*A RASHIN SANI*
*Story &,writing*
_Hafsaat Musa_
(Indon kauye)*Dedicated, Mom Zulaihat Lagos gabaki d'aya littafin A RASHIN SANI, sadaukarwar ne gareki Nagode sosai da kyautar ki gareni baki baya iya faduwar godiya ta gareki Momma❤️😍💃🏻🙏🏻*
*3&4*
Zainab! Kin fifita saurayi akaina kin fifita soyayaya akaina kin fifita farin cikin ki akan nawa farin ciki duk duniya babu wadda zai soki tamkar yadda ni mahaifiyar ki nake son karki aikata abu A RASHIN SANI...Zainab daga baya kizo kina dana sani karki aikata Abinda na aikata gashi haryanzu tabon shi yaki gogewa A raina kullum na tuno hakan sai nayi kukan nadama namiji bashi da tabbas wasun su basu san hallaci ba" fuskar ta shab'e shab'e da hawaye hannun ta dafe da kuncin ta ta dubi mahaifiyar ta "Mammy me wai jabeer yayi miki ne kika tsane shi ne Mammy kifadamin jabeer mutumin kirki ne kikasa b'oye tsanar shi har tafi ya shaida kin tsane shi yace min meyayi miki kika tsane shi ina kaunar jabeer," dakata zainab inhar kin nace sai jabeer ki tattara kayanki ki koma gun mahaifinki a yau.".. daga hakan Mammy ta koma tazauna batare da ta qara kallon zainab ba, zainab cikin kuka ta mike ta nufi d'akin ta wadrope d'in ta tafara zuba kayanta cikin trolley har tagaji key d'in motar dake mirror ta d'auka tafito ta ja akwatin ta ko inda Mammy take bata kalla ba ta fito Mammy mikewa tayi ta nufi d'akin ta, zainab tana zuwa ta bud'e bayan mota tasaka A trolley d'in sannan ta shiga mota mumber d'in jabeer ta kira "muhad'u bakin hanya yanzu".. Meke faruwa zee?" Ba doguwar magana bace ka iskeni titin... Gayamishi titin dazai iske ta tayi ta datse wayar...tare yima motar key ta buga maigadi horn dasauri ya bud'e mata ta fita Mammy na kallon ta window d'in d'akin ta har ta fita daga gidan,Mammy komawa tayi ta zauna tare da jawo wayar ta komai ta tuna ta maida ta aje tare dafe kanta da hannu biyu...
Kallon shi tayi karka damu Jabeer zuwanan da kwana 2 Daddy na yanason duk Abinda nakeso itama Mammy na zata huce kwana 2 shiyasa zan tafi gun Daddy d'in, ga ATM d'ina nan ga kuma pin d'inan na rubuta maka inkana da matsala zaka iya zuwa kafidda karka damu my jabeer zamu zama ma'aurata lokaci kad'an...cikin yanayin damuwa ya kalle ta tamkar zaiyi kuka "shikenan my zee i love you so much baby.." Me too My baby..." Badon sun suba sukayi bankwana da juna cike da kewar juna da kaunar juna,jabeer bin motar Zainab yayi da kallo har ta shud'e murmushi yayi tare zaro wayar sa "Jatau kuna ina ne?"...hayy oga J munan gidan sama"... Kaida horo ne inason ku aikata min wani aiki yanzu yanzu kufito kubi hanyar titin...zakuga wata mota dark ash kwatata musu motar yayi da number d'in mota d'in, mace a ciki Ina bukatar gawar ta.......
YOU ARE READING
A RASHIN SANI..
Mystery / ThrillerA rashin sani da jin rashin maganar iyayenta ta zabeshi A matsayin masoyin gaskiya, A rashin sani sanadiyar shi tayi rayuwa A gidan mahaukata a matsayin mahaukaciya mai tabin hankali, A rashin wadda ta fifita ashe dan fashi ne..