Hajiya Laure ba amma ganin banida wata sheda akan hakan yasani yadda koda wani ɓangare na zuciyata yana ƙaryata hakan.
Haƙuri nabata sannan nace "kibari insha Allahu zanyi mishi magana meybe wanine ya ɓato mishi rai a waje" ta amsami da "babu komi nayafe mishi saboda nima nasan hakan ba halinshi bane nagode kije ki huta Allah de yasauke ki lafiya kinji Fatima" murmushi kawai nayi najuya nayi cikin gida.
Daret ɗakina wuce kwance na iskeshi yayi filo da hannuwanshi idanunshi na kallon rufin ɗakin, yayi zurfi acikin tunani, harna zauna kusa da shi beko motsaba saida naɗora hannuna akan fuskarshi sannan yaja wata sassan yar ajiyar zuciya nace "haba mijina uban ƴaƴana meya ɓata maka raine haka nide nasan mijina bashi da zafin zuciya mutum ne shi me sanyi, please idanni naɓata maka ka yafeni wallahi bada sanina bane kayi min uzuri kasan ajizanci irin na ɗan adam".
Na idasa maganar ina zubar da hawaye, jawoni yayi jikin shi yarungumeni sosai ya jima yana maida numfashi sai chan sannan yace "kukan ya isa hakanan bakiyi min komi ba kinji share hawayen ki kinji my beauty" bansan sanda nasaki murmushi ba cikin ƙan ƙanin lokaci saigashi yasaki jikin shi harmuna fira da dariya, mune ba mufito daga ɗakin ba saida akayi kiran sallar magriba, alwalla yayi ya wuce masallaci nima nayi alwalla na tada tawa sallar.
Tun daga ranar da abin yafaru dana tambayeshi bayan yadawo daga masallaci yace min inde har banason naga ɓacin ranshi kar inkuma tada mishi da wannan maganar, nikuma tundaga ranar bansake yi mishi maganar ba, koda safiya ta waye da yafita wurin aiki Hajiya Laure ta tambayeni yadda mukayi da shi kawai nace mata cewa yayi wallahi bashi da kuɗi amma idan yasamu zai bata.
Yau tunda natashi da safe nakejina sai ahankali amma kawai ina cijewa, kasan cewar litinince Kabir yana shirin fita wurin aiki, hakanan natayashi yayi shirin tsaf narakko shi har ƙofar ɗaki nayi mishi addu'a yatafi, na gyara ɗakina tsaf nayo wanka inade tajin kamar abu na sukata amarata amma ba sosai ba tun abun nayi kaɗan harya fara yawaita, gashi gida nika ɗai saboda tun da abunnan yafaru Hajiya Laure bata faya zaman gida ba domin idan ta fita tunsafe wata rana ma bata kwana agida kamar yau tunda suka fita jiya da rana ita da wata ƙawarta Hajiya Magajiya har yau basu dawo ba.
Tun ina dauriya har na sare chan wajen sha ɗaya da rabi na safe abun yaƙaru sosai ina duƙe aƙasa sai faman yarfe hannu nakeyi saboda nikaɗai nasan irin azabar da nikeji. Kamar daga sama naji maganar Kabir akaina yana "subuhanallahi Fatima lafiya?" marata kawai na iya nuna mishi, "sannu bari inje insamo mota muje asibiti kinji Fatima sannu" da gudu yafita befi minti biyar da fita ba saigashi sunshigo shida Baba Jimmai maƙwafciyar mu, ɗagani yayi chanchank yakaini mota.
Asibiti muka nufa muna isa aka amsheni cikin gaggawa na wahala sosai domin har suna bazan iya haihuwa ba saboda ƙarfina ya ƙare wajen 6:45pm likitan dake kaina ya fito, da sauri Kabir yatareshi yana doctor ta haihu kuwa? "a'a har yanzu gashi ƙarfinta yaƙare idan har kana buƙatar rayuwar matar ka to saide kasa hannu ayi mata aiki acire abinda ke cikinta" suman tsaye Kabir yayi tofa masoyan FALMATA kukawo agaji....................
*_GA GORON SALLARKU NAN MY PEOPLE NIMA INA JIRAN NAWA TUNDA BAKU BANI RAMADHAN BASKET BA SAIKU HAƊAMIN DUKA YANZU ASHA SHAGALIN SALLAH LAFIYA, SU O'O .KARDE ACI NAMA DAYAWA AZO CIKI YABURKICE ACIKAMANA SHADDAR GIDA BANKIRA SUNAN KOWA BA DUK WADDA TA TSARGU DA ITA NIKE _*
ummuhfaɗima111@gmail.com
*_UMMUHFAƊIMAR KUCE_*
YOU ARE READING
HAƘURI BA YA ƁACI
ActionLabarine akan Falmata ƴar Fulani da mijinta Kabir suna tsanin son junansu saboda ita Falmata bata da kowa sai shi amma dare ɗaya ta neme shi tarasa, gata da yara biyu ga wahalar matar da suke haya agidan, kai abumma sai wanda ya karanta abun tausayi...