~~~~~~
I fall in love with your kindness, because it adds peace to my wounded but striving soul.
- Unknown.
***
Ruƙayya na tsaye daga jikin windon, hannunta rike da kofin wani shayi dake tiriri, idanunta na manne akan shukokin harabar gidan nasu dake waje, kamar nazarinsu take tana son gano wani abu a jikinsu, amma a zahiri kalaman aminiyar mahaifiyarta da ake kira da Hajiyar Sudan wadda ke magana a baya ne suka shiga kunnenta.
" ... Da mun tura wanda za'a samu ya kwance abin nan ke kin sani Nafi, yadda na ake da tabbacin na kabari baya dawowa haka aiki na yake ci..."
Sai kawai ta juyo a hankali tana kallon Hajiyar Sudan ɗin kafin kai tsaye ta katse ta.
"Ban gane ba, ta yaya zamu iya kai abin har cikin gidan?"
"Yanzu duk bayanin da muke yi baki ji komai ba? Tunanin me kike yi bayan wannan?"
Cewar Mahaifiyarta Hajiya Nafisa, amma ga Hajiyar Sudan ɗin wani shu'umin murmushi tayi tana kallonta sannan tace.
"Ƙyale ta Nafi, yanzu zata fahimce ni tsaf."
Ta fada ba tare da ta ɗauke idonta daga kan Rukayyan da itama ke kallonta ba, kuma da hannunta na hagu ta yi mata inkiya da alamun ta ƙaraso ta zauna a gefenta.
Rukayya ta kalli wajen, ta sake kallon fuskarta... Allah ya sani bata son matar sam, don ta daɗe tana zargin itace ta bawa mahaifiyarta shawarar data fito da ita daga gidan Ma'aruf, sai a yanzu da suka ga da gaske babu yadda zasu yi da ita akansa sannan suka hakura, ko kuma tace mahaifiyarta ta hakura don har yanzu bata gama yarda da ita Hajiyar Sudan ɗin ba sam, amma sanin cewar bata da wata hanyar da ta wuce tata yasa ta cije lebbenta kawai sannan ta ƙarasa ta zauna ba tare da kallonta ba.
Kuma kai tsaye sai ta fara bayani daga inda ta san zata fahimta.
"Yanzu mun aika masa da takardar sammaci, ba nufinmu a shiga shari'a ba kamar yadda nayi miki bayani, a iya gaban alkali za'a sulhunta komai a tsakaninku kin san duk abinda zaki faɗa da kuma shaidun da muka samu wanda zasu saka komai ya tagi daidai, don haka daga nan za'a baki ƴarki ki taho gida da ita.
Kwana ɗaya kawai a tsakani, zaki haɗa kayanta wanda a ciki zamu san yadda za'a dinke ƙullin nan a cikin jakar yadda babu wanda zai tiya gani, sai ki kirashi wani waje inda zaku haɗu ki kalallame shi da zancen wannan yarjejeniyar taku, ki karbi kuskurenki da komai ki kuma bashi yarinyar da cewar kin yarda ta koma hannunsa kamar yadda kuka shar'anta, ki gaya masa cewa bayan wani lokaci ya dinga kawo miki ita kina ganinta.
Da wannan zamu barta a wajenta tsawon sati guda inda a sannan ne za'a sami wadda zata je gidan da sunan ta kawo sauran kayanta, a wannan lokacin za'a sami dabarar da zata kwance ƙullin nan, wanda da anyi hakan Ruƙayya, shikenan sai ki cigaba da kurbar shayinki kina kallon abinda zai biyo baya."
Ta ƙarashe zancen da wani faffaɗan murmushin da ya sassauta zuciyar Rukayyan a lokacin, don sosai yasa ta jin cewar kamar da gaske sunyi nasarar sun gama, tayi niyyar magana amma sai mahaifiyarta ta riga ta.
"Idan komai ya tafi daidai, sai ke kuma ki bar hakarƙarin mu ya huta haka kije can ki ƙarata."
"Ai babu abinda zai kuskure ma, na gaya miki idan kinga an samu saɓani a wannan abin Nafi, to gawar da aka binne zata fito ta dawo duniya, don haka ku kwantar da hankalinku kawai."
Wannan zancen yasa su yin dariya dukkaninsu kafin hankalin Ruƙayya ta juya ga wayarta da ta shiga ƙara daga can inda ta baro ta a jikin windon data tsaya.
YOU ARE READING
Farar Wuta.
RomanceA lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...! #AyshaShafi'ee #FikraWriters #FararWuta