14

11 1 0
                                    

*A RASHIN SANI*...

*Page 14*

"Maryam meke damunki me faruwa ne dake ne nine fa Anya kece?"
nice Khaleel ka kashe ni  ka kashemin rayuwa ka cuceni bazan taba yafiya a gareka ba kuma sai sawwake min bazan zauna dakai ba da kasa anciremin mahaifa a jikina bani ba haihuwa har abada  Khaleel Meyasa ka aikata hakan A gareni Khalil  jifa tafarayi da kayan dake cikin palour har tasamu Daddy a goshi dakyar batare da ta ankara ba  yajawota  jikin ta Ya matse "Haba Maryam kinatsu mana kinsan bamu kadai bane a gidanan inda zainab ta dawo ta iske ke ki cikin wannan yanayin fa" "ka kyaleni  Khaleel ka sakeni kagama da rayuwata ka kuma cuceni ka sakeni bazan kara zaman aure dakai ba" fashewa tayi da wani irin kuka  mai cin rai, "Kiyi hakuri Maryam kiyafeman inbaki yafeman bansan yadda zanyi ba tun haihuwar zainab naga yadda kika sha wahala kuma lokacin banason haihuwa rayuwata zanga duk takura ne shine da mukazo nan England nasamu wani Doctor mukayi magana akan acire miki mahaifar baki d'aya tunda ga zainab mun samu ta ishemu, nakai ki asibitin kikayi kwana 3 tun lokacin, nima yanzu Maryam Allah yajarrabeceni da son yara nasan ubangiji ne ya kamani a lokacin da na nuna bani da ra'ayin haihuwa zanyi fito na fito da ubangiji kiyi hakuri maryam bazan iya sakin ki ba nidake mutuwa ka raba inhar nayi miki hakan Allah bazai taba bari na ba nayi mugun Butulci"... Mammy kallon Daddy kawai tayi tare da fizge hannun ta tabar gun tashige d'aki tasa key babu irin yadda Daddy baiyi ba akan  tabud'e taki bud'ewa d'akin sa  ya nufa ya dafe kai yana matukar jin Muguwar Nadama takamashi inda shima yakejin yana son yara inda ubangiji ne ya kamashi kuka ya dinga rizgawa tamkar lokacin da yarasa mahaifin sa tashi yayi ya kwashe Abubuwan shaidat dazata maida Mammy nigeria domin tunda ta ambaci  tafiyar sai tayi ta ya b'oye su inda bazatayi tunanin su ba,Rayuwar gidan Profesor ta canza baki d'aya Mammy babu wadda ta tsana ta gani tamkar Daddy Zainab ta shiga damuwa ganin yadda rayuwar gidan su ta canza wadda bata taba ganin hakan ba tun tashin ta bata taba ganin sab'ani tsakanin Mammyn ta da daddy sai kauna kullum data gani sabuwa wajen su da kulawa da juna.. A hakan rayuwa ta cigaba da tafiya har komawar su Nigeria yayi babu wani shiri tsakanin Mammy da daddy ba yabo ba fallasa  Mammy tabi duk hanyar da zatabi ta tafo nigeria kafin lokacin Amma bata samu dama daga kasar ba, har sai lokacin da kasar ta d'ibar musu komawa,Daddy ya shiga matukar damuwa sosai ganin yadda Mammy ta sauya mishi tamkar ba ita inda itama tausayin Mijin ta ya kamata Amma inda ta tuna Abinda ya aikata A gareta sai taji tamkar tazuba mishi poison ya mutu,  "Maryam gani durkushe gabanki ina neman afuwar ki akan abinda yafaru yariga yafaru tunda ka zainab Allah yabamu zata haifu zamu hada wata zuriar mai yawa  Kinji maryam... " zan yafe maka Amma da sharad'i  d'aya"..  cikin Farin ciki Daddy ya kalli Mammy jin ta sakko.. Fadi komai nene zan miki Maryam.. "Khaleel ka cuceni rabani da  kayi Amma bayadda zanyi bazan iya maido ta ba tunda aikin gama yariga yagama hakan kuma yana daga cikin bin umurnin Mahaifina danakiyi..ka tabbata bazaka karo  Aure ba domin kada Matar ka tayimin gori wata rana  akan hakan duk wuya duk rintsi saboda nasan babu namijin dazai kuma marmarin aurena A hakan banda wani Amfani tunda nida haihuwa har abada.."
Maryam dake kad'ai zanyi rayuwa har abada babu wata daga ke sai yar mu zainab Allah ya rayamana ya kuma yafemana Kuskuren mu bare ni dana aikata babban Kuskure zan kuma ta neman tuba gareshi" ...daganan Farin ciki yadawo zainab tadawo ta iske hakan   inda itama tayi farin ciki ganin Parents dinta sundawo tamkar da
Dawowa nigeria....Silar rikecewar Komai... Daddy yagama aikin dayakema England Inda yau jirgi ya sauke su A Airport.. Mammy da Daddy suka shaki kamshi qasar su inda suka d'au wasu shekarun basu cikin ta zainab kuwa waige waige ta dinga yi, Mota ce tazo ta d'auke su suka nufi gidan su Daddy wadda tuni Agyarashi Fes! tamkar bashi ba   an sauke su inda Aunty Uwani da Aunty Saratu (Sisters din Daddy) suka dinga kallon Mammy yadda takoma wata hamshakiya kasaitaciyat mace ga wani irin kwarjini da tayi ga mutane sai zainab dasuke tabi da kallo tamkar d'iyar turawa sun lura ma tamkar batajin hausa taki sakin jiki da kowa ma sai Mammyn ta da Daddyn ta...  Mama sai bin Mammy take da wani irin kallo    tana tab'e baki,

"Kai salamane Mijin Hajiya ko Mijin tace  Matar ka tafini ko duk maganar danake fada maka bakajin ta tabi ta bayan kunnen ka ta wuce  zan gani in nina haife ka ko kai haifeni wallahi  sai kayi aure  inaso inga yalwar jikoki tunda matar ka tayi d'aya haryanzu shiru inta ga wadda tayi karatun boko an asirce ka.. kaje kaga Mansura yar gidan yalwati mun tsaida magana ita zaka aura kuma a cikin wannan satin tunda Allah ya hore maka komai tashi kabani waje nida jikata an koyamata kiyayata uwar ta ta koyamata rashin so na duk wani asiri zai kare"... Mama kada ambaci komai kuma ka tsallake umurni na wallahi sai nad'aga maka Nono...

Turkashi...
ina Alqwarin da Daddy yayima Mammy gashi mahaifiyar shi tace inhar ya ketare umurnin ta zata d'aga mishi Nono? meye silar Batawar Mammy da Daddy har suka kyale juna tsawon wasu shekaru kuma suna da Auren juna?...  Ya labarin zainab wane hali take ciki ne ya suka hadu da Jabeer? jabeer ya ci bulus kenan? zainab zata cigaba da rayuwa kuwa.. tarin Amsoshin nan duk suna tare da yar mutanen katsinawa😂  

mai bukatar ji zai iya nemana ta wannan number din 09038667286 zakuce kodai na kudi ne taw Albishirin ku kyauta ne fa 😂 zandai daina post a ko ina sai group din dana bude domin  novel din Nabarku lafiya anatare masoya😍

yanzu zamu fara💃🏼

A RASHIN SANI.. Where stories live. Discover now