~~~~~"Kiyi hakuri Amina, amma sun shaida min cewa yaron yana da matsalar taɓin hankali!"
A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata walƙiya har da tsawa a cikin ɗakin! Kuma bayan walƙiyar ta ɗauke a idanun Amina, Baba ya cigaba da maganarsa.
"Wannan maganar ita ta sanya a safiyar yau dana shaidawa Kawu mallam dukkan abinda ya faru ya tara meeting din da ya sanya yinin mu a gidan, don har su Kawu Ibrahim da Kawu Hamza sun zo a yau..."
Ba shiri tasirin sunayen ya sanya Amina ta sake ɗago da idanunta ta kalli mahaifin nata, yayyen Baba hudu ne kuma shine ƙaraminsu, Daga Kawu mallam sai Kawu Abubakar da suke kira da 'Baban kurna' sai kuma Kawu Ibrahim da Kawu Hamzan da dukkansu biyun suke zaune a garin Abuja tare da iyalansu, don haka bata san adadin mamakin da zata iya kiyastawa ba na cewar saboda maganarta Kawu mallam ya taso su a yau tun daga can suka zo, ganin yadda Babn ke kallonta yana son fassara yanayinta yasa ta maida idanunta ƙasa a hankali yayin da hannunta na dama ya kamo karshen skirt dinta da ƙarfi.
"Amina a jiya babu irin boren da mahaifiyarki bata yi min ba akan maganar nan, dukkan ku shaida ne cewa Halima mace ce mai biyayya gare ni, don tun daga ƙuruciyarku har yanzu babu ranar da ɗayanku zai ce kunji kanmu ni da ita game da wani al'amari a gidan nan, duk abinda na fada ko nayi daidai ne a wajenta, amma a karo na farko jiya mahaifiyarki ta bijire min akan wannan hukuncin, tace bata yarda ba, tace ba ni kadai na haife ki ba itama tana da nata haƙƙin akanki don haka ba zan siyar dake ga wasu mutane ba kamar yadda ta fassara al'amarin.
Kuma bayan zuwan su Kawu Ibrahim a yau sai suma duk suka goyi bayanta, da ni da Kawu mallam da Baban kurna Amina mune kadai muka hango wannan al'amarin ta fuskar alkhairi da kuma cigaban ki wanda su basa gani. Don haka na san a shekarunki da kuma hankalin yabzu zaki iya banbance daidai da akasinta, don haka muka yanke cewar matsayar tana gare ki yanzu, duk ɓangaren da kika zaɓa shi zai fi rinjaye kuma maganar ta zauna kenan har abada, kar ki ga cewar na amsa musu acan, ki faɗi ra'ayinki Amina babu wanda zai taɓa ganin laifinki don rayuwar ki ce, mu duk ƴan kallo ne kawai.
Don haka kije kiyi tunani daga yau zuwa gobe, saboda idan har ɓangaren mahaifiyarki kika ɗauka, ina so ne muje mu sami mutanen tare da su Kawu Ibrahim kafin su koma kuma kafin wani abu ma daga ɓangarensu yayi nisa. Kije kiyi tunani Amina."
Shikenan! Shikenan sai duk bayanin ya ƙare da wannan jimlar, lokaci kuma ya fara bugawa da adadin awannin da zasu tadda goben, goben da Baba ta furta kamar tsawonta na shekara guda ne.
Taji lokacin da ya miƙe ya zo ya wuce ta, taji shi ya zura takalmansa daga waje sannan taji ƙarar takunsa na nufar hanyar soro, sai kawai ta rufe idanunta gabaɗaya tana hadiye wani abu da bata sanshi ba a maƙogwaron ta.
"Duk abinda mahaifinki ya fada haka ne ya faru Amina, kuma ba komai yasa nayi hakan ba sai don nemar miki ƴancinki..."
Da wani sassanyan amo muryar Amma ta maye gurbin ta Baban tun kafin ta bude idanunta
"... Ƴancinki nake nemar miki Amina, don ni na hango abinda mahaifinki ya kasa ganowa, mutanen nan masu kudi ne da gaske, kuma duk tsananin kirkin mai kuɗi a zaune yake cewar baya taba son mu'amalar rayuwarsa da talaka kamar mu, zasu taimaka, zasu yi zumunci kamar yadda ita wannan Hajiya Kilishin ke yi amma aure Amina, aure babban abu ne da shine linzamin rayuwarka ta duniya har zuwa lahira, don haka kowa ya sani cewa hakan ba ƙaramin abu bane ga rayuwar mutum da zai haɗa shi da kowa.
Da ke muka je auren wani ɗansu a shekarun baya da suka wuce, kinga matar daya aura ai, kinga irin tarin dukiyar ubanta da danginsu, don ba a banza bahaushe ke cewa 'ƙwarya tabu ƙwarya ba... Kowa daidai dashi yake nema. Saboda haka Amina ko makaho yaji wannan zancen ya sani cewa mu ba daidai da mutanen nan muke ba, sun nemi aurenki ne kawai don son zuciyarsu..."
YOU ARE READING
Farar Wuta.
RomanceA lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...! #AyshaShafi'ee #FikraWriters #FararWuta