FITA TA SHIDA

48 7 0
                                    


https://www.wattpad.com/story/273909650?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

BAƘAR DUHUWA ⚫

  ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

© OUM-NASS 🏇

FITA TA SHIDA

  Kallonsa ya ci gaba da yi yana nazartar jikinsa da kuma gumin da ya jiƙa shi sharkaf.

   "Yaushe ne muka yi haka da kai sarkin fada?"

Sarki Mu'az ya faɗa yana ƙara tsare sarkin fadan da idanuwansa.
  Jikinsa ne ya shiga rawa da karkarwa kamar mazari yana jin numfashinsa na sarƙewa, iskar wajen tana masa kaɗan ta yanda bata isa ga huhunsa.

  Kai sarki Mu'az ya girgiza a ransa yana jinjina al'amarin mutane, yana kuma jin nauyin abin da sarkin fadan ya masa duk da shekarunsa.

  Da kai ya yiwa dogarin alama a kan ya shigo da mutanen cikin fadar. Da sauri Dattijon da matarsa suka shigo suka gurfana.
   "Allah ya ƙarawa sarki lafiya da nisan kwana, Allah ya ƙarawa sarki adalci da tausayin talakawa."
   "Amin Dattijo. Mai ke tafe da ku Dattijo, ka faɗi maganar ka kai tsaye sarki na sauraronka." Zagi ya faɗa  da sauti mai amo.

   Kuka Dattijon ya ƙara fashewa da shi, matarsa na ƙara nata sautin kukan.
   "Kai tsoho ka faɗi maganarka kai tsaye, nan ba gidan mutuwa ba ne."
  Da hannu Sarki Mu'az ya yi masa alama akan ya yi shuru, sannan ya yi gyaran murya har a lokacin idanuwansa na kan Dattijan mutanen guda biyu.
   "Ina sauraronka Baba. Me ke faruwa da ku?" Ya yi maganar cikin sanyin muryar da ta zama jiki a gareshi.

      "Abin akwai girma da nauyi a matsayinmu na talakawan garinku mu shigo da irin wannan maganar. Duk da mun kasance a ƙarƙashin ikon kulawarku ne Rankash daɗe. Sai dai ba mu da zaɓi a matsayinmu na iyaye wanda ya wuce mu zo gareka da koken abin da ke faruwa a cikin unguwarmu ta talakawan Buhayyir.
  Rayuwarmu da ta bayin da suke hidima a gareku bata da banbanci, sai dai ma su bayin su fi mu jin daɗin cin mai kyau da kwanciya a waje mai kyau. A yayin da suke ƙarƙashin kariyar dogarai da kuma sanya idanuwanka.
  Sai dai mu....." Ya saki kuka mai sauti domin maganar ta maƙale a kan fatar bakinsa.

     "Mu rayuwarmu kamar bishiyar da   aka yanke samanta ne aka barta dungulumi ne Rankash daɗe. A ko wata rana fargaba da tsoro ke maye wajen kwanciyar hankalinmu. Bamu da murya mai amon da zamu yi magana ta isa gareka. Bamu da ƙarfin zuciyar da zamu ci gaba da fuskantar barazanar da kullum ake mana.
   Ƙarfinmu ya ƙare, juriyar yaranmu ta gaza Rankash daɗe."

   Shuru fadar ta yi har babu mai ƙwaƙƙwaran motsi a cikinta, kowa ya kasa kunne yana jin abin da dattijan mutanen ke faɗa.

   "Ku fidda mu a duhu bayin Allah. Mene ne yake faruwa a unguwar taku?" Shamaki ya faɗa

     "Ko wata rana wasu mahaya dokuna sukan shiga unguwarmu da tseren gudu, suna bi ta kan yaranmu da kuma kayan sana'armu. Idan muka ɗaga kai muka kallesu su dake mu su kuma yi mana barazana da mutuwa, suna mana iƙirari akan su na hannun daman Yarina Ubaidullah ne. Duk abin da suke da saninsa.
Yanzu haka yau ɗinnan sun bi ta kan yaranmu guda biyar da suke karatu a tsangayar malam Ja'i. Uku a cikinsu sun rasa ransu ya yin da biyu ba a san inda kansu ya ke ba.
  Wannan ba shine na farko ba, domin hatta yaranmu ƴan mata ba su ƙyaleba duk lokacin da suka gansu sukan yi musu magana ta rashin ɗa'a da kuma ja musu mayafinsu, wani lokacin sukan sa su a cikin gasar tseransu.
   A yanzu maganar da nake ma yaranmu a tsorace suke da rayuwa a cikin garin Buhayyir. Wadda har ta kai matakin da suka daina fita. Dan Allah rankash-daɗe ka tallafi rayuwarmu ka kawo mana sauyi da gyara a unguwarmu. Kai ne kaɗai bangon da ya rage wanda zamu jinga mu kuma yi kuka a share mana hawayenmu." Dattijon ya faɗa yana haɗe hannunsa waje ɗaya.

BAƘAR DUHUWAWhere stories live. Discover now