FITA TA BIYAR

63 10 1
                                    

https://www.wattpad.com/story/273909650?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

BAƘAR DUHUWA ⚫

  ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

© OUM-NASS 🏇

FITA TA BIYAR

    4 August, 1999

Garin ya yi duhu ƙirin, baka jin sautin komi sai na rugugin hadarin da ya gama zagaye sararin samaniya. Cida na ta rugugi wanda ke ƙara tsoratar da duk wani bawa da ke doron duniya.
   Kafin a yi walƙiyya mai haske a kuma kece da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.

    Kukan jariri ke amsa amo a cikin wata duhuwar jeji da babu kowa a cikinta, babu kuma  motsin alamun mutane na wucewa ta wajen balle a tsammaci rayuwarsu a wajen.
   A hankali sautin kukan ke ci gaba da cika dajin a yayin da ruwan sama ke ƙara ƙarfin sauƙarsa.
  "Tssssiiii... tsiii." Sautin kukan tsintsaye ya fara zagaya dajin, yana matsowa inda sautin kukan jaririn ya fi yawa. Tsintsayen manya ne masu launin baƙi da shuɗi a jikinsu, ko kaɗan ba su yi kama da kalar tsintsayen da muke da su a gida da sauran yankinmu ba.

    Da ƙarfinsu suka fara zagaye inda kukan jaririn ya ke har suka yi nasarar katange shi da fuffukensu ruwan ya zamana yana sauƙa a jikinsu. Daga ƙarshe wani ƙaton tsuntsun da ya fi sauran girma ya tsugunna ya ɗauki jaririn da duhun wajen bai sa an ga fuskarsa ba.
Sauran tsintsayen suna mara masa baya, har suka shige cikin jejen sosai, cikin wata duhuwa da ta lulluɓe wajen, ba'a ganin komi a wajen banda duhu da kuma sauƙar ruwa a wajen.
Sai dai abin mamaki haka tsintsayen suke tafiya a wajen kamar yanda suke tafiya a rana.
   Wani waje ne mayalwaci da yake zagaye da sheƙar tsuntsaye da yawa, da kuma rufi a kanta ta ciyayi da wasu zarara abin wanda baya barin ruwa ya sauƙa a sheƙar ta su ya cikata. Shimfiɗar da ta fi ko wacce girma tsuntsun ya shimfiɗa jaririn da doguwar tafiyar da suka yi da shi ta sa shi barci.

Shima tsuntsun ya shige cikin shimfiɗar yana lulluɓai yaron da fiffikensa, wanda hakan ya sa jaririn sauƙe ajiyar zucita.

     *********
JEJIN TARSHUƘUL-MUT

Wani baƙin jeji ne mai ɗauke da na'u'ikan bishiyoyi kala-kala waɗanda suka yiwa jejin zagaye da duhun da rana bata ratsa shi sosai, baka ganin ɓulluwarta. Jeji ne da ya ke ɗauke da manyan aljannu marasa imani marasa tausayi da suke ta kaiwa da kawowa a cikinsa.
  Daga tsakiyarsa akwai wani ƙaton dutse da manyan aljannun da suka fi sauran muni suke zagaye da shi, hannayensu riƙe da muggan makamai, ko wani lokaci a shirye suke su farwa wani baƙon tsuntsun da zai gifta ta cikinsa, balle kuma aljannu jinsinsu.

   Wani ƙaton girgiza dutsen ya yi a lokacin da ya ke fidda wani sautin rugugi mai amo da ya cika dajin.
  Hakan yasa duk Aljannu da suke cikinsa risinawa suna duƙar da kawunansu ƙasa, kafin wani lokaci dutsen ya dare, wani mummunan halitta mafi muni a cikin aljannun ya bayyana ya fara takawa ƙasar wajen tana ƙara rugugi da fidda wani sauti mai amo.
   Har ya buga kafceciyar ƙafarsa a ƙasa hakan ya bada sauti mai ƙara da girgizar ƙasar wajen, inda ya buga kuma ya tsage wajen ya shiga rabewa.
    Hannunsa ya ɗaga yana nuna ƙasar wajen ya na surkullensa take kuma wajen ya koma ya haɗe, sannan ya fidda wani huci a bakinsa da ya haddasa fitowar feshin wuta.
    "Aiyukana da na shafe ƙarninka huɗu ina tafe da shi yau ya tarwatse. Alƙalamin taurarina ya sanar da ni damuwar tauraron da zai daƙusar da ƙarfin ikona.
   Ku shiga duniya ku bincike min wannan tauraron da haskensa ya disashe nawa, na rantse da Baƙin duhun zaluncina sai na daƙusar da haskensa a tare da ni. Sai na shafe iko da tasirinsa. Ku shiga duniya kada ku dawo min ba tare da amsar inda ya ke ba."
  Kamar walƙiya haka aljannun suka shiga ɓacewa da bin iska wasu kuma haskensu na gilmawa suna ɓacewa.
  Shima ƙaton aljanin ya ɓace bayan ya haɗa wata guguwa da sauti mai ƙara kamar zai tashi duniyar da fika-fikansa, bishiyoyin da suke jejin sai da suka yi rangaji da zubar da ganyayyakin da ke jikinsu.

BAƘAR DUHUWAWhere stories live. Discover now