https://www.wattpad.com/story/273909650?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading
BAƘAR DUHUWA ⚫
®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
© OUM-NASS 🏇
FITA TA GOMA
2 October 2000
Iska ce mai ƙarfi take kaɗawa a dajin, bishiyoyi suna rangaji kamar za su zubda rassansu. A yayin da baƙaƙen tsintsayen suke kaɗa fika-fikansu suna zagaya saman bishiyoyin da suke dajin, tsiiii tssiii suke jera kuka a tare kamar masu rera waƙe.
Yanayin yanda ta ke tafiya da kuma rashin hanzarinta zai sa ka tsammaci babu abin da ke faruwa a dajin, duk da shekarunta ba za su haura biyu ba, amma salon yadda ta ke tafiya a hankali da kuma miƙewar gashin kanta ya isa ya sheda ma cewar wani abu baya tafiya dai-dai a tare da ita.
"Tssiiii, tsiii!" Sautin kukan wani tsuntsun ya cika dajin, sautin da yafi na sauran amo da ƙaraji. Hakan ya sa ta saurin ɗago korayen idanuwanta da su kaɗai ake iya gani a fuskarta taɗaga tana kanne idanunta guda ɗaya, ganin tsuntsun ya fara sauƙowa ƙasa yasa ta saurin ɗaga hannunta sama gashin kanta da ya mata rumfa a fuskarta ya ƙara rufe korayen idanuwanta.
A hankali tsuntsun ya sauƙa a gabanta ya fara kakkaɗa fiffikensa a hankali kamar mai mata fifita, sannan ya risinar da kansa ƙasa "Tsiin tsunnn tsutt tsii." Ya shiga rera mata sautin.Hakan ya sata sauƙe ajiyar zuciya, wadda ta haddasa ɗaukewar iska mai ƙarfin da ke kaɗawa a wajen.
Hakan ya sa sauran tsuntsayen suma sauƙowa ƙasa suka yi abin da wancan tsuntsun yayi.
Gashin kanta ne ya kaɗa ta fara sautin kukan da suke, har a lokacin fuskarta rufe ta ke da gashin kanta.
Juyawa ta yi daga wajen tsintsayen ta nufi wani wajen wata bukka da aka yita ƴar ƙarama dai-dai ita, sai dai tana saman wata bishiya ne ƙarama da bata da tsayi, amma tana da yalwar ganyayyaki.
Hannunyenta ta wara duka biyun, sai dai abin mamaki sai gashi tana yin sama har ya iso wajen da bikkar ta ke ta shige a binta.*****
A zabire ya miƙe yana buga kafceciyar ƙafarsa a cikin rairayin sahara wanda hakan ya sa halwarsa girgiza kafin ya ankare ta tarwatse gaba ɗayanta.
Ransa ne ya dugunzuma idanuwansa suka fara fidda hayaƙi, kafin wani lokaci hancinsa ya fara feshin wuta.
Tuni dakarunsa suka tsorata da ganin yanayinsa, domin basu taɓa ganin Shugabansu ya yi irin wannan fushin fa."Ran sarkin aljannun duniya ya huce. sarki sarakai na duniya mai ƙarfin iko da jujjuya duniya a tafin hannunsa! Wanene yace ba kai ba mu nuna masa ƙarshensa. Wa ke shirin tado da yaƙin duniya yanzu mu hautsinata. Kai ne Sarkin Aljannu duniya Surƙuƙul Mulk, kai ne maganin rafkanannen mai rashi jin magana."
Bakinsa ya buɗe yana ƙara hura hancinsa, har a lokacin feshin wuta na fita tsakanin ƙofofin hancin nasa, da kuma bakinsa da ya buɗe.
Sai da ya ɗauki tsawon daƙiƙa hamsin sannan ya rufe bakin nasa, feshin wutar ta ɗauke daga hancin nasa. Hayaƙin da ke fita a idanuwansa shima ya ɗauke cak. Sai dai bangon ginin ke faman ci da wuta kamar zai hallakar da su gaba ɗaya."Kome ya ƙare min Suzan. Kome da na ke killacewa da ɗora burina akan zai kasance ƙarƙashin ikona ya tarwatse.
Tasirin Ikon da ke tare da ita zai iya lallata nawa ikon Suzan. Zan sake komawa dajin Bani Uwais, zan fafata da su har sai na dawo da ita ƙarƙashin ikona."Wanda ya kira da Suzan ne ya sunkuyar da kansa ƙasa, yana kaɗa fiffiken da ke jikinsa a hankali, da kuma cure hannayensa waje ɗaya.
"Ƙarfin ikon mulkar duniya ya kasance wanzazzai a gareka ya shugabana Surƙuƙul Mulk. Nasara da tasirin sihiri su zama sarrafaffun abubuwan da ke cikin ikon Surƙuƙul mulk.
YOU ARE READING
BAƘAR DUHUWA
RandomLokaci da rayuwa wasu ababuwane da suke tsere da rige-rigen cimma junnansu. Har na tsawon zamani Bakwai akan iya riskar abin da aka bari a inda aka aje. Idanuwan da suka liƙe da lalimen neman shahara sukan tono ɓaunar da take neman kaifaffen hasken...