https://www.wattpad.com/story/273909650?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_readingBAƘAR DUHUWA ⚫
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
© OUM-NASS 🏇
FITA TA BAKWAI
5 August, 1999
Aljani Surƙuƙul-Mulk ke faman kaiwa da kawowa a saman dajijjika da ke kewaye da nahiyar Bani Uwaisu, sai dai baya ganin kome da ke cikin nahiyar, asalima wani ƙaton haske ya masa iyaka da ganin abin da ke cikin Nahiyar.
Hankalinsa ne ya dugunzuma da rashin ganin abin da jikinsa ke bashi tabbacin yana cikin nahiyar ta su.
Sai dai manyan fika-fikan tsintsayen da kuma yanda suke ƙoƙarin lura da shi ya sashi ɓoye inuwarsa a cikin dajin.Wani haske mai ƙarfi ya fito daga ciki nahiyar bani Uwaisu ya faɗa kan ƙirjin Aljanin Surƙuƙul-Mulk. Nan take wuta ta fara cin ƙirjin nasa, hakan ya sa ya saki ƙara mai amo wanda dajin sai da ya amsa.
Tuni ya zama hayaƙi a wajen ya koma farkon dajin. Kamar wanda aka yi watsi da shi haka ya shiga mirginawa yana curewa a cikin rai-rayin saharar da ke wajen. Can kuma kamar an dakatar da shi ya tsaya a waje ɗaya yana lilo.
A lokacin ya rikiɗa ya dawo daga ainihin halittarsa mafi muni daga cikin jinsin Aljannu. Ƙwala-ƙwala idanuwansa ya shiga warawa, yana damƙar rai-rayin sahar da ke wajen, yana kaiwa saitin kafcecen hancinsa da ya wadaci a wulla a ƙaton gida a cikinsa.
"Tabbas wannan ƙamshin nasa ne. Kamar yanda alƙalamina ya shaida min afkuwar wannan al'amarin."
Wata ƙatuwar dariya ya kece da ita wadda ta haddasawa jejen girgiza, bishiyoyi suka fara rangaji kamar za su cire daga jijiyoyinsu."Anan zan kafa daulata, anan zan ci gaba da zaman jira har zuwa lokacin da zai bayyana a gabana, ya zama cikin ikona."
Tuni ya ƙara girgiza yana busa wata baƙar iska a bakinsa. Cikin abin da bai gaza mintina biyar ba wata baƙar guguwa ta karaɗai dajin, yashin sharar da ke wajen ya fara curewa yana tashi sama da sarrafa kansa.
Bayan daƙiƙa hamsin ƙurar ta lafa, dakarun Aljanun sa suka bayyana a gaban sa suna sunkuyar da kansu ƙasa."Mun amsa kiranka ya sarkin aljannu duniya."
Hanci ya hura wanda hakan ya tada ƴar ƙaramar ƙura a wajen.
"Wani sakamako kuka samo min dangane da binciken da na aika ku duniya a daren jiya."
Duƙar da kansu suka ƙara yi ƙasa "Muna kan bincikawa ne ya sarkin duniya. Ba mu samu alamar da ke nuna bayyanarta ba.""Shuru Muƙudar. Ni na samu alamar anan wajen, dan haka daga yanzu masarautar Turshuƙul-Maut ta dawo nan har zuwa lokacin da alamar zata gama bayyana anan. Dan haka ku hanzarta kafa min sabuwar masarauta ta."
Tun kafin ya gama rufe bakinsa suka fara curewa suna dunƙulewa a waje ɗaya, suna tada ƙura cikin abin da bai gaza minti arba'in ba suka kafa sabuwar masarauta a wajen.
Wata dariya Aljani Suraƙuƙul-Mulk ya saki sannan ya shiga masarautar da aka kafa masa ya zauna."Za mu jira muga ta inda za a keta iyakarmu. Ina so ko tsuntsu guda kada ku bari ya gifta nan ba tare da kun kawar da shi ba. Ina so ku kewaye Nahiyar Bani Uwaisu ta yanda babu wani abu da zai gifta a cikinsa ba tare da saninmu ba."
"An gama sarkin Aljannu duniya." Daga haka suka ɓace ɓat.
******
Hasken ranar da ya haska goshin jaririn ya sa shi buɗe idanuwansa yana sake rufe su. Ƙafarsa ya fara harbawa da ƙarfi jin babu alamun motsi a kusa da shi ya fara callara kuka, wanda ya amsa dajin gaba ɗaya.Tsssssiiii tssiiii sautin kukan tsintsayen ta fara zagaya jaririn suna masa rumfa da hasken ranar, a yayin da suka fara zagaye shi.
Hakan ya sa jaririn ƙif-ƙifta idanuwa yana binsu da kallo.
Har zuwa lokacin da babbansu ya zo ya zura bakinsa a cikin na jaririn yana zuba masa wani farin abu mai kama da madara.
Idan ya shanye sai ya sake tashi ya zagaya ya dawo ya sake sa masa a haka har sai da jaririn ya ƙoshi ya koma barci. Sai a lokacin tsintsayen suka koma hidimarsu ɗaya a ciki ta tsaya tana zagaya jaririn da ya ke sauƙe numfashi yana barci.
YOU ARE READING
BAƘAR DUHUWA
RandomLokaci da rayuwa wasu ababuwane da suke tsere da rige-rigen cimma junnansu. Har na tsawon zamani Bakwai akan iya riskar abin da aka bari a inda aka aje. Idanuwan da suka liƙe da lalimen neman shahara sukan tono ɓaunar da take neman kaifaffen hasken...