PART 2

51 1 0
                                    

💞💞 *_HAK'URI BA YA "BACI_* 💞💞
             

   *_Labari me bantau sayi da Al'ajabi Me cike da sadaukarwa_*

              *LITTAFIN*
*_NAFISAT ALIYU FUNTUA_*
       *_(UMMUHFA'DIMA)_*

*_{MAGA YAK'IN KAINUWA}_*

Bismillahir Rahamanir Raheem!

       _Masoyana ina mebaku Hak'uri akan rashin jin Cigaban *INDO AISHA* Hakan yafarune, Asanadin rasa wayata danayi, amma insha Allahu da zaran nasamu last, Pege d'in danayi zakujini da k'arashen shi, Insha Allahu dafatan zaku tayani nema. Nagode UMMUHFA'DIMAR kuce✋_

             *_Sadaukarwa ga dikkanku masoyana ngd da addu'o'inku agareni_*

follow me on telegram thanks
https://t.me/joinchat/HmqzDh2FIukO7at4

BABI NA 3~4

Kamal ne yace mama yunwa nakeji, hankalinta yak'ara tashi dama tsoronta kenan kar yaronnan yace yanajin yunwa domin batada abinda zata bashi, Ahalin datake ciki itama amatuk'ar buk'ace take da abincin.
     Tana cikin tunanin yadda zatayi da Kamal kawai sai jaririyarta itama tasa kuka saboda tagaji da rarime-rarimen neman nono, d'aukarta tayi da sauri tana jijjigawa amma kamar tana k'ara yawan kukan.

      Batasan fitar Kamal daga d'akim ba, saide banbamin fad'an Hajiya Laure tajiyo, wato ita ga shafaffa da mai wato tashige d'aki tayi bulum nikuma ga baiwar Ubanta wato shine ta turoka inkwashe jarina umbaku kucinye inrungume hannu to kaje kace mata muddun tanason nabata abinci ta fito tayimin, bauta nikuma inciyar daku.

        Hawayen fuskarta tashare, sannan tamik'e ta shimfid'ar da Menat datasamu tayi barci da kyar, tasan muddun ba fita tayi tayiwa Hajiya Laure aiki ba to tabbas bazata basu abinci ba koda dama ko, aikin tayi abinci datake basu be wuce Kamal ya cinyeshi, dama wajen wanke-wanke takesamu taci ta k'oshi irin raginnan da mutane ke bari acikin filet dakuma k'anzon dake atukunya.

     Kwanonin dake barbaje atsakar gidan sutafara har had'awa, ta kaisu wajen wanke-wanke komi takeyi cikin k'arfin hali takeyi saboda kowa yasan duk macen da ta haihu babu abinda take buk'ata kamar hutu.

     Hhhhhhhhhhhh habawa yarinya da yace miki barno gabas take aidade kinzauna acikin d'akin har Salen da yagudu yadawo ya yabaki abincin, k'anzon data kwashene acikin tukunyar wani har yafara bak'i shita d'igawa miya 'yar kad'an ta mik'o mata, gashinan shine rabonku yau domin ni abincina yakusa k'are kuma ga mutane da yawa kinsan ai bazan kwashe nabaku ba ga masu siya azaune ba.

     Hannu tasa tak'ar'ba tana godiya, wani saurayi ne yashigo cikin gidan wanda zai kai shekara sha biyar aduniya, dai dai Falmata tana fitowa daga cikin kitchen d'in a'a Maman Kamal bade kin haihu ba? Murmushi tayi eh aiko Allah yanufa, Masha Allah memuka samu?

     Menat kamal yayi karaf ya amsa, murmushi yakumayi kai kace nasamu mata Allah yasa me kyauce irinka? Eh tanada kyau, wow da kyau.
    Tofad'i ba'atambayeka ba yi hak'uri Mubarak kasan halin mutuminnaka da surutu, bari ind'akko maka ita kagani.

    'Dakin tashiga batare da tajira amsar shiba Babyn ta d'akko mishi wadda me nad'e cikin wani tsohon zanin atamfarta, fitowa tayi ta mik'awa Mubarak yarinyar.

      Amsarta yayi masha Allah kai gaskiya Maman Kamal kin iya haihuwa" masha Allah " Allah yaraya mana "Meenat Mekyau" murmushi kawai falmata keyi saboda yanda Mubarak yadage yanata zuzuta kyaun yarinyar koda ita kanta tasan yarinyar kam Masha Allah.

     Agaskiya Maman kamal ina kamu bari inje imfad'awa Hajiyarmu, nayi mata me kyau, ansar yarinyar tayi, tana "dariyar" shirmen Mubarak suka koma cikin d'akin abincin suka zaunaci,

      Mubarak mak'wafcin sune gida biyune atsakaninsu, Alhaji Auwal me takalma shine sunan Mahaifin Mubarak, mahaifiyarshi kuma Hajiya Halima macece me matuk'ar hak'uri ga kirki, duk fad'in anguwar ita kad'aice me taimakonsu Falmata, da abinci da sutura haka kawai Allah yasa mata matuk'ar k'aunar Falmata aranta yaranta Hud'u Zainab itace babba tayi aure tuni harda yaranta, sai Mubarak wanda yagama secondary school d'inshi yana jiran saka makonshi sai Jamil da Jamila sukuma ta gwayene 'yan shekara hud'u sune tsararrakin su Kamal wannan kenan.

       Mommy! Mommy!! Mommy!!! Na'am wai nikam yaushe zakayi hankaline Mubarak irin wannan kira kamar zaka ciremin kunnuwa, yi hak'uri Mommyna wallahi arud'e kai ko me yarud'aka d'annan? Maman Kamal ce ta haihu mommy kinga yarinyar kuwa wallahi kamar aljana saboda kyaunta ni har kusan tsorata nayi!.

      Hhhhhhhh kaide ahaka mutane keyi maka kallon me hankali, amma kaid'in sarkin shirmammune, huum mommy bazaki gane ba saikinga, Babyn wayyo saide abin tausayin kayan Kamal akasa mata kuma suma duk suntsufa gashi sunyi mata yawa!! Ya idasa maganar yana karyar da kai abun tausayi!.

      Allah sarki ai Falmata abar atausaya matace ai, eh wallahi mommy gawannan shegiyar Hajiya Murjar batada kirki ko kad'an to ya za'ayi haka rayuwa take kowa kagani, da irin tasa k'addarar, saide muyi fatan Allah yabamu “ikon cinye ko wacce irin kaddara ya kadarto mana arayuwa, ameen Mommy shikuma mahaifinsu Allah ya bayyana musu shi ta amsa da “Ameen".

    Bayan mungama cin abincinne na d'an samu na kwanta, kwanciyata ba da d'ewaba Assalamu alaikum" naji ana sallama a k'ofata, wa'alaikummussalam, Na'amsa inatashi zaune domin na gane muryar matar, Maman Jamil kishigo mana.

      Labulen d'akin ta d'aga tashi fuskarta cike da fara'a sannu Maman Kamal yawwa Hajiya sannuku, yawwa Ashe munsamu k'aruwa, uhuum to barkammu  Allah shi raya manasu akan sunnah, azuciyarta ta amsa da ameen saboda kasan cewarta cikakkiyar ba fulatana me cike da alkunya.

    Yarinyar ta mik'awa Maman Mubarak, masha Allah 'ya barkallahu masha Allah. Allah yasa cikon musulmai ce, ameen fira suka d'anta'ba sannan tayi mata sallama ta mik'e zata tafi wata jaka ta Ghana most go matsa kaiciya ta ajiyewa Falmata, a"a Hajiya hadda d'a wainiya kude baku gaji dayi mana d'awainiyya Ubangiji Allah yabiyaku, da mafificin alkairi Allah yabaku abinda kuke nema duniya da lahira nagode ta idasa maganar tana me fashewa da kuka.

     Haba Falmata gaskiya banajin dad'in abinda kikeyi duk abinda nakeyi miki inayi mikine domin Allah donni wallahi tunsanda nadawo unguwar nan da zama Allah yasamin k'aunarku da tausayinku araina domin inayi miki kallon k'anwata ta jini, kidena kuka kinji Falmata.

     Share hawayen nayi ina mek'ak'aro murmushi, domin ayanzude kaf duniyannan Maman Mubarak ita nikeyiwa  kallon kowa Nawa, bayan k'addara da rabo sun rabani da nawa 'yan'un, har soro narakata ina k'arayi mata godiya, anannanaga ashe nikad'aice agidamma domin bammasan fitar Hajiya ba, domin dama Maman Mubarak bata shigowa gidammu ko yomin aike muddin Hajiya Murja tanan tun radda taci mata mutunci.

     Kayane sosai Nagano acikin jakar harda famfas me d'ari da madaran yara ga kayansawa danawa Dana Kamal, kayan *Meenat* kuwa aisumfi nakowa yawa aciki, bayanna gama ganin kayan kukana naci sosai domin kewar Mijina takuma dawomin sabuwa, saida nagaji don kaina nayi shiru saboda babu me rarrashina, ina addu'ar nima Allah yakawo min ranar da zan  farantawa wa'innan bayin Allah ko kad'anne.
           *Wannan kenan.*

      *_Wacece Falmata kubiyoni domin jin wacece ita_*

*_Comments d'inkune zaibani k'arfin gwiwar cigaba da typing no comments no typing Ummuhfadimar kuce_*

Don't for get

*Pls Share*

HAƘURI BA YA ƁACIWhere stories live. Discover now