~~~~~~~This could be the start of something new.
-High School Musical"Ina zamu je?"
Aminah ta tambaya lokacin da Ma'aruf yayi wata kwana data dauke su daga titin da ta kula cewa tun da suka shigo cikin garin Jifaywan a dazu shi suka yi ta miƙewa, muryarta a hankali ta fito yayin da take kallon hanyar.
"Wani waje." Amsar tasa ta fito a gajarce ba tare da ya kalle ta ba.
Sai ta juyo a hankali ga barin kallon titin da suke kai ta kalle shi ita, idanunta na shaida rashin fahimtar zancen, a can ciki kuma ruɗanin da take ciki, kamar ba zata ce komai ba amma sai muryarta ta sake fitowa.
"Nayi zaton gida zamu tafi."
Kalaman suka fito tare da nauyin yadda a yau bakinta ya furta wani waje daban da sunan Gida, saɓanin wajen da ta taso da rayuwarta a ciki. Ya girgiza kansa sannan ya juyo ya kalle ta, nauyin idanunsa suka sa taji kamar ta sunkuyar da kanta amma ta daure.
"Dare yayi kuna bana son tuƙin dare a babbar hanya, so anan garin zamu kwana sai gobe tukunna."
Yadda sautin muryarsa ya fito a cikin motar da kuma yadda yake kallonta yasa ta haɗiye wani abu a makogwaronta da bata san meye ba kafin ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan kuma ta sunkuyar dashi ƙasa ta shiga wasa da karshen mayafinta, tattaunawarsu da Amma bata kare ba sam zuwansa ne ya katse su, wanda ta san haka ne, da tun a can ta roƙe shi fa ya barta ta kwana tare dasu idan yazo da safen sai ya koma ya ɗauke ta, wani abun ya sake zarcewa makogwaronta tuna cewa a yanzu bata san ina zai kaita su kwana ba ma.
Amma duk da haka sai taji wani ɓangare a cikin zuciyarta na washewa, zuciyarta na rage nauyin da take ɗauke dashi a ɗazu mai cike da taraddadin rashin sanin abinda zata yarda dashi a al'amarin Hajiya Kilishi, ko ba komai yanzu ta san tana da babbar hanyar da take da yakinin zata samawa kanta mafita kamar yadda Amma ta fara gaya mata, Har a yanzu tana jin tasirin kalamanta da ya cika kanta taf! Yana ƙara buɗe wasu sababbin shafuka da a iya zagayen tunaninta gabaɗaya ita bata hango su ba.
Tana jin yadda amon kalaman nata ke zagaye cikin kanta, ma'anarsu na bi ta cikin jijiyoyinta suna taso da ƙarfin gwiwar da ta nemi ta rasa, kuma duk da taraddadin da take ji, koina a cikin kanta dama jikinta yana gaya mata cewar yanzu ne komai zai fara, don kamar yadda Amma ta fada ne babban kuskuren da Hajiya Kilishi tayi, ya riga ya bude musu ƙofar nasarar su.
"Mafitar ta riga tazo hannunki Amina, buɗe idonki kawai zaki yi ki kalle ta, kina da rabin maganin wannan matsalar yanzu a hannunki, wanda babban abun shine sanin halinta da kikayi, ita kanta bata sani bane amma tayi babban kuskure wajen bayyana miki sirrinta duk kuwa da na san cewa iya abinda take so ki sani kawai ta faɗa akwai sauran ƙurar da dole na san ta lulluɓe. Amma tun ana na fara raina lissafinta Amina, don da ace tayi bunƙasar da zan sara mata, da zata sami tarin hanyoyin da kema zata juya ki ba tare da kin san sirrinta ba..."
Wasu daga cikin kalaman Amman kenan da suka ƙara saka ta yarda cewa mahaifiyarta na cikin irin daidaikun matan da ake misali dasu a duniya, masu halayen da dimbin jama'a zasu gani tamkar a mafarki, da kowacce kalma da ta gaya mata a yau, zuciyarta ta ƙara yarda cewa mahaifiyarta itace babban makamin da zata iya tunkarar komai dashi a duniyar nan bayan addu'a.
Sai dai akwai wani abu guda daya a cikin kalaman nata dake fassara abinda zuciyarta bata taɓa lissafawa ba, abinda har yanzu da ta tuno yake rikita lissafinta yana sa hannayenta rawa, har yanzu bata gama sanin tunanin Ma'aruf game da ita ba, don haka ba zata taɓa iya ɗorar da komai ba a wannan fannin.
Ta rufe idanunta tsawon wasu sakanni kafin ta sake buɗe su tana ƙoƙarin saita kanta. Amma ta gaya mata cewa lokacin wani rauninta ya kare, kar ta yarda wani abu ya gaya mata cewa an fi ƙarfinta ba zata iya ba, tace mata itama macece, duk wani abu da take taƙama dashi itama tana dashi, kawai ita tana amfani da nata wayon ne ta mummunar hanya, don haka idan ita zata ɓullarwa gaskiya, a lokaci kadan ne zata kawo karshenta don gaskiya itace sama da komai a duniyar nan.
YOU ARE READING
Farar Wuta.
RomanceA lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...! #AyshaShafi'ee #FikraWriters #FararWuta