13

3 1 0
                                    

*A RASHIN SANI*...

*Page 13*

Mairo ta zubar da jini inda kuma har zuwa lokacin bata haihu ba, Malam yashiga tashin hankali domin yana matukar son mairo haihuwar ce bayaso yanzu..  cikin ikon Allah nakudar ta taso mata baki d'aya ta haifi kyakyawar d'iyar Mace  wadda har ta zarta ta kyawu..Allurar Bacci akayi mata domin ganin yadda tasha wahala  inda kuma cikin sa'a basai ankara mata wani jinin ba   aka gyara jaririya tana rike Hannun Mama  tana ta tarairaiyarta Amma Malam ko kallon inda Jaririyar yake baiyi  ba Mama ta d'auka Alkunya ce,kwanan su biyu asibiti Aka sallamesu har zuwa lokacin Malam bai d'auki jaririya ba Mairo tana lura dashi sai datayi kukan ta ta share lokacin waya bata yawaita ba Mama tacema malam yaje ya sanar da iyayen ta tun haihuwar nada kwana d'aya  Amma yace akwai wata hidimar dayake sai da akayi kwana 2 sannan  yaje inda suka tafo da wata gwagwon Mairo wadda zata dinga kula da ita..Mairo saidai tayi kukan ta goge tabbas tasan Alhakin Baffah ne ke d'ibar ta abisa kin bin umurnin sa tabi son zuciyar ta gakuma inda ya kaita..anyi hidimar Suna wadda kusan rabin hidimar Mairo tayi batare da kowa yasani ba  daga ita sai Inno d'in ta ko Baffah bai sani ba ranar suna Malam yarada ma Jaririya Zainabu Abu..Anyi hidima ankare lafiya bayan wani lokaci zainab tafara girma masha Allah kyawun ta yana kara fitowa da kamannin ta da mahaifiyar ta da mahaifin ta inda ciwon dataji bai kirguwa data rarrafo ta taho gun malam zai ture ta tafadi kasa ta fashe baki haka Mairo zatazo ta d'auke ta ta wanke mata ita kuka Zainab kuka, gobe bazai hana ta dawo gun Mahaifin ta shikuma bazai fasa ture ta tafadi ba har taji ciwo  ba har takai data fara tsoron shi matukar gaske data ganshi zatayi saurin tafiya jikin mahaifiyar ta ta lab'e tare da ririketa inda ko da Mama bata yarda inda Mama tace Mairo ce ke koyamata tsanar ta, Kullum da daddare sai malam yaba Mairo wasu pills tasha wadda ita kanta batasan ko namenene ba inta tambeyeshi sai yace tasan bazai bata abinda zai cutar da ita ba nakarin lapiyar ta ne, shekaru suna ta tafiya Babu Abinda ke had'a zainab da mahaifin ta sai matukar tsoron shi datake Ana hakan gwammanti ta d'auki nauyin d'aukar wasu malamai na makaranta gwammanti zuwa Kasar England karo karatu inda har da malam cikin inda yasamu aikin koyarwa a wata secondry school, inda kuma inhar kanada mata da yara dasu zaka tafi har karatun su gwammanti ta d'au nauyi, ahakan malam suka d'aga kasar England da mairo da Zainab... inda ya maida Mairo wata universty anan England  tana karantar Mass. Com, inda ita kuma Zainab aka sakata primary duk da malam yadaina hantarar ta yanzu kokarin jawota jikin sa yaje Amma taki sakewa dashi kwata kwata saida mahaifiyar ta,...Basu dade da zuwa  England bamalam ya d'auki Mairo suka nufi wata asibiti wadda ita kanta mairo batasan Abinda zasuyi ba  tunda aka kwantar da ita bisa wani gado bata kara sanin Abinda ke faruwa sai bayan kwana 3  tafarka inda ta tambaye malam Abinda yafaru da ita yace bata lafiya ne an dubata ne, batakara bin ta maganar ba kuma, rayuwar farin ciki ta tadawo musu baki d'aya tare da kaunar junan su,

Bayan wasu shekaru...

Maryam Ahmed Ruma tazama Hamshakiyar yar boko  gata hamshakiyar yar gayu tazama kasaisaitaciyar mace...   inda take aikin gidan wani televison anan England inda shikuma Malam yazama professor inda England ta rike sa yana musu aiki na wasu shekaru kafin ya koma nigerian Inda zainab ta koma budurwa tana ajin karshe a secondry school  kyawunta yafito sosai gata doguwa   tana da d'an jiki ga manya ido Masha Allah zainab tana da kyau sosai,tananjn hausa da turanchi inda tafima yin turanchi tunda shi Daddyn ta yake mata Mammyn ta keyi mata hausa inda tace bazata yaren ta akan wata boko,  inda take da fara'a  kowa nata ne  taji d'an nigeria sai tayi kawance dakai saboda Mammyn ta da Daddyn ta suna fada mata asalin su nan da wani lokaci kadan zasu koma gida,

Mammy ce zaune tsakiyar Palour ta jefar da mayafin ta da gyalen ta  hatta kallabin ta tacire  kuka take Kukan ta Daddy yaji yafito "Maryam lafiya?" dasauri ta mike "kada ka matso kusadani Khaleel wallahi natsaneka  kamatso sai na kasheka Macuci azzalumi.."... Kamar dirar mikiya Daddy yaji wannan kalamai Bakin ta tamtama yake Anya Mairon sa ce...

# Not Edited

mai bukatar Group din A rashin sani yayimin magana nasaka shi danagama labarin su mummy zandaina post dinsa ko ina sai group din dana bude nagode A cigaba da hakuri🥰🙏🏻

A RASHIN SANI.. Where stories live. Discover now