BAƘAR DUHUWA ⚫
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
© OUM-NASS 🏇
FITA TA BIYU
Yana bin su da kallo har suka ɓace daga ɗakin suna rufo masa ƙofar a hankali, hawayen da ya ke dannewa ne suka ziraro daga idanuwansa.
'Ya sani ko wani abu a rayuwa akwai yiyuwar shuɗewarsa, haka matsala da laruru suna da ƙayyadadden wa'adin tafiyarsu. Amma kuma yaushe ne? Ta ina ne? Waɗannan bashi da amsarsu sai Ubangijin da ke juya zamani da lokaci ne yasan lokacin faruwarsa.'Taɓa kafaɗarsa da aka yi da kuma ƙamshin da ya marabi hancinsa shi ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya shiga.
Idanuwansa ya ɗora akan kyakkyawar fuskarta da take ɗauke da zagayayyen kwalli a idonta, sai baƙin bakin da ta rine fatar bakinta da ita, wanda ya ƙarawa farar fatar fuskarta haskawa.
"Ya Amin ka yi sani cewa babu wani sauran ƙuncin da ya ke ragewa a duniyar nan. Kamar yanda zagayen launin ƙaddara kan zama mabanbanta a lokuta masu yawa. Idan har a matsayinka na amintacce a garemu ka samu rauni, ya kake tunanin kalar nawa raunin zai kasance? Musamman idan ka danganta zamowata uwar da ke ɗauke da nauyi da kuma rauni a lokaci ɗaya."Idanuwansa ya lumshe kafin ya sauƙe wani hucin zafi a bakinsa. Ya sani a rayuwa an hallice shi ne a wani yanki mai girma an kuma ɗaukaka matsayi da darajarsa, kamar yadda aka ɗora masa nauyin mutane da yawa a tare da shi.
Sai dai nauyin mutanen da ya ke mulka baya rinjayarsa kamar yadda na iyalansa suke rinjayarsa. Musamman Gimbiya Aziza da ta kasance mafi ɗaukan wahalhalu da kuma jure ko wani irin al'amura da suka shafi rayuwarsa.
Haka kuma ita ce wararriya a cikin duka matansa wadda ta ke a matsayin zaɓinsa, kuma ƙaddara ta juya akalar rayuwarsu ta fidda kyakkyawan furrai a tsakanin inuwar haɗuwarsu, Furran da ya kasance mai haske da laushi, mai kuma rauni cikin raunannun ahali."Har zuwa wani lokaci zaka ci gaba da tattaunawa da zuciyarka ya Amin?" Maganar Aziza ta sake dira a kunnuwansa a karo na biyu.
Hakan ya sa shi yin murmushi yana girgiza mata kansa "Ban sani ba Aziza! Ban san adadin lokacin da zan iya ɗauka a hakan ba.
Sai dai ina ji a raina ko wani abu ya zo a tsaginki yakan kasance mai muhimmanci sosai koda ace duniya zata kalle shi da mafi ƙasƙanci a cikin ƙasƙantattu."Ajiyar zuciya ta sauƙe a hankali sannan ta ƙaƙalo murmushi a kan laɓɓanta "Ba dai kana sake magana akan matsalar Abul-Nas ba?"
Bai yi magana ba ya ɗaga mata kai yana tauna laɓɓansa.Murmushi ta yi wanda ya ke nuna cewar ɗabi'arta ne yinsa a ko yaushe "Har zuwa wani lokaci zaka ɗauka kana damuwa akan larurar da ta zama jiki ga Abul-Nas? Ko ka yi tunanin hakan wata baiwa ce da falala a tare da shi na zuwansa a cikin saɓaɓɓiyar halittar da take nesanta shi daga hidimar mulki da kuma mugun ido. Musamman da ya kasance ƴan uwansa mata ne."
Kai sarki Mu'az ya kawar gefe daga kallon Aziza a hankali ya fara magana "Shin ba ki lura cewa duka ƴan uwansa suna da wani miki a tare da su ba? Duk da kasancewarsu mata ne hakan bai hana su kawar da kai da nuna halin ko inkula a kaina da mulkina ba Aziza. Asalima suna fafutuka ne tsakanin ra'ayinsu da muradan zuciyarsu. Gashi Maleeka ta faɗa harkar siyasa, Ma'isha kuma ita ba a maganarta ma tun da ta shiga cikin aikin (N.G.O) bata san ya na ke ba me ke faruwa da ni. Duk da kasancewata tsayayyen uba a garesu.
Ki kalli Kaashif har tsawon shekaru goma sha biyu ya yi yana fama da larura irin ta Abul-Nas kafin ya yi ciwo mai tsanani ya koma ga ubangiji. Haka Ƙasim ma Aziza. Ina jin tsoro akan abin da ke faruwa da yarana maza ya sake faruwa da Abul-Nas. Ina jin tsoron shima kada ya tafi ya barni Aziza. Shi kaɗai na ke gani a kusa da ni, shi kaɗai ya ke damuwa da matsalata duk da bashi da wadatacciyar lafiya a tare da shi."Ido Aziza ta lumshe tana jin taruwar wani abu a maƙoshinta, wani abun da ya ƙi faɗawa zuwa ƙasanta. Ba zata iya tuna adadin lokacin da ta ke ɗauka tana zubar da hawaye da neman amsa akan yanda igiyar ƙaddara ke wahalar da ahalin sarki Mu'az ba. Amma kuma bata so ta fiddo da rauninta fili ta ƙara masa sabon ƙunci akan wanda ya ke ciki.
YOU ARE READING
BAƘAR DUHUWA
RandomLokaci da rayuwa wasu ababuwane da suke tsere da rige-rigen cimma junnansu. Har na tsawon zamani Bakwai akan iya riskar abin da aka bari a inda aka aje. Idanuwan da suka liƙe da lalimen neman shahara sukan tono ɓaunar da take neman kaifaffen hasken...