💞💞 *_HAK'URI BA YA 'BACI_* 💞💞
*_Labari me bantau sayi da Al'ajabi Me cike da sadaukarwa_**LITTAFIN*
*_NAFISAT ALIYU FUNTUA_*
*_(UMMUHFA'DIMA)_**_MAGA YAK'IN KAINUWA_*
Bismillahir Rahamanir Raheem!BABI NA 7~8
Ina gida ina jiran Hamma ya dawo inji yanda suka yi da 'yan boko, shiru shiru babu Hamma babu labarinshi har dare tun daga nan na sha jinin jikina a kan tabbas da matsala! Sai yamma sannan Hamma ya shigo, ko da ya dawo bai ce mini komi ba nima kuma ban tambayeshi komi ba duk kuwa da yadda na d'okantu a kan inji, amma haka na hak'ura na shanye a raina.
A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah ga shi yau kusan wata biyu da zuwan Malaman boko wanda tun ina sa ran ganinsu har na fara fidda rai, ba wai don na daina son karatun a raina ba a'a,sai dai ma abin da ya k'aru domin duk sanda na kwanta bacci sai nayi mafarkin malaminnan na boko, abun ya dameni na rasa hanyar da zan samu inganshi saboda Hard'o ya hanani zuwa talla kai ko k'ofar gida yanzu an hanani fita.
Ina kwancen a cikin bukkata dake gefen ta Innata abun duniya duk ya isheni ga shi kwanakin nan sai inji zuciyata na tsananta bugawa na rasa dalilin hakan."yawwa ku shigo kun ganta nan" naji ana fad'a wanda kafin inyi yunk'urin tashi ko insan abinda ke faruwa, kawai sainagan mutane saman kaina Inna Binta wadda take amatsayin k'anwar Hard'o ce ta amshi k'waryar dake hannu Hassatu mak'ociyarmu nonon dake cikin k'waryarne ta watsa min ajikina, sukuma sauran matan d'akin suka d'auki bud'a me k'arfi.
Nide nawa idone saboda bansan abinda hakan ke nufi ba, nasande wannan abun ba'ayiwa mutum shi sai wanda zaiyi aure shine akeyiwa haka kamar kamun Amarya yake nufi hakan, a al'adarmu ta Fulani tuna hakan da nayine yasa gabana yabada wani irin rassss!!! Wani tsoro! ya rufar min, karde tunanina gaskiyane duba da yadda na lura kwanakkinnan gidannamu jama'a na yawan shige da fice, da Sauri na mik'e domin zuwa intabbatar saide abun haushin anrife k'ofar tawa ta waje kuma hakan shiyakara gasgata min tunani na.
Komawa nayi na kwanta naci gaba da yin kukana wanda a kwanakkinnan dama shiya zama abin yina, tun injiyo hayaniyar mutane harna dena juyowa alamar dare yaja, inan cikin wani irin hali me wuyar kwatance saina rik'a jin motsi alamar ana bud'e k'ofar d'akin danake ciki, da sauri natashi zaune ganin Hammana ne.
Muryata na rawa saboda sabon kukan! da yazo min, Hamma meke faruw....... "Shiiiiii" yace min tare da sa hannunshi abaki alamar nayi shiru, aiko shurun nayi kuwa saboda banida za'bin da yafice yinshi, "hijabina ya d'akko min ansa nayi nasa hannuna yajawo muka fito, rife d'akin Hamma yayi a hankali kamar yadda yake ta bayan dannin gidammu muka fice, nide binshi Kawai nakeyi har seda mukayi tafiya sosai, don saida mukabar Rugar Hard'o gaba d'aya muka fara shiga gefen k'auyen Rindi, tsaye muka hango wani mutum jikin mashin yana hangomu shima ya mi'ke, saida muka isa wajen sannan nagane ashe Malamin Boko ne.
"Hamma yace yi ha'kuri Malam Kabiru nabarka kanata faman jirammu ko? "Lah aiban wani dad'e da zuwa ba nima, " to bakomi Kabiru ga 'kanwata nan Falmata ka ri'ke min ita da amana na yarda da kai shiyasa na aura maka ita saboda Allah yasani ina matuk'ar 'kaunar 'yar uwarta bazan iya zuba ido ba a aura mata wanchen d'an iskan ba, kamar yadda na fad'a maka gobe suke shirin d'aura mata aure dashi shiyasa na shirya wannan hanyar kuma ina fatan tazama mafita agaremu don Allah karka cutar da Fatima Kabiru, ya idasa maganar yana had'e hannuwanshi alamar rok'o".
"Nayi maka al'kawari Hamma zan kula da ita muddin raina kai sheda ne ina matu'ar 'kaunar Fatima tunda harna iya jure duk wani wula'kancin da aka dingayimin akanta nagode maka Allah yabar zumunci"
"Ameen Kabiru Hamma ya amsa mishi tare da juyowa kaina wadda ina du'ke agefe inata faman kuka murmushi yayi tare da d'ogoni yace " haba 'yar 'kanwata ai insha Allahu kuka ya'kare arayuwarki ki kwantar da hankalinki kuma burinki zai cika ai kingane kowaye wannan? Yana nunamin malamin boko kamar yadda nasa mishi, kaina na d'aga mishi alamar eh "kiyi magana mana bad'aga kaiba ba.
Da 'kyar nabud'e baki nace eh malamin boko ne na idasa maganar muryata na hard'ewa alamar naci kuka harna godewa Allah, " dariya Hamma yayi yace to yanzu mijinkine, idanuna nazaro cikin furgita! da bazata nakalli Hamma sannan na juya na kalli Malamin boko "kinyi mamaki ko? Hammana ya tambayeni kaina na jijjiga mishi alamar eh murmushi yayi sannan yace " tabbas Kabiru mijinkine wanda na d'aura miki aure da shi a yau a babban masallacin juma'a bayan an idar da sallar juma'a d'azu umbaki mantaba nayi miki alk'awarin inde ina raye bazan bar aurenki da Yawale yayiwu ba ko?.
"To Alhamdulillahi yauna sauk'e nauyin da na d'auka ko yanzu nabar duniya zantafi ina me farin cikin dank'aki a hannu na gari kuma kisani Kabiru yana matuk'ar sonki, ba tallarki na kai mishi ba shida kanshi yaje neman aurenki amma Hard'o yak'i saboda yariga ya amsawa Baffa zai bawa d'anshi ke, koda shima na tabbata bada son ranshi zai bayar dake ga Yawale ba, amma komi yazo k'arshe ni na yanke wannan hukuncin da kaina batare da kowa yasani ba fatana agareki kibi mijinki kuma kiyi mishi biyayya.
Wani sabon kukanne yakuma kufce min wanda ni kaina bansan nami bane na dad'ine koko nameye oho. Nasihohi Hammana yayi mana sosai sannan yaja hannuna yamik'awa Malam Kabiru yace "gatanan kutafi komi nata kaine Uwa Uba Yaya dangi bata da kowa sai Allah sekai karka kuskura ka kawota gida nan kusa kubari sai komi ya lafa, ninabarku lafiya Allah ya k'addara saduwar mu. Yajuya yana tafiya ga dikkan alamu shima kukane yataho mishi, nima kukan nakeyi ina kiran Hammana!Hammana!! Hammana!!! Karka barni kataho gareni, ina yunk'urin binshi, Kabir ne ya rik'eni sosai ya hanani binshi ina kallo har seda Hamma ya 'bacewa ganinmu sannan yajuya yata da mashin d'inshi yace muje kinji hawa nayi muka tafi zuciyata na dad'a tsinkewa hawayena sunk'i tsayawa. Wannan shine mafarin komi na rayuwata data d'iyana....... Kubiyoni a next pege domin jin k'arshen labarin Falmata.
*_Gashinan nakuma yi amma adomin Allah idan aka k'ara mai-maita min irinna last pege bazan kuma bafa Comments d'inku shi zai bani k'warin guywar yimuku typing ako yaushe._*
*_PLEASE READ & SHARE THANKS_*
💞💞 *_UMMUHFA'DIMAR KUCE_* 💞💞
YOU ARE READING
HAƘURI BA YA ƁACI
ActionLabarine akan Falmata ƴar Fulani da mijinta Kabir suna tsanin son junansu saboda ita Falmata bata da kowa sai shi amma dare ɗaya ta neme shi tarasa, gata da yara biyu ga wahalar matar da suke haya agidan, kai abumma sai wanda ya karanta abun tausayi...