26

28 2 0
                                    

*A RASHIN SANI*..

       *26*

Firgice ta tashi daga baccin datake "Zainab! "
Kallon ta yayi tare datashi daga dardurman  sallah ya nufo ta "lafiya Maryamu meke faruwa ne?" "Abban Zainab wallahi mafarki  zainab nayi tadawo garemu har tana rungume mu tana kuka farin ciki gidanmu ya cika da mutane ana tayamu farin ciki"... Kuka tasa mai tsuma zuciya matsowa yayi daf da ita tare da rungumo ta jikin sa yana shafar bayan ta, kiyi hakuri kinji Inhar Zainab tana raye zata dawo garemu kinji tashi Muyi Sallah".. har toilet ya rakata ta d'auro Alwallah sukazo suna nafila suna miqa ma Allah kukan su har akayi sallar asuba sannan,

    *Bayan kwana 2*

Har zuwa wannan lokacin Zainab bata farfado daga doguwar sumar da tayi ba ma'aikata na kanta Amma shiru daka kalli Dr Ahmed kasan bashi cikin hayyacin sa da natsuwar sa tamkar wadda ya Dade  yana ciwo ne ga rama sai siririn hancin sa kawai, Shigowar shi kenan D'akin da zainab take ciki wajen gadon ya tsaya  yana kallon ta " Mommy Allah yabaki lafiya ya saka miki akan abunda wannan mugun yayi miki indai Ina rayuwa sai na daukar miki Fansa Akan abunda yayi miki"...tsananin b'acin rai ne ya bayyana A fuskar sa inda ya jawo kujera ya zauna daf da gadon take   kwance tare da dora hannun sa bisafuskar sa yana kallon kamar gizo yaga tana mishi inda yaga yatsun ta yana motsi dasauri ya qara baza idon sa, gani yayi hannun ta yana motsawa dasauri ya  miqe ya nufo gadon datake kwance numfashin ta yanata Kai kawo dasauri ya fiddo wayar sa wata number ya Kira bada jimawa ba wasu likitoci  su 2 suka shigo D'akin gadon da Zainab ke kwance suka nufa oxgen din  dake tare da ita suka cire... "Zata iya farkawa kodayaushe numfashin ta ya dawo ya daidai ta sai muga yanayin yadda zata farka din...kamar daga Sama sukaji tafara  magana... "Mammy! Mammy!! ..ki taimakeni ki yafemin don Allah... Mammy!!!! ".. inda da karfi ta furta hakan tare da bud'e idon ta  bin d'akin tayi da kallon ganin mutane tayi tsaye kanta  kallon hannun ta tayi gani drip tare da ita ga wasu mutane wadda ba San su ba... Dr Ahmed cikin tsananin Murna ya nufi gunta  "Mommy Sannu kinji kin farka meke miki Ciwo yanzu?".. zainab binsa tayi da kallon ganin yadda yake mata magana tamkar ya santa har ma da Kiran ta  da wani suna Mommy ita dai bata sanshi ba amma kuwa tanaji tamkar ta taba rayuwa dashi ne".. Muryar yaji kamar daga Sama, "Waye Kai? Don Allah Ina ne Nike Nan meke Faruwa dani Ina Mammy na take ku Kiramin Mammy na  Abba na nagansu...Dr  Labaran kallon Dr Ahmed yayi "Congrats Dr Ahmed ga duk Alamu Mommyn taka tadawo hayaccin ta wadda muke tsammani kodayaushe zata iya dawowa..".. Dr Ahmed cikin tsananin farin ciki ya kalli Labaran Tabbas Kuwa Dr ga duk Alamu Amma zamu tabbatar da hakan...kallon Zainab yayi ''kiyi hakuri kinji Baki lafiya ne ki Kara samun sauki kinji ko..." Toh Ina Mammy na da Abba na..".  Sunje su dawo ne." Dr Ahmed kallon Dr Labaran yayi da Dr Uzairu muje office Akwai maganar da zamuyi.'..A hakan suka bar Zainab take ta kallon kofa taga inda su Mammyn ta zasu fito, ta qagara ta ga Mammyn ta tayafe mata ketare maganar ta datayi ta fito daga gida ga abunda yasameta accident din datayi da rabo ta mutu...Yan fashi na bin ta A bayan ta ko ya akayi ta tsare ta daga garesu itadai tasan ta kaima wani Abu karo lokacin datake tserata daga garesu,....

_*After 3 days*_

Antabbatar da dawowar Zainab cikin hankalin ta  bayan gwaje gwajen da akayi mata a brain din ta batada wani problem yanzu  kwata kwata Dr Ahmed yayi matukar murna da Godiya ga Allah yayi kyauta ga mabukata har ummi ta lura da farin ciki dayake ta tambayesa  ya fada mata tabe baki tayi kawai tare fadar bashi da mata  sai surayya,....

##

Share hawayen Fuskar take wadda yaki tsayuwa tunda Dr Ahmed yagama bata labarin komai da komai, miqo mata handkicif dinsa yayi "Share hawayen ki."..
Batayi musu ba ta karba tana sharewa  taba jikin ta ta dinga Yi  cikin kuka, "yanzu ni zainab nayi hauka nayi rayuwa a mahaukaciya... tabbas Babu mai sanin ranan da kaddara zata riski ruhin sa  bai iya gudu ko Kuma ya hanata Faruwa a garesa  Kaddarar tawa kenan runtse idon ta tayi tabbas lokacin da Dr tanko ke kokarin raba ta da mutunchi ta taji kamar wani shock cikin kwakwalarwarta  kamar a mafarki  tadinga aika ta komai,  " Nagode Dr  Ahmed Allah yasaka da khairan Nasan duk inda Mommy take sunacan cikin tsananin tashin hankali kwashe tsawon wannan lokacin batare da sun San inda Nike ba a yau inason na bayyana gasu Mammy na, murmushi Dr Ahmed yayi  .." karki damu a yau zan kaiki ga Mammy kinji Mika mata wata leda yayi kishuga kiyi wanka ki canza kayan Nan mutafi kafin Rana tayi.. dasauri Zainab ta karba tare da sunkuyar da kanta wani kwarjinin bawan Allah nan takeji yau kwana 3 din Nan  ''na... ". Shi!!!! Dr Ahmed yayi mata da hannu banason jin komai daga gareki zanje cikin asibiti nadawo kafin ki shirya..daga hakan ya fita... toilet zainab ta shiga domin saka kaya cike da zumudin ganin Mammyn ta......

Not Edited...

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 04, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

A RASHIN SANI.. Where stories live. Discover now