Farko.

2.4K 211 53
                                    

~~~~~

Wajen karfe goma sha biyu na rana, matar dake cikin kitchen ɗin da aka zagaye da langa-langa daga ɗan madaidaicin tsakar gidan ta kwance wani ɗaurin itace dake gefe ta ƙara a cikin murhun gabanta sannan ta shiga firfita wutar da wani karyayyen mafici dake gefe. Dattijuwa ce mai kyawun jikin da idan ba fuskarta ka kalla ba zaka zabge shekarunta ƙiyasi.

Kayan jikinta riga da zani ne masu kyau da har karin guga zaka hango a jiki, gashin kanta mai laushi ya sirka da kananun furfura da ta fara yiwa kan nata rumfa.

Sai da ta tabbatar wutar ta kama sannan ta mike ta fito, a tsakar gidan ta tarad da babbar ƴarta mai suna Amina zaune tana tsintar wake a wani katon farantin silver, shekaru ne kawai suka banbanta kamannin fuskokinsu amma kammaninsu daya sak! Har yanayin jikinsu da komai.

Ƴar siririya ce mai yalwar gashi irin na mahaifiyar tata, komai a fuskarta maidaidaci ne mai sanyin kwatance, idanunta ne kadai abinda mai ɗaukar hankali don duk da ba girma ne dasu ba, amma suna da wani kyalli kamar an ɗiga wani abu a cikinsu.

"Yi sauri ki gama Amina, sha biyu tayi gwara muyi sauri a ɗora don yanzu zaki ji su sun dawo."

Amina ta buɗa labule ɗakin dake bayanta, ta kalli agogon dake kafe a cikin dakin sannan tace.

"Ashe lokaci ya tafi har haka, ban kula ba sam wallahi."

"Garin ne ba zafi ai shi yasa kika kwanta kika yi ta baccinki."

Da murmushi tace.

"Ni ai na gaji da tashi da wurin ne wallahi, da sun tafi makaranta sai inga gwara kawai na kwanta."

Mahaifiyar tasu da suke kira da Amma ta dauki wata tukunya dake gefe, ta nufi wajen ruwa da ita tana fadin.

"Ki cigaba da addu'a kawai, idan da rabon ki a cigaba da karatun nan zaki yi insha Allah."

Amina bata ce komai ba, don Allah ya sani ta fara karaya, shekararta guda kenan da kammala karatun sakandire dinta, kuma sakamokonta yayi kyau duk da cewar an taimaka musu wajen yin jarabawar, amma duk da haka ta san tana da kokarinta daidai gwargwado, shi yasa ko kadan ƙulafucin son cigaba da karatun bai bar ranta ba.

Kuma ba dole sai wani babban karatu ba, don ta daɗe da soke Jami'a a lissafinta, ta sani cewa mahaifinta bashi da halin wannan wajen, yana iya bakin kokarin sa wajen kula dasu da ɗan abinda yake dashi kuma duk da haka kullum cikin damuwa yake yana ganin kamar baya basu abinda ya kamata, don yasha fadin cewa yayi burin cewar ƴaƴan sa zasu huta da duk wani gata na duniya.

Don haka tunanin ta a kullum na ta samu makaranta ne ƙarama inda zata dan koyi aikin lafiya... Don mahaifiyarta tasha faɗa mata cewa ko allura ta iya yiwa mutane, idan tayi aure hakan zai taimake ta sosai fiye da ace ta zauna bata yin komai.

Zancen auren ya tuno mata da saurayin ta Abdallah, ta san shirye-shiryen komawa makaranta yake yi shi yasa bata ji shi ba kwana biyu, a matakinsa na ƙarshe yake a can wata jami'ar Sakkwato. Abdallah mutum ne mai kirki da kuma hankali, har islamiyyar dare yake da ita a bayan layinsu wanda yasa kowa ke ganin mutuncinsa kamar yadda itama take girmama shi a kodayaushe, tana ganinsa kamar yayanta shima kuma yana taimakon ta a komai kamar ƙanwarsa.

Mu'amalarsu daban take da yadda take ganin tsakanin ƙawarta Fatima da nata saurayin, abubuwa da yawa idan Fatiman ta gaya mata ta kanyi mamakin yadda suke iya kasancewa, don ita ko ɗaga ido ta kalli Abdallah bata iyawa sosai, sau da yawa ma ta kan manta cewa mu'amalarsu aure zata kai.

"Salamu alaikum, wai a bada gullisuwa."

Sallamar wani yaro ta katse tunaninta sanda ya tsaya daga jikin hanyar soro yana miko naira hamsin.

Farar Wuta.Where stories live. Discover now