Uku.

1.5K 264 56
                                    

****

A wannan daren...

NO. 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.

A cikin ƙawataccen ɗakin, wata yarinya ta buɗe ƙofar ta shigo, ba zata fi shekaru uku da kaɗan ba, tana sanye da irin kayan yara kamarta, wani ɗan gajeran skirt kalar lemon greeen, (lemon tsami) sai farar rigar da itama akayi mata da ado da irin kalar, gashinta da ba wani yawa ne dashi haka zalika tsawo ba an tufke shi cikin kalba guda biyu da ribbon masu kalar kayan.

Ta karaso cikin ɗakin daya gauraye da sanyin A.cn da aka kai maƙurarta, akwai wani tebur irin na ado dake gaban hadadden gadon dakin, ta kansa ta taka ta isa kan gadon, ta hau tana bi ta kan ƙafafun wadda ke kwance har ta isa daidai fuskarta da ta rufe da bargon data lulliba gaba ɗaya.

"Mammy Mammy Mammy...."

Ta kira ta na bubbuga daidai kanta da ƴan hannayen nata, a lokaci guda mahaifiyar tata ta yaye bargon daga fuskarta ta buɗe idanunta da kyar tana kallonta.

"Menene Hameeda? Me ya kawo ki?"

Ta tambaya ranta a ɓace.

"Mammy I'm hungry. (Yunwa nake ji.)"

Taja tsaki a hankali.

"Ina Nannynki?"

Sai kawai ta miko mata takardar hannunta, kamar ba zata karba ba sai kuma ta yatsunta  biyu ta sakala ta cikinsu sannan ta buɗe ta.

'Ajiya I'm sorry Oo, dey don call me now say my mother dey hospital. I'll return tomorrow by God grace.'

Ta sake jan wani tsakin mai tsayi, bata san sau nawa take gayawa Mary cewar ta daina yi mata pidgin a gida ba, amma don rashin mutunci shine har rubuto mata take yi a takarda.

Ta juya ta sake kallon yarinyar data tsura mata idanu, dogwayen gashin idanunta sun kusa haɗewa da juna, yadda take lumshe su ya tuna mata da fuskarsa a lokaci guda.

...idanunka kake gani ko Ma'aruf? Irin naka ne sak!

Muryar Mami ta haska a cikin kanta ranar farko na zuwan Hameedan duniya, ta tuno fuskarsa, yadda ya kalmashe ta cikin hannunsa, lumsassun idanunsa na haskawa da tarin ƙaunar da kamar wani abu ba zai taɓa giftawa a cikinta ba.

Ruƙayya ta sake yin wani tsakin da ya riga ya shiga cikin dabi'arta kafin ta ture bargon gadon ta miƙe, wata lallausar doguwar rigar bacci ce a jikinta da idan ka kalle ta zaka ga kamar tana zamewa ne tsabar santsi da kuma kyallin da take yi.

Ta kalli agogo wajen karfe bakwai na dare.

"Baki ci abinci bane da rana?"

Ta tambaya tana daure gashin kanta da za'a kwana a yini ana musu da wani akan cewar nata ne, don human hair ne (gashin mutum) da aka dinka mata shi cikin nata ya saje tsaf!

"Mami tun da na sha tea, Mary bata bani komai ba. Waya take ta yi."

Gwarancin yarinyar mai daɗi ya fito tana kallonta. Wani tsakin ta sake ja kafin ta dauki wayarta sannan tace.

"Oya, taho muje to."

Da sauri yarinyar kuwa ta sauko tabi bayanta, suka fita daga ɗakin zuwa wani dogon korido daya hada fuskokin ɗakuna, suka isa wani rantsatstsen falon da komai na cikinsa kalar ruwan gwal ne da kuma makuba, a gefensa akwai matattakalar bene, suka sauka har kasa zuwani falon da yafi wannan girma, ta jikin dining area suka shiga wata kofar da take ta kitchen ce, wani katon kitchen da yake a gyare tas.

Babu ko tukunya guda daya akan gas don haka ta san babu wanda ya dawo a cikin kannen nata uku maza, suma can yawonsu waye ma zai gansu yanzu da magaribar nan? Dama Ashraf mai bi mata ne idan ya dawo daga aiki sau da yawa zai shigo ya dafa abincinsa tun bayan da suka rasa Josh (mai yi musu girki)  yanzu kuma yayi aure sati uku da suka wuce don haka babu mai shigowa kitchen din.

Farar Wuta.Where stories live. Discover now