~~~~~
Let's go back to when we had not learn our names, when we introduced our souls, while our heart gasped for breaths. -Aliyu Jalal.
*
A cikin sabon gidan mutane sun fara raguwa sosai, ba kamar a ɗazu da koina yake a cike da mutane ba, Aunty Safiyya ta taho daga hanyar falo ta biyo wani ɗan dogon korido mai ɗauke da ɗakuna ta shigo ƙofar ɗakin dake gefe, a cikin ɗakin duk ƴan uwa ne na kurkusa sai kuma amaryar dake tsakiya kanta a sunkuye tana faman kukan da babu sauti sai hawaye kawai da take sharewa.
Aunty Safiyan da ta shigo tace.
"Na rasa yadda akayi aka manta da tsitsiyoyin nan wallahi, yanzu da ba sai a share gidan ba kafin mu tafi."
"Aunty ai na zata sharar dare babu kyau."
Ummi dake kokarin dora akwatuna can saman wardrobe din dakin tare dasu Momi ta fada tana juyowa.
"Wannan ai kamawa tayi..." Cewar Aunty Ma'u.
"Baki ga falon nan ba duk kasa ce wallahi, don bana ji akwai wanda ya shigo babu takalmi."
"Ni maigidan ma nake ji, haka zai shigo yaga waje duk ƙura?"
Ɗaya daga cikin matan Baban Kurna tace.
"Da za'a iya tunda akwai kofa ta baya sai a shiga gidan a tambayo su wallahi.
Mahaifiyarsu Ummi da itace zaune a gefen Amina rike da hannayenta ta girgiza kai tace.
"A hakura kawai, gobe da safe insha Allah sai su Maryam su zo su kawo mata kawai, su taya ta sharar ma."
Ta fada tana kallon Maryam din dake tsugunne a gaban Amina ta riko ɗaya hannunta.
"Ɗan kunnayen nan naki suna cikin wata ƴar ƙaramar jaka pink, ina jin a cikin wata Ghana must go aka saka."
Cewar Maryam din tana kallon idanun Aminan da duk yadda suka yi ja saboda kuka wannan kyallin na cikinsu na nan. Ta san ba zata amsa ba saboda haka ta cigaba da cewa.
"Hijaban sallarki ma suna cikin wannan karamin akwatin na undies, Amma ce tace in sa miki anan."
Sai ta gyada mata kai kawai tana ƙara share hawayenta lokacin da Aunty Safiyya ke tambayar su Ummi idan sun kwashe kayan cikin akwatunan kafin su dora su.
"Duk mun zuba su a cikin wadrobe ɗin, na kayan kwalliyar nan ne da kuma wannan Ghana must go ɗin zamu bari a ƙasa.
"Eh, ku barsu ta gyara ta kanta, sai ku zo mu tafi kuma don goma ta wuce."
Jin haka yasa Fatima ta taho daga wajen su Ummin tana ƙarasowa gaban Amina, lokacin da Maryam ke cewa.
"Idan zamu zo goben zamu zan taho da Hafsa insha Allah."
Fatiman ta sunkuyo tace.
"Amina litattafan nan naki ba'a ɗebo ba, sai dai daga baya ko Aminu ya kawo miki."
Sai a lokacin ta ɗago da idanunta ta kalle su, me yasa ne suke ta yi mata zancen kaya bayan ba abinda ke gabanta kenan ba? Mantawa suka yi cewa tafiya zasu yi su barta? Su barta a wannan wajen da bata san makamar abinda zata fuskanta ba, ko Abdallah ta aura ai dai sun san cewa wannan lokacin mai ciwo ne a wajenta, balle kuma mutumin da bata san ya yake ba balle takamaimai halinsa. Aunty Ma'u ta miƙe tsaye tana gyara mayafinta tace.
"Sai hakuri Amina, kin ji dai duk nasihar da akayi miki daga can gida, sannan su ma iyayen mijin naki kinga yadda suka karɓe ki, sunce ƴa suka karba ba suruka ba tunda dama duk ɗaya ne, kuma kowa ya san halinki Amina, duk wanda ya sanki yabonki yake yi... Mutanen nan sune basu sanki ba, kuma yanzu ne mafarin zamanku, dan Allah ki ɗorar da halinki a wajensu Amina... Don wannan gaɓar itace mafi alkhairin rayuwarki, ki sa su zasu zo suna bamu labarin kyautatawarki..."
YOU ARE READING
Farar Wuta.
RomanceA lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...! #AyshaShafi'ee #FikraWriters #FararWuta