💞💞 *_HAƘURI BA YA ƁACI_* 💞💞
*_Labari me bantau sayi da Al'ajabi Me cike da sadaukarwa_*
*LITTAFIN*
*_NAFISAT ALIYU FUNTUA_*
*_(UMMUHFA'ƊIMA)_**_{MAGA YAƘIN KAINUWA⚔️⚔️}_*
PEGE 19~20
Mashina suka tsayar ɗaya daga cikin su yace "Hajiya ina zakujene?" Kabir ya amsa mishi da "Rugar Arɗo zaku kaimu" kallon kallo mukaga masu mashin ɗin nayiwa junansu sannan ɗaya daga cikinsu yace "wacce Rugar Arɗo ɗin? Bade ta bayan gari ba?" da sauri natari numfashin shi nace "eh ita Rugar su Jauro" wani daga cikin ƴam mashin ɗin yace "amma de kun daɗe bakuje rigar ba ko? yace "eh gaskiya kusan shekara bakwai rabommu da nan ɗin meke faruwane?".
"Ah koda naji saboda Rugar Arɗo ta tashi tun wajen shekara bakwai baya kunga kenan tun wajen sanda kuka barta" Inalillahi wa'inna ilahirraji'u "yanzu kunason kuce min babu rugar ayanzu to ina mazaunan cikinta suke?" Kabir ya kuma tambaya, "muma de bamu sani ba saboda dare ɗaya muka tashi muka iske babu makiyayi ko ɗaya arugar sannan duk anƙona bukko kinsu ammade wasu nacewa ƙila ɓarayine suka shigo sukayi musu wannan ta'asar suka tafi da dabbobinsu saboda antsinci ƙonannun gawar wakinsu, amma ba'a gane kowa ba saboda sun ƙone ƙurmus!".
Ba wanda lura da Falmata wadda tayi mutuwar tsaye, aibata gama jin ƙarshen maganar mutanan ba tayi baya zata faɗi, da sauri Kabir ya ruƙota, mutane sukayo kansu da sauri wani acikinsu ya miƙowa Kabir ruwa ya yayyafa mata amma ta daɗe bata farfaɗo ba, sai cham taja doguwar ajiyar zuciya, tazabura ta miƙe tana wani irin kuka me cin rai, tana sabbatu "don girman Allah karkuce min Arɗona da Innata da Hammana sunƙone da gaske? Kuce min mafarki nakeyi ba gaske bane naroƙeku! wayyoni Allah nabani ina zansa kaina!".
Gabaɗaya duk wanda ke gurin saida ya zubarwa Falmata da hawayen tausayi! lokaci ɗaya gaba ɗaya tafice daga hayyacin ta! wani daga cikin masu mashin ɗin yace kuzo muje kuganewa idanunku yadda gurin yakoma" mashin ɗin suka hau suka nufi Rugar Arɗo ɗin.
Tashin hankali aisaida suka gwamce dama basu zo ba, saboda gaba ɗaya wurin yazama kufai babu komi yazama fili fallau, ai Falmata naganin yadda garinsu yakoma saida takuma yankar jiki ta faɗi awurin, bayan takuma farfaɗowa tayi cikin fikin gurin tana tafiya, tana kiran sunan ƴan uwanta saikace wadda za'a amsawa tafiya tayi harta kai wajen gidansu abunda yasama tagane wajen saboda dutsen dake kusa da randunansu, ƙarƙashin bishiyar mangwaro, koda bishiyar raƙone amma randunan suna nam saboda gina akayi acikin ƙasa aka saka su, kan dutsen ta hau tacigaba da sabbatun da kuka tana "Hammana kana ina kazo gani ina jiranka awurin fararmu nazo banganka ba nasande tanzu kadawo daga kiwo!" sabbatude iri iri tana kuka awurimma kawai akaga takuma shiɗewa.
Da sauri Kabir ya isa inda take aka yayyafa mata ruwa amma abanza ko motsi batayi ba, wani dattijo ne ya matso kusa da Kabor yace yaro kaɗauke ta daganan umba hakaba kota tashi saita kuma sumewa, rashin ahali haka yake da ciwo! amma babu yadda zatayi dole tayi haƙuri ta rungumi ƙaddara.
Ɗaukarta yayi wani acikin mutanen ya amshi Kamal da shima keta kuka kamar yasan abinda yake faruwa. Mashin suka hau daret cikin gari yayo dasu suna zuwa yasamu shatar mota har zuwa Dutsemma, lokacin ansamu da ƙyar ta farfaɗo tana numfashi sama sama, godiya yayiwa mutanen sannan me motar yaja su suka tafi, suna isa daret asibiti ya wuce da ita likitoci suka rufu akanta saida akasamu komi ya dai daita sannan ya wuce gida, gidan Baba yashiga yayi mata bayanin komi yabata Kamal tayi mishi wanka tabashi madara yasha yayi bacci sannan ta goyashi tayi asibitin wurin Falmata.
Tajima tana bacci domin bata farka ba sai chan cikin dare, koda ta tashi cigaba tayi da kukanta Baba da Kabir ne suka rufu akanta suna bata baki harta ɗan samu nutsuwa.
Kabir ne ya taimaka mata ta samu tayi wanka ta rama sallolin da aka biyota sannan ta ɗansha ruwan tea kaɗan sannan takoma ta kwanta, kwanansu biyar a asibiti sannan aka sallameta suka dawo gida Kabir ne yaci gaba da lallashinta yana bata baki harta ɗan fara saki.
Hannu bibbiyu ta rungumi mijinta da ɗanta saboda aganinta yanzu sune kaɗai gareta, akwana atashi ba wuya agurin Allah gashi Kamal harya shekara aduniya yayi girma abinshi yatake babu inda baya zuwa.
A lokacin kuma Alhamdulillahi Kabir yasamu cigaba sosai agurin aikinshi yasayi fili yanayi musu gini, alokacin kuma babban ɗan Baba yazo daga gari Mina inda yake aiki ya ɗauki mahaifiyar shi Baba ya maidata gurinshi Falmata tasha kuka saboda Baba ita takeyiwa kallo uwa, da ƙyar da lallashi suka rabu, ahaka rayuwar ta gangara da daɗi daba daɗi sunan zaune, rikicin dake tsakanin Kabir da Hajiya Laure sai abinda yayi gaba na rasa meye musabbabin abin natambayi Kabir amma yace min "bakomi" saboda haka yanzu kwata kwata yadena zaman gida idan kaganshi gida to darene da gari yawaye yake ficewa, ya maida hankalinshi kachokam akan ginin saboda yace min shifa yagaji da gidannan.
Baƙar rana wadda bazan taɓa mantawa da ita ba ranar wata talata bayan sallar ishsha'i na idar da sallah kenan saiga Kabir ya shigo da Sallama, amsamishi nayi sannan na ajiye Kamal wanda yau ya wuni yana darun kuka wanda narasa abinda kedamun shi saboda kuka ba sararshi bace.
"Sannu da zuwa Baban Kamal" murmushi yayi min sannan ya amsamin da "yawwa Amaryata kuma uwargidana ina fatan Allah ya barni dake har ƙarshen rayuwa ta" da "ameen ameen" na amsa zama yayi gefen gadommu yajawoni jikin shi yace "yace waike meye sirrinne? Naga sai wani ƙyalli kikeyi ne kode Kamal yasamu ƙanwane?" lah "a'afa ni banida komi kawai kaine sirrin dande baka kallon kanka kalli fa har wani teɓa kafara tarawa" na idasa maganar ina bugun cikin shi.
Dafe cikin yayi yace "wayyo Allah Ummina zata fasa min ciki" dariya mukayi gaba ɗayammu yace "Allah ba batun wasa yakamata ace Kamal yasamu Ƙanwa hakanan kingafa yakusa shekara biyu" nayi rau rau da ido nace " a'a nide ba yanzu duka yaushe na yayeshi ko watafa beyi da yaye amma kafara kiramun ciki kai harka manta wahalar da nasha ne?".
Huuuuoommm "bazaki gane bane wallahi ina buƙatar inga natara yara da yawa saboda nasan wata rana sune zasu tallafa mana insha Allahu don haka zonan da yardar Allah adaran saimun samowa Kamal ƙanwa ko ƙani" hhhhhhhhh "amma aikabari kaci abinci tukkuna ko?" "bazaki gane bane bari kawai idannasamu natsuwa naci abinci" " nidai a'a kabari muci abincin tukunna saiko mai ma ya biyo baya" " bazai yiwuba haƙuri zakiyi muci maci abinci daga baya amma saboda babu lokaci" daganan bekuma bani damar komi ba aranar mun faranta ran juna fiye da tsammanin me tsammani aranar ya gwada min shi jangwarzo ne, sai bayan komi ya lafane ina lafe ajikinshi yake cemin "nagode nagode Fatima ina roƙon Allah yasaka ki cikin aljanna maɗaukakiya ya share miki dukkan hawayenki keɗin tadaban ce arayuwa ta ina roƙonki da kiyafemin dukkan wani laifi da nayi miki ina sani ko bani sane kema naya fe miki koda baki taɓa ɓata min rai ba" numfashi yaja sannan yaci gabada cewa "ki kula mana da yarammu Fatima kibasu kulawa sannan kibasu ilimi musamman na addini" jikinane yayi sanyi sosai kuma Allah ya hanani inmishi tambaya akan meyasa yake yimin irin wa'innan maganganun saikace me barin wasiyya.
Tare mukayo wanka muka fito atsakar gidam mukaga Hajiya Laure duƙe aƙofar kitching ko metakeyi awannan daren oho, ko bayan mun koma ɗaki haka yaci gaba dayimin wasu irin magan ganu wanda nide ba gane kansu nakeyi ba.................
*_PLEASE READ AND SHARE_*
💞💞 Ummuhfaɗima111@gmail.com 💞💞
YOU ARE READING
HAƘURI BA YA ƁACI
ActionLabarine akan Falmata ƴar Fulani da mijinta Kabir suna tsanin son junansu saboda ita Falmata bata da kowa sai shi amma dare ɗaya ta neme shi tarasa, gata da yara biyu ga wahalar matar da suke haya agidan, kai abumma sai wanda ya karanta abun tausayi...