Sha Uku.

1.3K 200 136
                                    

~~~~~~~

There's a part of me that likes to beleive everything will be okay, then there's another that breaks down every chance it gets.
- Unknown.

**

Dukkan wata ma'ana ta mamaki da kuma tashin hankali shine yadda fuskar Amina tayi a lokacin da take kallon Hajiya Kilishi.

"Taɓa Aminu dana sa akayi tsaraba ce ga ƙwaƙwalwar ki Amina don ki saurare dukkan abunda zan gaya miki da kyau, ki yarda da dukkan kalamaina sannan kuma zuciyarki ta tabbatar da cewar Kilishin da zaki sani a yanzu da gaske take al'amuranta."

Tayi shiru bayan ta faɗi hakan hannunta na jawo wayarta da ta ajiye a gefe, babu ƙarar kiran dake shigowa alamun a silent ta saka ta.

"Ya akayi Awwalu?"

Muryar tata da ta canja tar ta tambaya cikin wayar bayan ta kara ta a kunnenta... Har a lokacin Amina bata motsa daga yadda take zaune ba, idanunta basu canja daga yadda suke kallonta ba, sannan ƙwaƙwalwar ta bata wartsake daga mamakin dake zagaye da ita ba, Ƙirjinta dake ɗagawa cikin numfashi mai nauyi shine kaɗai abinda zai sa ka san cewa idan ka taɓa ta ba zata tafi ta faɗi ba.

Wataƙila magana guda ɗaya aka fada a cikin wsyar wadda ta gamsar da Hajiya Kilishin, don bata ƙara cewa komai ba ta kashe ta kawai ta sake mayar da ita gefenta, sannan ta sake kallom Aminan, hasken fuskarta na yayewa alokaci guda

"Duk abinda zaki ji a yanzu ya zama tsakani dake ne Amina, idan ba haka ba a ƙarshen zancena zaki gane abinda zai faru idan har kika sako mutum na ukun mu a wannan zancen koda kuwa mahaifiyarki ce.

Da farko mu bar duk wani kewaye-kewaye mu tafi ga abinda yasa kika shigo gidan nan, tunda ni dake dama duk wani mai hankali mun san akwai dalilin aurenki da Ma'aruf..."

Ta gyara zamanta kaɗan sannan ta cigaba...

"... Cire mahaifinki ki ajiye shi a gefe, amma ko mahaifiyarki ta san ruwa baya tsami banza, a muryarta kawai na fahimci cewa irin zurfin tunaninta kika ɗauko Amina, ku duka kun san ba kowacce mace ce zata taka irin matsayin da kika taka a banza ba, zan ƙara tabbatar miki cewa shigowar ki cikin gidan nan dama cikin rayuwar Ma'aruf wani abu ne da ba don taimakona ba, ba zaki taɓa samunsa ba ko zaki mutu sau ɗari ki dawo, saboda a rana guda zamu iya samun mata dubu da zasu yarda da auren Ma'aruf ko da kuwa ciwon da yake dashi yafi haka tasiri, don ba'a  wayewar kowacce rana mata ke samun namiji irinsa ba.

Kuma shi kansa Amina, da an bashi zaɓi na sani tsaf zai kawo macen da zata fi ki a komai don irinsu kawai ya sani kuma yake mu'amala dasu, amma sai nayi amfani da ƙarfina da kuma ikona nace ke kaɗai za'a bawa wannan matsayin wanda dole kowa ya yarda da hakan, don haka duk wata soyayya da kika ga kina samu daga mutanen gidan nan dama shi Ma'aruf ɗin da ya fara saurarar ki duka saboda ni suke miki ba don komai ba, ni na ɗora su akan turbar zuciyarsu ta so ki kuma hakan ya zame musu kar dole."

A yanzu Amina tayi ƙoƙarin sunkuyar da kanta tana kallon hannayenta dake faman rawa suna kakkarwa akan cinyarta, zuciyarta na bugawa ne kamar zata faso kirjinta ta fito yayin da kowanne kalaman Hajiya Kilishin ke shiga kunnenta da tsantsar rudani da kuma tashin hankalin da akace ba'a saka masa rana.

Kuma shirun da Hajiya kilishin tayi baiyi tsawon da zata iya fitar da komai ba lokacin da muryarta ta cigaba da cewa.

"Bari in ɗauko miki komai tun daga farko Amina, ta haka ne zaki fahimci zance na.

Lokacin da ina yarinya a wajen kakata na girma, ita ta raine ni tun daga lokacin yaye har girma na, a wajenta na samu tarbiyya da kuma tarin wayo da dabaru irin na zaman duniya, har yasa tun a ƙananun shekaru ina iya kallon rayuwar mutum na bashi shawara mai kyau da zata ɓulle ga matsalolin sa, hakan yasa ƙawayena dama mutanen unguwar a lokacin suka laƙaba min sunan ƴar baiwa.

Farar Wuta.Where stories live. Discover now