Part 7

35 2 1
                                    

💞💞  *_HAK'URI BA YA 'BACI_* 💞💞
             

   *_Labari me bantau sayi da Al'ajabi Me cike da sadaukarwa_*

              *LITTAFIN*
*_NAFISAT ALIYU FUNTUA_*
       *_(UMMUHFA'DIMA)_*

*_{MAGA YAK'IN KAINUWA⚔️⚔️}_*

Bismillahir Rahamanir Raheem!

       *_Masoyana ina mebaku Hak'uri akan rashin jin Cigaban *INDO AISHA_* *_Hakan yafarune, Asanadin rasa wayata danayi, amma insha Allahu da zaran nasamu last, Pege d'in danayi zakujini da k'arashen shi, Insha Allahu dafatan zaku tayani nema. Nagode UMMUHFA'DIMAR kuce🤝🏻_*

             *_Aslm sister's zakuga ansamu chanjin sunan littafi daga Ba guduwa ya yi ba Mahaifinku zuwa Hak'uri ba ya 'Baci amma labarin shine na chanjane bisa wani dalili dftn zaku bani had'in kai ngd_*

Please kuyi subscriber dina a YouTube channel dina sannan kudanna kararrawa domin Samar daku da zarar mun Dora sabon shiri thanks👇

https://youtu.be/FZ4YW96_Ym0

 
  *_Yaude ba editing kuyi hak'uri da kura kuren da zaku gani bani da enop charge ne shiyasa⭕_*

BABI NA 11~12

Ba wani tafiya bane me nisa sosai tsakanin Daura da Katsina, cikin k'ank'anin lokaci muka isa cikin garin katsinan dukko d'akin kara kunya garemu ba muda tsoro, tunda motar mu tayi fakin naji zuciyata na wani irin tsananta bugu kamar zata fito waje.

       Juyawa nayi nakkalli malamina da ya d'akko mana jakar da muka sa kayan mu aciki, “yade madam kallon nameye”? Ya tambayeni yana k'ara fad'ad'a fuskarshi da kyakykyawan murmushin shi. “Bakomi” “ok muje kinji” binshi nayi me keke napep ya tsayar mana, me napep d'inne ya lek'o yace “ina zakuje ne”? Shi ya amsar mishi da cewa “k'ofar guga” me napep din yace “ok muje” jakar yafara sakawa achan saman kujerar napep din sanan yace “shiga muje” shiga nayi na zauna inajin bugun zuciyata na da d'uwa, shima shiga yayi ya zauna,.

        Tafiya mukeyi inata kalle kalle abunku ga bak'auyar ba fulatana, wadda bata ta'ba  shugowa cikin babban birni ba. “yawwa shiga layinnan na wajen transformed d'inchan” kwanar muka shiga dai-dai gaban wani  babban gareji (get) yace “yawwa ajiyemu nan” sauka mukayi daga cikin napep din sannan ya biya shi kud'inshi. “Muje mana kinja kintsaya ai munzo gida,” jikina yakumayin sanyi lalle Kabir d'an babban gidane koda banshiga cikiba amma nasan daga ganin wannan gidan kasan ma mallakin shi ya tara abin duniya.

     Binshi nayi muka isa gaban get d'in gidan, kanshi tsaye ya bud'e k'aramar k'ofar yashiga rik'e k'ofar yayi har saida na shiga tukun yasaki, da sauri wani buzu da ya fito daga wata k'ofa rik'e da buta gaddikkan alamu ban d'akine, yace “a'a megida kaine tafe yanzu?” ya amsa mishi da “eh Baba nine sannu ya aikin da mutanen gidan ina fatan komi Lafiya?” “Lafiya lau alhamdulillahi ya bautar k'asar angama ko?” dariya yayi yace “eh Baba Allah ya nufa nagama duka" “ah Alhamdulillahi masha Allahu Allah yabada aiki me kyau” ya amsa mishi da "ameen ameen Baba nagode ya shin Alhaji kuwa yana gari?” “eh aiko yana gari domin jiya jiyannan shima yadawo garin”.

        Babanne ya d'aukar mana jakar kayanmu ya yi cikin gidan da ita mukuma muka bi bayanshi, zamishi ga cikin falon gidan shikuma Baban yana fitowa, Malam Kabiru yace “sannu Baba nagode" ya amsa da “bakomi kabir komi nayi maka ban fad'i ba saboda taimakon ka agaremu muya kamata mu gode maka” dariya kawai yayi sannan ya doshi hanyar falon gidan sallama yayi, duk mutanan falon suka zubo mana idanu suna kallon mu duk yawan mutanen dake falon ba asamu guda d'ayaba wanda ya iya amsa mana sallamar.

         Nikam gaba d'aya nakuma da burcewa ga zuciyata jinakeyi kamar zata fad'o k'asa saboda bugun da takeyi min, juyawa nayi nakkale shi gani nayi ko ajikinshi ga dikkan alamu yasaba da wannan halin nasu, wata 'yar dattijiwar mace ce ta shigo cikin falon,  “a'a Kabir kaine tafe sannu da zuwa“ ya amsa mata da "yawwa mama dafatan dukkuna lafiya?" Lafiya qlau muke Kabir kai ke tafe da bak'uwa? “eh Mama tare muke" matsowa tayi taja hannuna tana cewa "shine kuma kabarta atsaye Kabir kaide halin 'yam fari na  d'awainiyya da kai wallahi” dariya yayi kawai batare da yace komi ba kan d'aya daga cikin kujerun falon ta kaini na zauna cikin rawar muryanace mata “Ina wuni” aigaba d'aya 'yan falon suka kwashe da dariya, tsawa ta daka musu tace meye haka wallahi duk zan sa'ba muku, yaran duk sai sukayi tsit.

HAƘURI BA YA ƁACIWhere stories live. Discover now