Part 8

32 1 1
                                    

💞💞  *_HAK'URI BA YA 'BACI_* 💞💞
             

   *_Labari me bantau sayi da Al'ajabi Me cike da sadaukarwa_*

              *LITTAFIN*
*_NAFISAT ALIYU FUNTUA_*
       *_(UMMUHFA'DIMA)_*

Bismillahir Rahamanir Raheem

          *_Not Editing🔞_*

BABI NA 13~14

Munyi tafiya mai nisa sosai sannan me keken yace "wai ina zan kaiku ne?" Juyawa nayi na kalleshi shima d'in niya ke kallo murmushi yasakar min, nima martanin murmushin na miyar mishi sannan ya kalli me keken yace "yace idan ka kai wurin motocin chen ka ajiyemu awurin" da "to" ya amsa mishi. Ajiye mu yayi awurin da aka ce mishin, sallamar shi yayi yaja mashin d'inshi yayi gaba.

       Mun jima atsaye awurin kowa da abinda yake sak'awa aranshi, wani neyazo yayi mana sallama amsawa Malam yayi sannan yace "tafiya zakuyi ne? naganku tsaye ananne tun d'azu" ya amsa mishi da "eh tafiya zamuyi lodin ina da ina kukeyi? Anan wajen" mutumin yace muna lodin ko wanne gari anan " ok wacchen motar ina zata mutumin ya juya yakalli wurin da Kabir yake nunamishi inda wata gov ke lodi, "wachchen motar Dutsenma zataje" Dutsenma ya mai-maita aranshi sannan yacewa mutumin "eh muma chenmukayi" ok ba matsala muje gashi ko kunyi sa'a mutum biyu muke nema domin ta cika.

        Kayammu ya d'auka mukuma muka bishi a baya yasamana jakarmu sannan muka shiga cikin motar yabiyasu zuwa wasu 'yammintoci motarmu ta tashi muka d'auki hanyar Dutsemma, sai gab da mangariba muka shiga cikin garin saboda mund'an samu tsaiko a hanya, dai-dai wajen gidan mai total anan sukayi fakin d'in motarsu alamar nanne matsayarsu.

     Muma fitowa mukayi daga cikin motar kamar yadda kowa ya fice kayammu yad'akkomana muka bar wurin bakin titi muka fito tsayawa mukayi na d'an wani lokaci inga tunanin yadda zamuyi yakeyi aranshi. Kallona yayi yace d'an jirani anan inazuwa kinji karfa kije ko ina" da to kawai na amsa mishi.

        Wajen wani mutum mai shagon provision yaje, sallama yayi wa mutumin. Amsawa yayi yana d'ago kanshi ya dubeshi hannu yabashi suka gaisa, Malam ya "am don Allah tambaya nakeyi" mutumin yace. "To Allah yasa nasani" ameen "uhhmmh mu bak'ine kuma agaskiya bansan kowa ba agrinnan shine don Allah taimakon da nike nema awurinka ko kasan wani gidan haya don Allah ka taimaka min tare nike da matana". Shiru mutumin yayi kamar me tunanin wani abu sai da ya d'an jima sannan ya ce. " A gaskiya nide ban Sani ba amma muje wajen Auwalu me waldar chan k'ilanta shi yasani saboda niba d'annan layin bane" ok ba matsala muje d'in.

      “Assalamu alaikum Malam Auwalu barka da rana”. Wanda aka kira da Auwalu d'agowa yayi yana amsa musu sallamar da sukayi mishi, hannu ya mik'a musu suka gaisa yana cewa “a'a Nasiru kana lafiya? Yakuma kasuwartaku?” amsawa yayi yace “ Alhamdulillahi kasuwa da godiya”.

       Hannu ya mik'awa Kabir yace “barka” yawwa sannu da aiki wanda aka kira da Nasiru ne yace “dama abinda yasa kagammu wannan de bak'one mene man muhallin zama kamar yadda ya same ni da maganan kona san wani gidan haya anan kusa. Tonide na fad'a mishi akan bansaniba saboda nide ba'anan nake ba amma bari muzo wajenka tunda de kai anan kake.”
  
 
         “Ah masha Allah to bak'o barkanka da zuwa” Kabir ya amsa mishi da “yawwa” “eh to gaskiya de anan kusa inaga ba wani d'aki se agidan Hajiya Laure” “gidan Hajiya Laure fa kace bade Laure me abinci ba?” Nasiru ne yake yiwa Auwalun wannan tambayar. Amsa mishi yayi da “eh itade wadda kake maganar” juyawa yayi ga Kabir yace mishi “to kaikaji akwai wani d'aki ammafa adomin Allah bazan 'boye maka komi ba akan matar gidan mafad'a ciyace ta sosai sannan kuma bata da kirki kwata-kwata kuma idan lokacin biyan haya yayi batada uzuri itade kawai kabata kud'inta tokaji kad'an daga cikin halin Hajiya Laure. ”

HAƘURI BA YA ƁACIWhere stories live. Discover now