BAƘAR DUHUWA ⚫
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
© OUM-NASS 🏇
"BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM"
FITA TA ƊAYA
12 April 1998
"Kamar yadda kuka sani ko wani ƙarni yana zuwa da nasarori da kuma cikar muradai a cikinsa. Wannan ƙarninma haka yake, zai zo da sabbin abubuwa da kuma ɓulluwar sabon al'amarin da zai dulmiyar da wuyanku zuwa ƙasa. Abubuwan da aka shekara hamsin ana binne da su zasu haƙo kansu ta hanyar bayyanar haske mai ƙarfi da zai tarwatsa idanuwanku. Tabbas sau ɗaya ake samun irin wannan damarmakin a duniya, ba zan ce muku ga yanda za ku yi ba, amma kuna da damar da zaku daƙushe bayyanar wannan hasken a cikinku."
Cikin tashin hankali suke kallon fuskokin junansu, kafin daga bisani su mayar da kallonsu ga Bokan nasu da yake da wata mummunar fuska duk da bashi da wani jiki na arziƙi amma duk halittunsa a yamushe suke da kuma ban tsoro.
"Wani irin haske ne wannan boka Marshuƙul Jals? Ta wata alama zamu gane bayyanarsa mu daƙusar da shi?"Boka Murshuƙul Jals zai sake jujjuya abin tsafinsa ya ce "Ɓulluwar sabon tsuron da ya fito daga makusancin sarki. Wanda ke bashi kariya ta kula da shi, a cikin tsakiyar duhun dare da kuma sauƙar ruwan sama mai tsanani. Duk lokacin da kuka ga sama ta kece da ruwa da kuma mutuwar itaciyar da ta fidda ɗa, ina tabbatar muku wannan ita ce mai warware muku ko wani shirinku da kuka ɗauki tsawon lokaci kuna yi. Dan haka ku gaggauta tsigeta.."
Sake kallon shi suka yi cikin mutuwar jiki da rashin fahimtar falsafar shi, suka kalli juna na wani lokaci. Kafin suka hada baki tare da cewa.
"Duk mun kuma shiga rud'ani da rashin tabbas ga wannan al'amari. Kanmu ya sake kullewa fiye da lokacin zuwanmu wajenka. Shin zaka iya fayyace mana abinda ka ke nufi? Domin mu kamar makafi muke a gaban ka."
Cikin fusata ya ƙura musu ido, iya adadin lokutan da ya ɗauka yana wannan aikin bai taɓa cin karo da shu'uman mutane kuma kangararrun mutane daƙiƙain da basa fahimtar kome sai zalincin ba, kamar su.Sake buga sandar tsafin ya yi sannan ya kalle su a karo na babu adadi ya furzar da wani turirin zafi a bakinsa yace musu.
"Tabbas lokaci yana ƙara ƙaratowa, masu himma suna ƙara himmatuwa, masu fafutika suna kara jajjircewa, shin me ku ka tanadarwa wanzuwar hakan? Shin a haka zaku cigaba da tafiya ina sakawa kuna warware min? Taya zan lamunci ina isarwa kuna ƙoƙarin sai na maimaita muku abin da ya gabata, sam ba zan ɗauki hakan a matsayin sabon abu ba. Amma zan iya fuskantar kowanne ƙalubale ga kwakwalenku da basa fahimtar sauƙaƙƙen harshe. Dan haka ku ƙara himma gurin fahimtar abinda zan gaya muku dan ba wasa da sakarcin ya had'a mu ba, lokaci ya riga da ya gabata."Shiru suka yi tare da zare idanun su, suka kuma kasa da kai suna masu faɗin.
"Tuba muke ya shugaban bokayan kasar mu, hakuri mu ke baka, ba zamu sake aikata abinda muka aikata ba. kai kamar bango ne a garemu da muke karuwa a jikinsa muna tsayawa da ƙafafuwanmu, mabiyanka ne mu na gaske ba masu butulce maka ba." Suka fada a lokaci guda.Murmushin jin dadi yayi tare da nuna ikon shi yace.
"Sai ni ki guda sama maza gudu, sai ni namijin gamji me ture hassadar mai hassada! Giwa nake me tafiyar kasaita! Alfadari me hawan ban mamaki.Ni ne jiya ni ne yau! Ni ne na shekaran basassa, ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya! Guguwar Annoba lakume me karan kwana! Bishiyar kuka me tattara almatsutsai! Babban ifiritu me maganin kananun kananun aljanu, babban Shaiɗani kabuwaya! Ni dakalin majina a hauni a zame na hau mutum na zauna dai-dai! Ni ke bada sa'a a yi nasara kowa ya kamani ya kama hanyar shi."
Sosai yayiwa kan shi kirari sannan ya warware musu bayani da yayi musu kafin suka tashi daga gaban shi suka masu duka mishi kamar zasu mishi sujada, suka shiga fita da bayan sun. Sai da suka fita cikin kokon ramin, sannan suka sauke ajiyar zuciya. Suka kalli juna, kafin suka fara haura manyan duwatsu da kurmin suna kokarin fita daga cikin dajin.
Kallon juna suka yi, kafin suka samu damar fita cikin kungurumin jejin, suna shiga jinjina alamarin.
Kafin daya daga cikin su ya kalli daya abokin tafiyarsa yace mishi.
"Shin ka fahimci abinda Marshuƙul Jals yake nufi? Ko zaka warware min."
YOU ARE READING
BAƘAR DUHUWA
RandomLokaci da rayuwa wasu ababuwane da suke tsere da rige-rigen cimma junnansu. Har na tsawon zamani Bakwai akan iya riskar abin da aka bari a inda aka aje. Idanuwan da suka liƙe da lalimen neman shahara sukan tono ɓaunar da take neman kaifaffen hasken...