Part 10

29 1 1
                                    

💞💞  *_HAK'URI BA YA 'BACI_* 💞💞
             

   *_Labari me bantau sayi da Al'ajabi Me cike da sadaukarwa_*

              *LITTAFIN*
*_NAFISAT ALIYU FUNTUA_*
       *_(UMMUHFA'ƊIMA)_*

*_{MAGA YAƘ'IN KAINUWA⚔️⚔️}_*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

Bismillahir Rahamanir Raheem!

BABINA 17~18

Mutuwar tsaye Kabir yayi saida doctor ɗin ya jijjiga shi yace "kana jina kuwa?" sannan yayi furgigit ya amsa da "eh doctor yanzu babu wata mafita?" ajiyar zuciya doctor ɗin yaja yace "gaskiya mafitar kenan acire abinda ke cikinnata" Baba Jummai ce ta matso kusa dasu tace "karka damu kaji Kabir insha Allahu za'a dace gwara kasa hannun ayi mata aikin saboda wannan wahalar da takesha zai iya taɓa lafyarta" shiru yayi na ɗan lokaci kafin yace " babu komi bani insa hannun" ok "biyoni office" .

       Suna tsatstsaye aka fito dani zuwa ɗakin aikin, najigata sosai duk jikina yayi sanyi anturo ni akan kujerar ɗaukar marassa lafiya muna zuwa dai- dai inda suke tsaya na kai hannu na riƙo hannun shi cikin sassanyar murya irinta wanda yagama jigatuwa nace "kayafe min mijina dukkan laifin da nayi maka nasan mutuwa zanyi! sannan ina roƙonka akan don girman Allah kaje rugarmu ka roƙa min gafarar iyayena kona samu rahamar Allah nagode da irin kulawar da kabani arayuwa mijina". na idasa maganar ina zubar da hawayen karaya!.

      Kasa cewa komi Kabir yayi saide wasu irin zafafan hawaye dake fita daga idanunshi yana kallo har aka shigar da ni ɗakin aikin ina wai wayenshi.

       Ya haɗa kai da bango yanata addu'ar Allah yafitar mishi da matar shi lafiya, jiyayi andafa shi juyowa yayi Baba Jummaice tace "kayi haƙuri addu'a kawai take buƙata kaje masallaci kayi sallah kaji anyi kiran mangriba daganan kaga sai kayi mata addu'a kaji ɗannan damuwar bata da amfani" da "to" kawai ya amsa mata sannan ya wuce zuwa masallacin.

       Acikin ɗakin tiyatar kuwa bayan sun shiga angama haɗa komi na aikin har anchanja min kaya zuwa na tiyata kawai sai sabuwar naƙuda ta tashi, likitocin suka rufu akaina cikin ikon Allah saiga kan ɗa ya turo, da taimakon Allah dana likitocinnan saigashi na haifi yarona lafiya ƙalau, anan suka gyara mu nida yarona sannan suka turomu akan gado zuwa ɗakin hutu.

        Likitan nafitowa yayi dai dai da shigowar Kabir yadawo daga masallaci, atare suka tari juna, "doctor ya matata take?" lokitan ya amsamishi da "kwantar da hankalinka matarka da ɗanka suna cikin ƙoshin lafiya, matarka ta haihu da kanta batare da anyi mata aikin ba" Alhamdulillahi! kalmar sa suka dinga mai-maitawa tsakanin Kabir da Baba kenan " yanzu suna ina?" Murmushi likitan yayi yace "muje ingwada maka su kuka yaƙare madam ta sauka lafiya ko?" dariya sukayi dukkansu sannan suka bishi zuwa ɗakin da aka kwantar damu.

      Ina kwance amma ba bacci nikeyi ba saiga su sunshigo kaina yayo daret kota kan ɗan bebi ba, "sannu Fatima ubangiji Allah yayi miki albarka Allah yaraya mana ɗammu" ameen ya Allah Baba ta amsa mishi tana miƙo mishi ɗan amsar shiyayi yayi mishi addu'o'i sosai sannan ya miƙawa Baba shi, ba'a sallame mu aranar ba sai washe gari da safe.

        Bayan mun dawo Baba tayi min wanka tayiwa yaron wanka tashirya mu tsaf abinci merai da lafiya Kabir ya shirya mana da kanshi dama tuni yasiya komi hatta kayan tea yasiyamana wanda zamu wuce arba'in basu ƙareba kayan Baby kuwa aiba amagana komi de masha Allah Baba ce ke kula damu sosai Hajiya Laure kuwa nide ko idonta bangani amma de naji tana yiwa Uban ɗan barka awaje.

       Ranar suna yaro yaci sunan Kamal ba laihi munyi taro ƴan unguwarmu duk sunshigo mana da matan abokan Kabir duk sun zazzo mana akayi taro lafiya aka watse, Baba taci gaba da kulawa damu, hakama muna samun kulawa daga wajen uban ɗan fiye da tunanin me tunani, har mukayi arba'in ɗana yayi gwanin ban sha'awa dashi ga yaron kyakykyawa yabiyo ubanshi sak babu ta ina yabar babanshi.

       Bayan watanni da haihuwata muka shirya tafiya ruggarmu, ranar wata labara wadda bazan taɓa mantawa da itaba arayuwata, munyi shirimmu tsaf nagoya yarona abaya tsaf, muka fito gidan Baba nashiga nayi mata sallama akan zan tafi garimmu tayimana fatan alkhairi tarakkomu har tasha bata bar wajen ba saida motarmu ta tashi sannan tayi gida mukuma muka nufi garin daura koda motar muta tsaya agarin daura, saina samu kaina da wani irin faɗuwar gaba jiki duk yayi sanyi sosai daga daura muka hau motar da zata kaimu Rindi wanda dagananne zamu samu mashin yashigar damu Rugar Arɗo.

        Bayan munsauka agarin rindi muka tari mashin akan yakaimu Rigar Arɗo amma abinda me masu mashin ɗin suka faɗa mana shi yayi mugun razanamu wanda har yasa komi yatsaya min chak..... tofa meyake faruwane? me masu mashin suka gayawa su Falmata ne? Tonima de banida amsar saimu biyo Falmata.................

*_YAWAN COMMENTS_*
*_YAWAN TYPING_*

*_PLEASE READ & SHARE_*

             *_UMMUHFAƊIMAR KUCE_*

HAƘURI BA YA ƁACIWhere stories live. Discover now