💞💞 *_HAK'URI BA YA 'BACI_* 💞💞
*_Labari me bantau sayi da Al'ajabi Me cike da sadaukarwa_*
*LITTAFIN*
*_NAFISAT ALIYU FUNTUA_*
*_(UMMUHFA'DIMA)_**_{MAGA YAK'IN KAINUWA⚔️⚔️}_*
Bismillahir Rahamanir Raheem!
*_Wannan shafi gaba d'ayanshi nakine kiyi yadda kikeso da shi kiturawa Wanda kike so mallakin kine domin saboda ke nayi typing d'inshi inda badanke ba da wallahi nadena typing d'inshi amma albarkar kaza k'adan gare kansha ruwan kasko MOMMYN MEENAL marubu ciyar (AISHA HUMAIRA) Aminiyar k'ware wallahi ina matuk'ar alfahari dake kinzama jinin jikina Allah yaraya mana zuri'a ya albarkacesu da ilimi me amfani ameeen ina k'aunarki irin ba adadinnan_*
BABI NA 9~10
Tafiya mukayi sosai sannan yafaka mashin d'in agefen wani gida, koda bansan k'arfe nawa ba alokacin nasan dare yayi sosai duba da yadda ko ina yayi shiru babu kowa a waje kowa ya natsu, haushin karnuka ka wai ketashi.
Waya yaciro daga aljihun gefen wandonshi, mun iso kazo ka bud'e mana abinda kawai naji yace kenan ya maida wayarshi a aljihunshi, k'arar bud'e k'ofar ne yasa duk muka juya muna kallon k'ofar, wani matashi ne shima kamar Malamin bokon nufo mu yayi yana cewa “Kabir kuk'araso mana Amarya sannu da zuwa” hannuna Kabir yakama yace “muje” binshi nayi simi-simi jana yayi har cikin wani d'aki wanda daga ganin yanayin d'akin kasan d'akin saurayine saboda katifa ce kawai sai kujerun roba guda hud'u sai kayan kallo da fankar sama, sai 'yantarkace irin wanda baka raba d'akin samari da shi kasan cewar akwai wutar nefa shiyasa nasamu damar ganin duk abinda ke cikin d'akin.
Bayan yashigo dani d'akin ya ajiyeni agefen katifar, juyawa yayi yace “ina zuwa” nide da idanu na rakkashi, yad'an jima da fita sannan yadawo hannunshi d'auke da kula da ruwan leda, agabana ya ajiye kayan sannan ya zauna gabana yace “Fatima” d'agowa nayi nakalleshi yakuma cewa “kiyi hak'uri kinsan kowanne mutum da kalar tashi jarrabawar sede kowa yayi fatan ganin yacinye tashi jarrabawar yakamata kibar wannan kukan hakanan ga abinci nan kisamu kici sannan ki kwanta kinga dare yayi nisa sosai saboda yanzu kusan k'arfe 02:58am kinga uku saura kenan”.
Kaina na girgiza mishi alamar bazan ciba lalla'bani yayi da irin dad'in bakinsu na maza yasani naci abincin kuwa sosai saboda dama na jima rabon da nasa wani abu acikina, ruwan ya mik'o min nasha sannan shima yaja kular gabanshi yacinye sauran abincin sanan ya matsar da kular gefe guda, yace “to ki kwanta tunda de yanzu nasan abincin ya fad'a ko”? Ya idasa maganarshi da tambaya.
Kasa na kwanta yace “a'a tashi ki hau kan katifar kinji” a'a kabarshi zan kwanta ananma yayi nagode, na gyara kwanciyata ko minti biyar banyi dakwanciyaba bacci yayi gaba dani. Bayan yadawo daga masallaci sannan ya tasheni, “kitashi kiyi salla kinga har gari ya fara waye wa gwara idan kinyi sallar seki kuma kwanciya karrana ta fito bakiyi salla ba” mik'ewa nayi amma abin mamakin saina ganni kwance akan katifar d'akin bayan kuma ninasan ak'asa na kwanta, kallonshi nayi amma bance mishi komi ba murmushi yayi saboda yagane kallon tuhuma takeyi mishi.
Mik'ewa nayi tsaye waje muka fito ya gwada min band'akin, shiga nayi nayo fitsari sannan nad'aura alwallah a cikin d'akin nasameshi ya shimfid'a min abin salla, ina kwana na fad'a muryata adisashe saboda kukan danasha bana wasa bane.
“Lafiya lau Sarauniyar mata Fadimatuz'zahara'u kin tashi lafiya?” Lafiya lau na amsa mishi kaina ak'asa saboda wata irin kunyarshi nakeji, tasowa yayi daga kan kujerar robar da yake kai ya dawo gabana fuskarshi cike da murmushi. Yace “d'ago kanki ki kalleni kinji Fatima” d'agowa nayi nakkaleshi amma da sauri nayi k'asa da kaina saboda wani irin kwarjinin danaga yayi min.
Dariya yayi yace “ to tunda bazaki kallenin ba kibani hankalinki, domin magana zamuyi me muhimmanci kingande yadda komi namu yazo a juye ba irin na sauran mutane bako? Kaina nad'aga mishi yaciga da cewa “to inason mutsaya munutsu mubawa marad'a kunya inaso kidinga yimin kallon Hammanki domin ta hakane kawai zan samu insauk'e duk wani hakk'in da yabarmin, kuma inason ki ajiye duk wata kunya agefe duk abinda kikasan zaki iya gayawa Hammanki inason ki fad'amin kinji. Nikuma nayi miki alk'awarin tsaya miki akomi naki muddin inada numfashi ajikina bazan ta'ba barinki kiyi kukaba insha Allahu”.
“Kice wani abu mana kimbarni inata faman zuba nika d'ai” k'asa nakumayi da kaina nace insha Allahu za ka sameni meyin biyayya adukkan umarninka, murmushin shi mekyau yakuma yi yace “to Alhamdulillah naji dad'in maganarki, sai magana ta gaba ranar litinin insha Allahu zaki fara zuwa makarantar boko, wata irin zabura nayi ina k'walo idanu nace don Allah da gaske kakeyi, dariya yayi sosai sannan yace “eh da gaske nakeyi zaki fara zuwa makaranta burinki zai cika” aiban san sanda nayi wani irin tsalle na afka ajikinshi ba saboda dad'i wayyo Hammana kazo kaji burina yacika zamfara boko.
“wayyo zaki karyani irin wannan tsalle haka” da sauri najenye jikina cikin fara'a nace yi hak'uri kaji, murmushin shi yakuma saki “bakomi nide burina kiyi farin ciki arayuwarki.
Nagode nagode ubangiji Allah yabaka ikon sauke dukkan nauyin da yarataya akanka nande nadinga jera mishi addu'o'in nasara arayuwarshi yana amsawa da “ameen ameen”.Daganan nafara sakin jikina da shi Inda har nake tambayarshi ina iyayenshi suke ya amsamin da “iyayena ba anan garin suke ba ni asalina d'an garin bauchi ne amma zama yakawo mahaifina cikin garin katsina, kuma dukkusan karatuna agarin bauchi nayishi tun daga primary har secondary d'ina duk achen nayi, bayan nagama secondary d'inane nadawo gurin mahaifina inda anan najona karatuna a 'yar aduwa university katsina harnagama yanzu hakama dakika ganni anan n.y.s. wato bautar k'asa aka turoni yi anan ashe rabon had'uwar mune. Nika d'ene awurin mahaifiyata kuma nine babba aduk fad'in gidammu mahaifiyata ta rasu tun ina d'an shekara bakwai aduniya shiyasa ma natashi a hannun kakanni na wa'inda suka haifi mahaifiyata gidammu gidan yawane, saboda matan mahaifina uku kuma kowacce tanada yaranta amma sannu ahankali duk zaki san kowa.
Yacigaba da cewa “mahaifina yana matuk'ar k'aunata ada amma a yanzu bansan laifin da nayi mishi ba wanda ko gaisuwata ba ya amsawa. Kinji d'an taik'aitaccen tarihin rayuwata, kuka na fashe da shi nace kayi hak'uri kaji Baba zai huce k'ila laifi kayi mishi ba kasani ba, itakuma Mama Allah yajik'anta yayi mata gafara. “ameen Fatima nagode da addu'arki kinji”.
Kamar yanda yace kuwa hakane yafaru ranar Litinin nafara zuwa makarantar boko, aji hud'u ya kaini na primary tun bana fahimtar komi sannu sannu harna fara gane komi saboda irin yadda yake k'ok'arin koyar dani a gida duka boko da islamiyya kuma yasani a wata isamiyya datake acikin layin da muke ciki, koda dama ba yabon kaiba inde akan ilimin addinine banida matsalar komi, tini yagama abinda ya kawoshi a makarantar amma saboda karatuna ya k'ara lokaci shekarata biyu a makarantar saboda k'ok'arina yasani na zana jarrabawar bari primary, ranar danagama kuwa ina cike da farin ciki zanshiga babbar makaranta.
Gashi acikin shekara biyun nan munyi wata irin shaquwa da shi me k'arfi toko ina munatare gida da makaranta babu abinda ke rabamu, amma duk wa'innan shekarun da mukayi tare beta'ba kusanta taba amatsayin miji, se ranar da nagama karatuna na primary a wannan ranar ya amshi budurcina, tarairaya kam babu irin wadda bana samu daga mijina, komi nace inaso shiyake yimin wata shak'uwa da zazzafar soyayya suka k'ara shiga tsakaninmu daga nan muka had'a kayanmu, mukayi sallama kwatas d'in malamai, dake cikin gari daura muka nufi garin katsina wurin Family din mijina, mafari matsala!!!...............✍🏻
*_Gashinan yauma nayi muku inkunga dama kuyi comments inkunga hagu ku k'iyi kunji mutanena wallahi taraku nakeyi karkuyi fatan ganin ranar da zan amayar daku._*
💞💞 *_UMMUH FADIMAR KU CE_*💞💞
YOU ARE READING
HAƘURI BA YA ƁACI
ActionLabarine akan Falmata ƴar Fulani da mijinta Kabir suna tsanin son junansu saboda ita Falmata bata da kowa sai shi amma dare ɗaya ta neme shi tarasa, gata da yara biyu ga wahalar matar da suke haya agidan, kai abumma sai wanda ya karanta abun tausayi...