https://www.wattpad.com/story/273909650?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading
BAƘAR DUHUWA ⚫
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
© OUM-NASS 🏇
FITA TA TAKWAS
Zafin da jikinta ya ke da kuma rawar sanyin da ya ɗauka ya taimaka mata wajen ƙara mata azaba ciwon da ke jikinta. Tana jin numfashinta kamar baya isa ga huhunta, tana jin wani abu na curewa yana tokarewa a ƙirjinta.
Tun bayan faruwar wannan al'amarin take jin jikinta babu daɗi, tana jin kamar an ɗora mata wani gugumen nauyi daga kanta zuwa ƙirjinta, nauyin da bata san wa zai kama mata shi su sauƙe ba, bata da tabbacin yaushe ne zata rabu da shi.Da sallama ya shigo gidan ganin bai ji motsinta ba ya kutsa kansa ɗakin, sai dai ganin halin da take ciki ya ƙara jefa shi cikin tashin hankali.
"Ya Asma mai ke faruwa?" Ya ƙara kusa da shimfiɗarta. Sai dai yana zama kusa da ita ya ji hucin zafin da jikinta ya ke.
"Subhanallah! Jikinki ai zazzaɓi ne ya Asma." Ya yi maganar yana tallafota zuwa jikinta.
Tuni fatar jikinsa ta ɗauki zafin hakan ya sa shi ƙara ruɗewa. "Kin sha maganinki ne?"Kai ta girgiza masa cikin zafin ciwon "Ba zan iya shan magani ba Ya Musa! Abin da ke damuna ba shi da maganin da zai iya warkar da shi." Ta yi maganar tana maida numfashi.
Hakan ya sa Ya Musa rintse idanuwansa, saboda jin kalamanta ya ke tamkar sauƙar yaji a cikin idanuwan nasa.
"Har yanzu dai akan wannan matsalar kike damuwa Asma? Mene ne yasa ba zaki yi haƙuri ki sanar da kanki cewar ba ke ce silar ciwon Abul-Nasr ba? Me yasa ba zaki ɗauki haƙuri da dangana kamar yanda iyayensa suka yi ba?
Duk soyayyar da zaki masa ba zata kai kamar ta iyayensa ba Asma."Kai ta kawar daga kallon fuskarsa tana jin taruwar hawaye a cikin idanuwanta "Na san ba ni ce na zama silar ciwonsa ba Ya Musa. Haka ba ni ce na yi naƙuda da rainon cikinsa ba, ban zama ɗaya daga cikin iyayen da suka yi silar zuwansa duniyaba.
Sai dai hakan ba yana nufin zan ji ƙasa da soyayyarsa akan ta iyayensa ba ne. Ba lallai ace mutum ya shiga zuciyar wani ya ɗauki wani al'amura na rayuwar cikinta da ke faruwa a tare da shiba.
Akwai ɗaci, akwai ciwo sanin ilimi da kuma ɓoye shi. Bani ce na ɗora masa ciwonba, amma ina ganin kamar ni ke da alhakin sama masa maganin da zai iya samun lafiya. Sai dai wata ƙaddarar ta datse min hanzarina akan al'amuransa. Wannan ƙuncin, wannan ciwon, shi ke addabar zuciyata ya Musa. Ina jin kamar zuciyata zata iya tsalle ta faso daga ƙirjina, ina jin ƙunci da zafi mafin ƙuntata a rayuwata.
Me yasa ne ƙaddara tafi wahalar da mutanen kirki? Me yasa ko wani lokaci azzalumai ne ke nasara a kan mutanen kirki? Me yasa?" Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka, kukan da yake fitowa tun daga ƙasan zuciyarta, kukan da ta daɗe tana so ta yi shi, tana kuma fatan faɗawar abin da ke ƙasan maƙoshinta zuwa cikinta.Ƙara rungumeta ya yi a jikinsa, yana jin tausayinta da shiga damuwar da ba ta shafeta ba, a yayin da gefe guda na zuciyarsa ya ke ƙara girmama al'amuran matar tasa.
"Allah S.w.a kan jarrabi bayinsa mafi soyuwa da jarrabawa mafi wahala dan ya auna ƙarfin imaninsu. Adadin wahala da ƙalubalen da ka samu a duniya adadin nasarar da zaka cimma a duniyarka da lahirarka.
Asma mutanen kirki sune waɗanda suke godiya ga Ubangiji a yayin da ya jarrabe su, suke kuma jure ko wani ƙunci da wahala ba tare da sun jingina wahalarsu akan wani ba, suka kuma haƙiƙance da yarda akan Allah s.w.a zai kawo musu sauyi a rayuwarsu.
Ki kula da kyau Asma, wanda ke aikata zalinci a duniya hankalinsa a tashe ya ke, ko wata rana a tsorace yake da ruɗewa akan fallasuwar al'amarinsa. Allah ya zuba musu ido ne dan ya ga ta inda wayonsu zai tseratar da su.
Mu ba wasu ba ne Asma, bamu da ikon sauya rubutun da ƙaddarar wasunmu ta yi, ko tamu ƙaddarar ba mu da ikon sauyata. Zamowarki mai magani hakan ba yana nufin zaki warka da duk wanda kika so ba. Asalima idan Allah bai amince ba sai kiga ko kin bada maganin ba lallai a ce an warke ba.
Ki cire ko wata damuwa a ranki, ki kula da lafiyarki ko dan abin da ke cikinki, wanda muka shafe shekaru masu yawa muna addu'ar samu."
Ya yi maganar yana ɗora hannusa akan cikinta, hakan ya sa wani sabon hawayen silalowa daga cikin idanuwanta.
YOU ARE READING
BAƘAR DUHUWA
RandomLokaci da rayuwa wasu ababuwane da suke tsere da rige-rigen cimma junnansu. Har na tsawon zamani Bakwai akan iya riskar abin da aka bari a inda aka aje. Idanuwan da suka liƙe da lalimen neman shahara sukan tono ɓaunar da take neman kaifaffen hasken...