https://www.wattpad.com/story/273909650?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_readingBAƘAR DUHUWA ⚫
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
© OUM-NASS 🏇
FITA TA HUƊU
"Auwwwsh!" Abul-Nasr ya faɗa yana dafe kansa.
Hakan yasa Asma yin sauri wajen duba goshinsa da jini ke zuba, saurin yagar zanin jikinta ta yi ta dafe wajen da jini ke zuba a goshin nasa.
Cikin ruɗewa ta rungume Abul-Nasr, wani tashin hankali mara iyaka ne ya marabci zuciyarta, had'e da kuka mai sautin gaske. Wani mugun tsoron rayuwa da mutanen da suka kewaye ta da kaidinsu ya shige mata, bata san lokacin da ta kuma rungume Abul-Nasr a kirjinta ba kamar da za su dawo su sake ranata da shi, kuka mara sauti take tare da ƙara matse shi a jikinta."Wannan wacce irin rayuwa ce? Wannan wacce irin Fitina ce da take bibiyar daular Buhayyir? Yaushe za a daina irin wannan takun saƙar tsakanin masu bore da masu kula? Yaushe masarautar Buhayyir zata daina fusakantar wannan ƙalubalen ne?"
Hawaye ne masu zafi suka zubo a kan kwarmin idonta, wanda yasa Abul-Nasr ƙara ƙanƙameta, hakan ya sa ta kallonsa taga hawayen na sauƙa a goshinsa ne, saurin goge hawayen ta yi, sanann ta ɗago Abul-Nasr daga rungumeta da ya yi, ta zaunar shi akan cinyarta, sai a lokacin ta kula ba iya goshinsa ba ne ya samu rauni, hatta bakinsa ya fashe, jini na zuba a hefensa.
Ɗauke ƙyalle mai kyau ta yi ta jiƙa shi da ruwa ta fara goge masa goshinsa da bakinsa da suka tuje, tana jin wani irin tausayinsa na caccakar ƙirjinta. 'Sai yaushe ko mai zai wuce? Yaushe ko mai zai zama tarihi? Yaushe ko mai zai daidaita?'Yanzun shi sun mata barazana da mugun kulli, taya zata fara?.
***
Ita rayuwa cike take da ƙaddarorrin Ubangiji, sannan tun ranar gini tun ranar zane, da ace mutum yana da ikon tafiyar da ƙaddarar sa tabbas da haka ta faru tun a shuɗaɗɗan karni.Sau da yawan mutanen da kake tunanin sune zasu tsaya maka, ba su bane suke bada rayuwar su domin kai ba, sai dai wasu na daban da baka zata ba baka yi tsammanin su ba su ne suke dafa ma da tsayawa akan al'amuranka.
A duk lokacin da duniya ta samu yawaitar zubda hawaye da koke-koke na sauyiwar wasu al'amura masu girma da nauyi, sai ka samu tun tale-tale ake samun masu zubdawa, a lokacin da dubannin suka yi tafiyar bazata a cikin da'irar ƙaddararka, sai ka samu bila adadin sun yi zuwan ƙaddara rayuwarka hakan ne zai nuna maka yadda rayuwa take tafiyar angulu da zamaninnka da kuma muhimmanci ga wanda ya juro tazgaon da take tafe da ita.
Idan da bawa zai bawa kansa shawara tabbas da ya fara duba yadda Allah ya yi tsarin halittarsa, da kuma bada matsayi bayan matsayi tsakanin mutane da dabbobi ko da a cikin daji ne, zaka samu akwai shuwagabannin, balle kuma tsarin mulkin irin na Al'umma. Wanda sai ka yi tsayin daka gurin fuskantar al'ummar ka, sai ka yi faɗi tashi domin kafa al'ummar ka, amma kuma a hakan zaka samu wani daga can kana tufka yana warware maka.
Wannan ba wani abu ba ne domin tun daga Al'ummar farko aka fara haka har zuwa yau da komai ya ke tafiya kafaɗa da kafaɗa. Sannan irin waccan ya ci gaba da faruwa. Shin wane ne zai dakatar da faruwan haka?Daular Buhayyir.
Babban yanki ne daga yammacin Afirka, yanki ne da Allah ya albarkace ahi da abubuwa da yawa, kama daha manyan jarumai izuwa manyan Malamai da manyan attajirai.
Daga cikin abubuwan da Daular ta ke da shi akwai zinare, da ɗanyen man fetur. Sannan suna cikin ƙasashen da suke samun ruwan sama. Shi yasa suka kasance na gaba gaba a noman rani da damina, idan ka ga yadda Allah ya basu wannan baiwar zaka zata hankalinsu na zaune a waje ɗaya ne.
A labarin kunne ya girmi kaka, an sha jin labarin cewa garin ya jima da kafuwa.
Sarki Mu'annas Dayyib shine sarki mafi jimawa bayan sarki Dayyib. Sai dai sarakunan biyun sun fuskanci ƙalubale daga mutanen da suke jikin su, musamman yardaddun su, sannan, sukan mutu da baƙin cikinsu.
YOU ARE READING
BAƘAR DUHUWA
De TodoLokaci da rayuwa wasu ababuwane da suke tsere da rige-rigen cimma junnansu. Har na tsawon zamani Bakwai akan iya riskar abin da aka bari a inda aka aje. Idanuwan da suka liƙe da lalimen neman shahara sukan tono ɓaunar da take neman kaifaffen hasken...