https://www.wattpad.com/story/273909650?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading
BAƘAR DUHUWA ⚫
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
© OUM-NASS 🏇
"BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM"
FITA TA UKU
Bayan sallah azhar Ya Musa ya fito cikin gaggawa, domin kai saƙon maganin da Ya Asma ta sanya ya sassako mata. Kiciɓus ya yi da Arwah bin Arshan. Babban khadimin Ubaidullah Mu'annas Ɗayyib. Kuma Arwah da zuri'ar su, suna da kafaffiyar tarihi a cikin masarautan. Manyan khadimai ne na haƙiƙa.
Shi yasa Ubaidullah ya ɗauke shi saboda yanayin tsarin sa da ɗabi'ar sa ya yi daidai da Arwah.
Murmushin fatar baki yayiwa Ya Musa. Kafin ya ɗauke kansa bayan ya daidaita tafiyar sa da ta Ya Musa.
"Nasan ba zaka rasa wata masaniyar akan Abul Nasr ba? Ko ita Ya Asma? Akwai wani sabon ci gaban da ake samu dangane da lafiyarsa?"Tsayawa ya yi cak tare da kallon Arwah bin Arshan.
"Kamar ya kenan?"
"Kamar yanda na tambaye ka, na san ka san mai na ke nufi.Kai Ya Musa ya girgiza "Hmm!" Ya faɗa sannan ya yi gaba abin sa, yana jin babu daɗi. Masarautan Buhayyir a cike ta ke da ƙananun abubuwa marasa dad'i da kyau. Jan numfashi ya yi tare da nufar hanyar sashin bayi. Duk in da ya wuce gaishe shi ake saboda darajar su da kuma matsayin su a gurin mai Martaba Sarki Mu'az Mu'annas Dayyib, uwa uba matar sa mai daraja ce Ya Asma, babbar likitan da take kula da lafiyar Yarima Abul-Nasr. Yana shiga ya same ta kamar kullum tana nazarin wasu magungunan, ƙurawa maganin ido ya yi, sannan ya nufi inda take ya dafa kafadar ta, bayan ya kuma maimaita sallamar da ya yi.
"Amin wa'alaikumun sallam. Barka da dawowa" Ta faɗa da maɗaukakin murmushi a fuskarta.
Ajiye mata kayan yayi tare da zama kusa da ita. "Sannun da aiki"
"Yauwa" ta faɗa bayan ta tattara duk nutsuwar da ta bawa Maganin ta ɗaura akan fuskar sa da ya gaza ɓoye damuwa da tashin hankali.
"Ko da ban san mene ne a cikin zuciyarka ba, amma na ji a jikina duk abin da yake bakinka ba ƙaramin abu bane, kuma ba wani sabon abu bane da zai dame ni, kamar ta kullum ce damuwar " ta faɗa tare da ƙura masa ido.
Zama ya yi yana kallon yadda take ƙara aikinta, bakinta yana rawa. Alamar addu'o'in take akan maganin.
"Ya Musa!" ta sake faɗa tana dakatar da abin da ta ke."Asma! duniya cike ta ke da mutane masu ɗauke da madafin zalimci, Allah ya basu aron rayuwa suna ta zabga abinda ransu yake so, mutanen kirki kuma an barsu da kaddarar su na ta zarga igiya a tsakanin wuyansu da ƙoƙarin daƙusar da su ƙasa."
"Idan ka faɗi haka kamar ka nunawa Ubangiji gazawar sa ne, karka taɓa kallon abin da mutanen banza suke, ko da yaushe buɗaɗɗiyar gaskiya ita ce sama da kome." ta faɗa tare da yin murmushin nasara akan aikinta.
Gyara zama ya yi yana kallonta, tun kuruciyarta take wannan hidimar, har yau bai tab'a ganin gazawarta ba sai akan laluran Abul-Nasr, bai taɓa ganin kukanta da damuwarta ba sai akan Abul-Nasr.
Ya sha farkawa cikin dare ya same ta tayi sallah ta dawo gurin maganinta tana aiki, bai tab'a zatan kaunarta da aikinta ya kai har haka ba, sai akan Abul Nasr."Tunanin me kake haka? Ko kana nazarin abin da yake faruwa ne?" Ta tambaye shi bayan ta zo kusa dashi ta zauna, tana me kallon shi cikin nutsuwa.
"Ban san me yasa nake jin daɗi idan nayi nasarar akan aikina ba, amma idan akan Abul-Nasr sai naga kamar kome lalacewa yake, sai naga kamar bana abin da ya dace ne."Shiru ta yi na wani lokaci kafin ta ci gaba da cewa.
"Ina tausayin yaron, ina son naga ya samu lafiya, ina son naga ya zama cikakken mutum kamar kowa, bana son ya ci gaba da wannan laluran." Ta faɗa hawaye na zuba daga cikin idanunta.
Ajiyar zuciya Ya Musa ya sauke tare da kallonta.
"Ina ji a jikina nasara tana dab da iso mu, amma yau she? Da wani lokaci ne? A wata shekara ne? Duk Allah shi kadai yabarwa kan sa sani. Rayuwar Abul-Nasr abar tausayawa ce, dan ma baki ga yadda Yarima Ubaidullah ya wulaƙanta mai martaba a gaban jama'a ba. Sai da naji kwalla ya zubo min."
YOU ARE READING
BAƘAR DUHUWA
CasualeLokaci da rayuwa wasu ababuwane da suke tsere da rige-rigen cimma junnansu. Har na tsawon zamani Bakwai akan iya riskar abin da aka bari a inda aka aje. Idanuwan da suka liƙe da lalimen neman shahara sukan tono ɓaunar da take neman kaifaffen hasken...