*A RASHIN SANI🎀*...
*Story & writing*
*Hafsat Musa*
(Indon kauye)*TYPING📲*.....
*1 OCTOBER 2021*
*Page 1&2*
Sad'af Sad'af take tafiya domin batason aji takun tafiyar ta, kusa fita ne ta tsinkayi muryar ta bisa kanta Zainab! tsayawa tayi cak domin wadda take gujewa karta ganta ta ganta, "Ina kike shirin tafiya ne kike tafiya tamkar b'arauniya ne?"..
"Mammy gun Jabeer zani yana waje ne tundazu yana jirana." tab'e baki tare da yanayin fuskar ta ya canza "Zainab wai sai yaushe zaki fita sha'anin Jabeer ne?" Mammy don Allah me jabeer yayi miki ne kika tsane shi nidai inason jabeer kiyi hakuri Mammy jabeer mutumin kirki ne fa"..daga hakan ta juya ta fita, wadda ta kira mammy ne tabita da kallo har ta fice samun kujera tayi ta zauna tare da tagumi tana tunanin wasu shekaru can baya da suka shud'e mata,wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata.. Hango ta yayi kura mata ido yayi tare da datse wayar da yake har ta k'araso gunshi bai daina kallon ta ba "Jabeer!"..
Firgice yadawo daga tunanin da yatafi "My zeey har kinfito?" Tunanin mekake inata jera sallama bakaji ba"...tunaninki nike Zee na." Murmushi tayi tare da gewaya ta bud'e murfin mota ta shiga suka cigaba da firar su irin ta masoya kallon Jabeer tayi "jabeer kamar naga kana cikin damuwa ? Kafadamin please...Baby meyasa Mammynki bata son tarayyar mu ne? Jingina kanta ta tayi jikin kujera "My jabeer nima bansani ba bansan Abinda yasa Mammy ke batason tarayyya ta dakai ba, "My zeee ina sonki sosai". Karka damu Jabeer komai zai wuce zan ma Daddy na magana.." Murmushi yayi mata tare kashe ta da wani kallon so inda taji wata kaunar shi takara yawa a zuciyar ta ji zata iya jure komai tare da rasa komai indai har akan jabeer baza tab'a rabuwa dashi ba sun d'auki wani lokaci suna firar irin ta masoya har dare yafara musu sannan sukayi bankawana ta nufi cikin kamar yadda tayi d'azu haka tayi shiga sadaf sadaf turus tayi gani mammy ta zaune cikin palour fuskar ga hawaye "Mammy!" Cikin fushi ta taso ta nufo ta tas! ta d'auke ta da mari da furta sunan ta da karfi "Zainab!.."...Turkushi bamu fara komai ba meke jawon hakan ne?....
#Sannuku mutane na ina muku fatan Alkhairi Allah yabani ikon fad'ar abin da zai amfani ku shirmen ciki ayi watsi dashi
# Ranakun post ba kullum watakila sai bayan kwana d'aya
# Rashin comment zai tashi daga Free ya koma na kudi
YOU ARE READING
A RASHIN SANI..
Mystery / ThrillerA rashin sani da jin rashin maganar iyayenta ta zabeshi A matsayin masoyin gaskiya, A rashin sani sanadiyar shi tayi rayuwa A gidan mahaukata a matsayin mahaukaciya mai tabin hankali, A rashin wadda ta fifita ashe dan fashi ne..