https://www.wattpad.com/story/273909650?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading
BAƘAR DUHUWA ⚫
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
© OUM-NASS 🏇
FITA TA TARA
August-5-2000
Dajin Bani Uwais. Aljani Surƙuƙul mulk kallon Halwan shi ya yi tare da gyaɗa kai.
Duk yadda yaso hango iyakar dajin bai samu damar haka ba, lumshe idanun sa ya yi tare da takarkarewa ya fasa ihu, da kurawa wadda ya haddasa halwar tasa take girgiza kamar ba ɗɗkɗzai tsage.
Kwalla ne ya zubo masa daga manyan idanuwansa, daga ƙarni zuwa ƙarni ba karamin muguwar walaha ya sha ba, yana gagarari da lalimen neman matsaya na dai-daito da alƙiblarsa.
Sai da ya shekara sama da ɗari biyu yana neman masu irin tauraron jaririyar amma saboda rashin mutunci sun hana shi ganin ta ko da inuwarta ne.
A haka ya gaji da zagayensa ya dawo cikin dakarunsa ya zauna yana huci da jiran tsammani na zuwan lokacin da zata bayyana ta fito dan kanta.
A can cikin dajin kuwa takawa ta ke a hankali gashin kanta ya lulluɓe kanta baki ɗaya, kayan jikinta kuwa baƙaƙen kaya ne, wanda suka ƙara fidda Yanayinta duk da bata wuce shekara ɗaya da wani abu ba, amma haka ya boye Yanayinta da farin fatar ta.
A tsakanin fuskarta gashin kanta ne ya tsagu. Baka iya hango kome sai korayen kwayar idanun ta, lumshe shi ta yi tana kallon yadda tsuntsayen suke tashi, d'ago kai tayi tare da kukan kamar tsuntsayen. D'aga hannu tayi tana tsiii tsiii.
Juyowa wani baban tsuntsu ya yi mai launin baƙi da tambarin fari a goshinsa, sai da ya yaishawagi sama, sannan ya kuma dawowa tare da surar ta, yana wata irin ƙara.
Sauran tsuntsayen suna mishi ƙara da binsa kamar yanda suke yi, haka itama yarinya ke ɗaga hannu tana tsiii tssii kai sautinta na fita da irin sigar nasu kukan, suma kuma sauran tsuntsayen suka shiga mara mishi baya. Sunan kukan nasu. Abin kamar suna tseren gudu idan wannan ya wuce wannan sai wannan ya zo ya wuce shi, suna ratsa tsakanin duhuwar da ke cikin dajin nasu.
****
22 september 1998Duk da kasancewar sa mutum me adalci, sai dai baya jin a ransa zai ji cewar ya zalinci Ubaidullah, baya jin abinda ya yi a bisa kuskure ya aikata, duk abin da ya aikata akan Ubaidullah baya jin akwai buƙatar a ga laifin sa kamar yadda mutane dayawa suke ganin kamar zubewar darajar Ubaidullah ne aura masa ƴar ƙaramin gida.
"Allah ya taimaki Mai Martaba. Ka duba ka ga ni, akwai mutane da yawa daga attajirai da masu sarautu zuwa ƴan kasuwa, manyan jami'an gwamnati. Me yasa baka nemawa Ubaidullah auren yaran su ba? Sai ƴar karamar gida, yarinyar da fatara da yunwa yake jingine da jikinta, yarinyar da bata san yadda ake sarrafa malamai ba! Kowa yasan waye Ubaidullah! Kowa yasan girma da darajar Ubaidullah, tarin ilimin shi da wayewar shi bai cancanci wannan hukuncin ba. Ka duba ka gani."
Ta faɗa tare da sunkuyar da kanta, daukar butar shayin tayi tare da zubawa a karamin kofi. Ta tura mishi gaban shi, sai da ya gama nazarin jaridar kafin ya d'ago manyan daradaran idanun shi akan ta. Karamin murmushi yayi sannan ya mai da kanshi kofin shayin. Yana kurb'a tare da gyara zaman kishingid'ar da yaji yana kallon ta.
"Ban kalli tarin yalwa da buɗin da Ubangiji yayi min ba,ban tab'a jin ko ganin kuskure akan abin da na aikata ba.!" Fasali yaja tare da kallon kofin shayin, yana jin wani irin yanayi a ranshi.
"Laifi yayi na hukunta shi,sannan ita kanta yarinyar nagartacciya ce,haka kawai ba zan dauki abin da nasan ba zai iya gyara mishi alkibla ba. Ubaid bai da kirki ina fatan wannan haɗin ya sauya mishi ƙaddaran shi."
YOU ARE READING
BAƘAR DUHUWA
RandomLokaci da rayuwa wasu ababuwane da suke tsere da rige-rigen cimma junnansu. Har na tsawon zamani Bakwai akan iya riskar abin da aka bari a inda aka aje. Idanuwan da suka liƙe da lalimen neman shahara sukan tono ɓaunar da take neman kaifaffen hasken...