~~~~~
Ana gobe sallah ne ranar, ita da Maryam sun je kasuwa siyayar mayafai da takalmi, tun kusan sha biyu suka fita har mutane suka fara alwalar sallar la'asar basu gama siyayyar ba.
Maryam dake riƙe da ledar kayan da suka siyo kalli tsinken kwakwar da suka auno tsawon kafar Hafsa dashi tace.
"Ai wallahi dama na san takalmin yarinyar nan shi zai bamu wuya, kafa kamar ba ta mutane ba ƴar firit da ita."
Amina ta share gumi a gefen fuskarta tace.
Har tunani nake ko ba daidai na auno ba wallahi gashi mun kusa gama siyen komai..."
Bata karasa ba ta tuno da sakon garin da Amma tace su siyo zata yi teba dashi da daddare.
"Kin san na manta da garin Amma... zo muje wancan layin na san zamu samu."
Maryam ta girgiza kanta.
"Mu raba tafiyar kawai lokaci ƙara wucewa yake, ga wani kantin takalma can, bari naje na duba idan ma ban samu ba zan jira ki sai kizo ki same ni anan."
Da haka suka raba tafiyar, Maryam ta tsallaka ta cikin cunkoson mutanen ta nufi kantin ita kuma tabi layin gefensu inda nan ɗin ma turuwar mutanen ce wadda dama sun riga sun shirya mata, don tun ana saura sati ɗaya sallar suka so zuwa kasuwar amma rashin haɗuwar kudin yasa dole sai yau suka samu suka fito.
Ga rana, ga azumi amma yadda mutane suka hargitse baza kace kowa a gajiye yake ba. Da kyar ta samu ta ɓulla layin da masu garin suke, kuma akan ragin naira hamsin ɗin da zasu yi kuɗin mota dashi, sai da ta kusan shanye layin tana tambaya da ƙyar ta samu wani acan ƙarshe yace zai rage mata.
Tana tsaye yana ƙoƙarin auna mata, wani yaron shagon nasa ya shigo, irin samarin nan ne masu magana, yana shigowa ya haye kan ɗaya daga kantocin shagon yana fadin.
"Allah na tuba a yadda ake wannan ranar ga azumi ai wallahi komai talauci na ba zanyi aikin sauke gari ba, don mugunta kaga yadda suke jefo musu buhun nan daga sama, wani har sai ya kai ƙasa wallahi kafin ya ɗago."
Maganar ta ɗauki hankalinta, tana hango yadda nauyin buhun gari yake ace mutum ya dauka a wannan ranar.
"Yau ma mota ta sauka ne?"
Mai shagon ya tambaya yana miko mata ledar garin.
"Gata can yanzu ta tsaya, ka san shi Auwalu ko da goma yaga sunyi ƙasa sai yayi aike."
Ta miƙa masa kuɗin tana faɗin ta gode, amma kafin ya karba saurayin yayi saurin miƙo hannu ya karba sannan ya miƙo mata yana mata murmushi, irin halin ƴan kasuwa.
A kofar shagon kuwa tana fita taga motar ana ta sauke garin, tausayin masu yin dakon ya tafi har cikin ranta ganin yadda ko a ido buhun ke da nauyi, tana tafe tana ganin fuskokinsu lokacin da idonta ya kai kan fuskar da ta sa ba shiri hannunta ya saki ledar garin nan... Mahaifinta ta gani dauke da wani katon buhu yana ƙoƙarin kaiwa inda sauran ke saukewa, mahaifinta dai Baba, Baban daya shirya tsaf a yau ya fita suna yi masa a dawo lafiya.
A wannan lokacin yana gaɓar farfaɗo wa daga karayar arzikinsa ne, don duk da kokarinsa wajen yi musu kayan sallah, har saida aka haɗa da kuɗin Aminu kafin komai ya isa, bata san lokacin da hawaye ya fara biyo kuncinta ba, taga ya sauke ya koma sake ɗauko wani... Baba mutum ne mai tsananin son dogaro da kansa kowa ya sani, yayyensa duka sunyi kokarinsu wajen tallafa musu tunda al'amarin ya faru, amma babu wanda ya isa ya ɗauke maka cin yau da gobe sai Allah, don haka ta san nauyin ya cigaba da tambayarsu ne yasa har ya kawo kansa yin wannan aikin don kula dasu.
YOU ARE READING
Farar Wuta.
RomanceA lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...! #AyshaShafi'ee #FikraWriters #FararWuta