Sanarwa.

1.3K 136 57
                                    

~~~~~~

Assalamu alaikum.

Fatan alkhairi ga tarin Masoyan FARAR WUTA da ma duk wani littafi da ya kasance nawa. A lokaci irin wannan nakan nemi kalamai in rasa, nagode da dukkan support ɗin ku tun daga shafin farko na farar wuta zuwa in da na tsaya.

Ina kuma ganin tarin saƙonni da ƙorafin ku akan rashin samun update akan lokaci, ina jin kalmar HAKURI kamar tayi kaɗan, amman ita kaɗai nake da ita. Na fara littafin nan ne ba tare da na hango tarin uzururrukan da suka dinga taso mun ba, suka kuma zama dalilin rashin samun update ɗin da ba kwayi.

A yanzu mun kawo karshe littafi na ɗaya, kuma gashi wani abu ya taso mun da zai sa rubutun dakatawa na dan wani lokaci.

Na sani...
Na kuma fahimta tun kafin ku furta.

Kuyi HAƘURI, zai dawo ba da daɗewa ba, amman saboda dalilai da yawa littafi na biyu zai koma Paid Story cikin tsarin da nake fatan dukan mu zamu ji daɗin shi. Idan baku same shi gabaki daya a lokaci ɗaya ba, In sha Allah zai dinga zuwa akan lokaci.

Wanda na ɓatawa a farkon tafiyar nan zuwa yanzun, banda kalamai masu yawa sai neman afuwa da kuma bada hakuri.

Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kuma bamu aron lokacin sake haduwa dan karasa tafiyar FARAR WUTA.

Kar ku manta yanzu tafiyar ta fara...

Zan baku labarin yadda nasara ke samuwa babu boka ba Malam!

Zan baku labarin soyayyar Ma'aruf da wataƙila zata narkar da zuciyarku kamar ruwa.

Zan kuma baku labarin yadda mata ke samawa kansu mafita ta hanyar wayo da dabarar da Allah ubangiji ya halitta a ƙwaƙwalwar kowacce mace.

Nagode muku fiye da yadda baki zai iya furtawa.

#AyshaShafi'ee
#fikrawriters
#FararWuta.

Farar Wuta.Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon