*A RASHIN SANI*...
*Page 17*
Tunda suka fara tafiya Babu Abinda Mammy tace ma Daddy kallon Gefen titi take Fuskar ta tana sharar Hawaye..can sun d'anyi Nisa Mammy batare da ta kalli Daddy ba "inhar kasan matar ka tanan kada ka kaini gidan ka kabarni nasamu muhallina nazauna"..bata kai da tarewa ba ne"...Mammy bakarabin ta kanshi ba har suka iso garin Kano inda tuni bacci ya d'auke Zainab saida Daddy ya tayar da ita inda dama tuni Mammy ta shigewar ta...
Bayan kwana 7
*Takun saka*Tsawon kwana bakwai d'i nan babu Abinda ya hada Mammy da Daddy duk Abinda Mata take ma Miji Mammy tana ma Daddy kan ta ne haryanzu bai gano ba Mama tare da Y'ayyen Daddy da Amaryar da Mama ta had'a Auren su da mahaifiyar ta sunzo har gida sunci ma Mammy mutunchi inda ashe Amaryar Daddy Mansura ita tabada sanarwar daurin Auren A katsina don Mammy ta gani takuma tura mata text messages, Ko Inda suke Mammy bata kalla ba inda taja hannun zainab suka shige d'aki tabar su har suka gama Abinda suke sukayi tafiyar su sunji haushin rashin kulasu da Mammy batayi ba suyi mata karewar cin mutunchi...
------
Turowar kyaure yaji d'agowa yayi domin har yafidda rai da zata amsa kiran shi daya roke ta yana son magana da ita samun waje tayi ta zauna can gefe "Maryam don..." dakatar dashi kafadi Abinda zaka fada shine kawai dama kataba jin wadda ba'a cuta ba anbashi hakuri in har bakada Abin fadi wallahi zan tashi nabar maka d'akin ka kada ka sake bani hakuri ni".. Ajiyar zuciya yayi "nan da kwana 3 zamu koma Abuja shine nace kifara shirye shirye " dariya yaga Mammy tayi wadda tunkafin asamu matsalar nan "Abuja fa da ni kuma ai kawai inkana son kwanciyar hankali kaje kaja Amaryar ka kutafi Amma ni Maryam bazan taba zuwa Abuja ba Khalil karka dauka saboda kaunar ka nadawo gidanka Biyayar Baffah ce kawai tasani nadawo gidanka Amma da tuni na guntule igiyar Auren nan dake tare dani zan fada maka wani Abu wadda inhar baka aikata hakan ba zan dauki Zainab muyi nesa da kowa da kowa babu wadda zai sake jin duriyar mu har abada wallahi ko kuma ni nayi nesa da kowa...So nake kayi nesa dani ko kuma ka rubuta takadar saki na ka kyaleni nayi rayuwa ta ni daya don Allah Amma inhar ka nace dole sai ka zauna dani bani bukatar ka kusadani kwata kwata banason ganin ka banason jin muryar ka ko kadan Inhar da yuyuwar haduwar mu ni zan fada maka inda zamu hadu bawai kashigo nan gidan ba da sunan mijina ina kallon ka wallahi kafadama Baffah ga Abinda ke faruwa wallahi sai nayi nesa da kowa wadda sai sake jin labarina ina fatan ka fahimta da duk Abinda na fada kadaina tunanin Maryam A matsayin mata tana zaune dakai yanzu A matsayin Biyayyar Mahaifin tawannnan shine Tushen Komai inda Mammy ta kafa ma Daddy sharudda akan ya nesa ta kanshi da ita kwata kwata tunda yaki sawwake mata Auren shi wadda biyyaya ce tasa take zaune dashi Anya kuwa Mammy...Inda ya d'auki Mansura suka tafi Abuja badon yanason hakan ba Inda sukuma suka dinga murna da farin ciki da hakan suna murna wai asiri da Mammy tayi mishi ya kare shikam ya bi umurnin Maryam ne don yasa ancuceta komin kuma jimawa zata safko daga dokin Fushin data hau yasan maryam d'in shi da kafiya akan Abinda ta kafe akan shi bazata sauko don yanzu ba shiyasa zai lallabata zai kuma da cigaba da Adduar har ranan da zata safko... Wannan kenan.. A haka Daddy yakoma Abuja Inda Mammy tasamu aiki A wani gidan televison dake kano tana aikin ta ba ruwan ta dasu mama ko shiga harkar su rayuwar ta take kawai Mama kuwa farin ciki kamar me taraba Daddy da mammy inda kuma suke jefar ta da kalamai wai karuwanci take inda duk magagunun suna dawo mata batada lokacin su ne shiyasa bata damu da lamarin su ba, Zainab kuwa tasamu Admission a B.U.K. tana karantar Law..
*Bayan wani lokaci..*
A haka rayuwa take ta tafiya Mammy tana rayuwar ta da diyar ta kadai kuma duk magaganun dasu Mama keyi tana jinsu su ta share akan ta neman Maza.... Zainab ta kamallah karatun ta cikin kwanciyar hankali ba matsalar komai damuwar ta d'aya rabuwar kan iyayen ta kawai wadda ta rasa wace matsala ce ta rabasu haka da sukayi Nesa da juna inda kuma Mammy tayi mata wani gargadi akan kar taji komai gun Baffah inko taji zata hadu da mummuna bacin ran ta wadda bata taba gani ba, Masu gari zainab tana kamallah karatu tasamu aiki A babbar court A matsayin lawyer gwammanati inda ake kuma matukar ji da ita saboda tsananin gwazon ta da basirar ta da jajircewa akan aiki ta kowa yasan Barrister Zainab wajen kwatar ma duk wani marar yanci yanci ta kowane b'angare... Had'uwar zainab da Jabeer kuwa sun hadu ne a wajen bikin wata Friend d'in ta inda shi kuma yana cikin Abokan Ango inda yana ce ma Zainab Amma taki kulashi kwata kwata a wajen tarasa inda yasamu number yafara bibiyar ta tun bata kulashi ganin messaege din sa da call din sa yasa tafara dan kulashi daga hakan har sukayi sabo mai tsanani da shakuwa har yafara zuwa gidan su Mammy ganin ta daya da Jabeer taji kwata kwata bai kwanta mata ba baiyi mata ba tarasa dalili hakan kodan tana d'auke da tabon namiji wadda bazai taba gogewa ba har abada.. ta nuna ma Zainab bata ra'ayin jabeer Amma ta toshe kunnen ta akan Jabeer mutumin kirki ne,
zainab kullum cikin yima jabeer hidima take tunda yafada mata shi maraya bata damu da talauchin sa inda yafada mata yana aikin wani company a matsayin karamin ma'aikaci inda tace kar yadamu komai zai wuce kuma zata iya zama dashi a kowane yanayi....inda shikuma Jabeer zuciyar sa ba haka Son Manufa yake ma Zainab....Dawowa Labari....
wayyo chajina yakare😂
muna dawowa Labarin yanzu zamuji wane Hali zee take ciki ne A wane yanayi zata farko ko kuma ta sheka ne muyi zaman makoki.. su mammy wane irin labari zai riske su ne..muje zuwa fa✍🏻
inki ganin ruwan comments inyi zamana Abuna Allah🤣
YOU ARE READING
A RASHIN SANI..
Mystery / ThrillerA rashin sani da jin rashin maganar iyayenta ta zabeshi A matsayin masoyin gaskiya, A rashin sani sanadiyar shi tayi rayuwa A gidan mahaukata a matsayin mahaukaciya mai tabin hankali, A rashin wadda ta fifita ashe dan fashi ne..