Part 4

44 2 0
                                    

  💞💞 *_HAK'URI BA YA "BACI_* 💞💞

   *_Labari me bantau sayi da Al'ajabi Me cike da sadaukarwa_*

              *LITTAFIN*
*_NAFISAT ALIYU FUNTUA_*
       *_(UMMUHFA'DIMA)_*

*_MAGA YAK'IN KAINUWA_*

Bismillahir Rahamanir Raheem!

       _Masoyana ina mebaku Hak'uri akan rashin jin Cigaban *INDO AISHA* Hakan yafarune, Asanadin rasa wayata danayi, amma insha Allahu da zaran nasamu last, Pege d'in danayi zakujini da k'arashen shi, Insha Allahu dafatan zaku tayani nema. Nagode UMMUHFA'DIMAR kuce✋_

             *_Sadaukarwa agareki Anty Fauzarmu Big Anty Shugaba ta gari munayi miki fatan alkhairi Adming Kainuwa writer's Allah yaja kwana_*

BABI NA 5 _ 6

Sunana Fatima amma amfi kirana da Falmata, kasancewar mu fulani nikaina bansan mu aslin 'yan ina bane, kasacewar nide tashi a Daura ne jahar Katsina a wani k'auye mesuna Rindi, Rindi shine asalin cikin garimmu amma mu ba'aciki muke ba kasancewar Mahaifina ba fulatanine irin fulanin masu yawo daji daji, kamar yadda Inno tata'ba fad'amin cewa sunyi yawon gari-gari amma Mahaifina beta'ba wuce, Shekara guda aduk jejin dasukaje, kasancewar duk Wanda yasan, Bafulatanin mutum bayason zama cikin gari.

       Dalilin dayasa kuwa muka tashi acikin rugarmu mesuna “Rugar Hard'o” alokacin da mahaifina yagama ciraninshi a wannan k'auyen, zai tafi ranar da zasu wucene Inna ta tashi da nak'uda ta dalilin dayasa akafasa wannan tafiya kenan awannan ranar, haka rayuwa tacigaba da tafiya, sannu sannu har Rugar Hard'o tafara yin yawa ta tashi daga Bukka d'aya, saboda bak'uncin wasu Fulani da muka samu alokacin ina 'yar shekara d'aya da watanni.

      Su Baffa Audu sunzo rugarmu cikin ikon Allah sai Allah ya had'a jininsu sosaima wanda har kowa acikinsu yaji bayason rabuwa da d'an uwanshi, sannu sannu akwana atashi ba wuya wajen Allah saiga Rugarmu ta dawo gari guda, alokacin Nataso yarinya kyakykyawa sonkowa k'in wanda yarasa, Allah yayimin farin jinin Samari sosai, amma nibana kula kowa saboda Allah yasani nide burina alokacin ba aureba burina inshiga makarantar arna wato boko saboda abin yana matuk'ar burgeni duk sati idan mukaje Daura cin kasuwa, innaga yara da kayan boko sai inji kamar ink'wace insa ajikina.

      Wasa wasa abun yazama jinin jikina ko barci nakeyi sai indinga yin mafarkin wai ganinan cikin makarantar boko ina karatu, tun Inna bata fargaba harta gane tasamu Hard'o da maganar, aiko ranar munga ruwan tujara saboda Hard'o yayi mugun tsanar karatun boko, wanda har saida Inna tayi datasanin gaya mishi, Niko ko ajikina duk wannan hargagin da Hard'o yayi sainajima kamar k'aramin son abun yayi.

      Yauce ranar da kasuwar garimmu keci dawwuri nashirya nida su Lantana muka nufi cikin gari kowa da k'waryarshi akai, Muna tafe sunata faman fira amma nikam hankalina yanachan wajen tunanin yadda zangudar musu inje inkalli 'yam boko saboda dama haka nakeyi duk ranar da mukazo tallan mu saina gudu wajen kallon 'yamboko.

     Cikin ikon Allah yauma kamar kullum nariga kowa Saidawa, na had'a kayana guri guda, na k'ulle 'yankud'ina aha'bar zanin jikina,  kunga nide nawa yak'are bari inje ind'an zagaya kasuwa kafin naku ya k'are saimu tafi gida ko? Aike kam kinji dad'inki yadda dakin kawo Nono har wawaso akeyi aradun Allah ki godewa Allah, huummh Salame kenan kuma ainaku zai k'are insha Allahu, to Allah yasa to ameen de bari inyi sauri indawo kunji “To saikin dawo" Allah yasa nafad'a ina barin wurin.

        Tafiya nayi me d'an nisa sannan na iso makarantar, ta tabayan azuzuwansu, nake la'bewa ina le'kensu, hankalina yayi nisa wajen kallon yaran da akeyiwa karatu, wani Malamine ke koya musu lissafi wato maths, keeeeee!! Naji andaka min tsawa da sauri nayi shirin rantawa anakare amma sede na makaro domin tuni wani mutumi yayi charaf dani, ubamme kikeyi anan? Ummhummh zaki bud'e baki kiyi magana ko saina zaneki? Ya idasa maganar yana d'aga zabgegiyar bulalar dake hannunshi.

HAƘURI BA YA ƁACIWhere stories live. Discover now