~~~~~
Ɗimbin jama'ar dake yin tururuwa suna ƙara cika kowanne ɓangare na cikin masallacin su suka shaida auren mutum takwas ɗin da aka ɗaura kowanne kan sadaki mabanbanci, motoci kawai kake gani daga koina an ajiye su yayin da wasu ke ƙara shigowa suna daɗa adadinsu. Jama'a kuwa babu wanda ya san adadinsu sai ubangijin daya tara su gurin, dattijai da samari har ma da yara masu tasowa, gasu nan kala-kala kowanne ango da ƙungiyarsa da sai faman gaisawa ake ana ɗaukar hoto.
Daga can gefe, Kawu Ibrahim ya ƙaraso inda tasu tawagar ƴanuwan take, ya tsaya a kusa da Kawu Hamza yana girgiza kansa.
"Ka san yaron nan har yanzu bai iso ba."
"Ai ba zuwa zaiyi ba, gwara mu ma mu hanzarta mu bar wajen nan don ni jirgi na na ƙarfe uku ne ma, kuma akwai abubuwan da zanyi kafin nan."
Kawu Ibrahim ya juya ya hango su Kawu Mallam dake tsakiyar mutanen yana gaisawa da sauran ƴanuwansu fuskarsa cike da irin kalar tasa murnan, sai kawai ya juyo da kansa yace.
"Har yanzu na kasa gano dabararsu akan auren nan, babu wani abu dake nuna min cewa ba don saboda kudin mutanen nan komai ya faru ba."
"Koma meye dalilin nasu, a yanzu komai ya riga ya faru, kuma duk matsalar data faru daga yanzu kuma na tabbata shi ɗin yana da hannun ɗaukarta."
Kawu Ibrahim ya girgiza kansa.
"Muyi fatan alkhairi kawai, don har cikin zuciyata ina tausayin yarinyar nan, Amina tana da hankali wallahi."
"Hankalin da bai kamata ace an ƙuntata rayuwarta tun daga yanzu ba. Ai wallahi da nine da ikon Kawu mallam, auren nan ba zai taɓa faruwa ba."
Kafin Hamzan ya sake magana wayarsa tayi kara don haka ya dauka yayi gefe yana ƙoƙarin amsawa. Kuma sai a lokacin idanun Ibrahim suka iya hango masa Baba (mahaifin Amina) yana daga tsakiyar mutanensa sai faman gaisawa yake dasu fuskarsa ɗauke da ɗimbin fara'ar da ya kasa auna nauyinta dana kuɗin sadakin auren dake cikin aljihunsa, dubu ɗari cif!
A cikin ƙwaƙwalwar sa lissafi yake cewar ko da kudin zasu iya ninka adadinsu sau goma baya jin zai taɓa iya bada ƴarsa aure ga mutumin da akace yana da matsalar ƙwaƙwalwa, tunda gashi tun a yanzu sun fara gani, in ba haka ba wane ango ne yake ƙin halartar wajen ɗaurin aurensa?
***
Motar ta shigo kamfanin da saurin da ya saka maigadin da ya buɗe gate ɗin juyowa yana kallonta, kuma duk saurin nata sai da ta isa ga layin da ake ajiyar motoci ta tsaya sannan ƙofar mazaunin direba ta buɗe.
Ishaq ya fito sanye da wasu kaya kalar sararin sama, wayoyinsa rike a hannu ya rufe ƙofar sannan ya tunkari cikin ginin dake kallo shi, wani gini mai hawa uku da yasha adon gilasai tun daga samansa har ƙasa. Security ɗin daya bude masa ƙofa har sunkuyawa yayi bayan ya gane shi yana fadin.
"Yallaɓai sannu da zuwa."
Kuma maimakon ya amsa sai kawai ya tambaye shi.
"Ma'aruf yana ciki ko?"
"Eh tabbas, ai tun safe ya iso yallabai"
Jin haka yasa Ishaq ɗin yin gaba zuwa hanyar matattakalar da zata kaishi sama, wata receiptionist (mai karbar baki) a wajen mai suna Rafi'at ta shiga gaishe shi tana murmushin da ke manne cikin tsarin ayyukanta, kuma da mamakin yadda akayi bata manta fuskarsa ba duk da karancin zuwansa wajen ya ɗaga mata hannu yana zarcewa zuwa saman.
A hawa na farko can ƙarashe ofishin Ma'aruf ɗin yake, don yana tuna lokacin da yake gaya masa cewa ya canja office, ya isa ƙofar daidai lokacin da sakatariyar Ma'aruf ɗin mai suna Martha ke fitowa riƙe da wasu files a hannunsa.
YOU ARE READING
Farar Wuta.
RomanceA lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...! #AyshaShafi'ee #FikraWriters #FararWuta