12

2 1 0
                                    

*A RASHIN SANI*...

*Page 12*

"Maryamu nayafemaki Amma kada ki manta da sharadin danayi miki"  kitashi kuje Allah yabaku zaman lafiya da Mijinki"..kuka tafashe dashi takasa tashi inda sai da wata gwagon ta tazo ta d'auke ta haka b'angaren  innar ta sukayi bankwana inda aka nufi da Mairo Birnin kano... kwanan su daya aka juyo akabar mairo d'akin ta tare da uwar mijin ta  wadda Malam yaja katanga ya fidda Part d'in sa d'aki d'aya ne sai kitchen.. lullube take bisa gado sai kuka take tunda aka tafi akabar ta take kundudene cikin mayafi   shigowar shi taji hakan baisa ta d'ago Fuskar ta  zama yayi bakin gadon tare da aje ledar da ya shigo da ita "Maryam".. shiru babu Alamun zata amsa mishi qara matsawa yayi daf da ita tare da jawo ta jikin sa "Maryam menene kike ta kuka sai kinja ma kanki wani ciwo ne na dabam haba maryam nadauka dana shigo da wannan kyakyawar Fuskar taki zan gani sai na iske kina kuka" rungomota yayi jikin sa tare da cire mata mayafin jikin ta yafara rarrashin ta har tayi shiru, ya lallabata sukayi sallah.. "kitaso  muje wajen  Mama muyi ta sai da safe".. Mairo lullubin ta tagyara  suka nufi Part d'in Mama mahaifiyar  sa inda suka gaida ta takuma yimusu nasiha akan zaman aure da rayuwar Aure...

      Bayan wani lokaci..

rayuwar aure mai cike da farin cikin da kaunar juna ke guda tsakanin   Malam da mairo inda tuni ya maida ta  makaranta tagama da primary wato secondry school.. inda shima yakoma makaranta had'a degree na 2  rayuwa nata Mairo tafara rashin lafiya sukaje asibiti inda aka tabbatar da cewa mairo tana shigar ciki Malam baiyi farin ciki  kwata kwata da samun cikin ba domin bai tsara haihuwa yanzu ba inda ya lallaba Mairo akan a zubar da cikin ba yanzu zasu haihu ba tunda duk karatu suke ba yanzu ba sai sungama karatu sannan insuka fara aje yara yanzu   zasu rusa wasu tsarin rayuwar su...Mairo kin amincewa tayi da hakan akan abar mata cikin ta tanaso gashi shikuma malam bayaso daga wannan lokacin rayuwar ma'aurata tafara canzawa Malam ya d'auke ma mairo kwata kwata babu ruwan shi da ita wata rana sai cikin dare yake dawowa tayi bacci ma wurin surukar ta Mamah take samu kulawa tunda ta lura mairo tana da shigar ciki take nan nan da ita da tattalin ta..   Mairo ta shiga matsanancin kuncin rayuwa da damuwa akan d'aukewar da malam yayi mata tamkar bashi ba abu kad'an zatayi mishi ya daka mata tsawa Abincin ta ya daina ci  gashi ba kowa zata fadamawa ga kuma sharadin da Baffah ya fada mata saidai ta zauna d'aki ta sha kukan ta kwatsam wata rana tafara wan irin ciwon mara sai zubar da jini bata san lokacin da aka kaita asibiti ba tafarka ta shafi cikin ta babu inda aka sanar da ita tayi B'arin cikin  tashiga damuwa akan b'arin cikin ta datayi bayan an sallameta sundawo gida Daganan kuma Malam ya dawo ya lallabi mairon sa suka dawo tamkar da  soyayyar su..andade mairo bata samu ciki ba har mamah tafara magana akan shirun samun cikin mairo sai ga kuma ciki ya bayyana wannan karon Malam baisha wahalar shawo kan Mairo ba yabata wani magani cikin ya b'are...malam d'an Akidar boko ne sosai komai nashi A tsare yake yin sa inda yake fadama mairo tabari sai ta kamallah karatun ta  shima ya samu aiki sai tasamu ciki su haifi yara 2 zuwa 3 sun ishe su...  A hakan duk lokacin da zai kusanci ta yake bata magani suna rayuwar su cikin jindadi da kaunar juna.. A hakan Mama tafara canza ma mairo kan taki haihuwa  inda dama tunfarko  yan uwa malam basu shiri da mairo wai ta mallake musu qane suka dinga fada ma mama karya da gaskiya tun bata yarda har tafara yarda.. suka taso Mairo gaba... shekaru sunata tafiya har mairo ta kamallah secondry school d'in ta inda tafara kaguwa itama tanason ta haihu amma shiru shikam malam ko a jikin sa karatu yake yake daya kammalla wani ya dasa wannan bai damu da mairo taki haihuwa ba yafi bukatar hakan, kwatsam saiga wani cikin ya bayyana inda mairo tace wallahi bazata zubar da cikin ta ba yana kallo yadda mahaifiyar shi da danginsa yadda suka tsane ta  har suna maganar yakara Auren.. fada sukayi sosai da sosai inda duk ta danne amma da ka ganta kaga tana cikin damuwa bayannuwar ciki yasa mama ta d'an sakko inda take fada ma mairo "sai yanzu kika daina shan maganin yanzu kika shirya haihuwar ne a haka ta daure  ta tai rainon cikin ta inda malam babu Abinda yake tofawa akan cikin ko ganin ta baya son yi tayi kukan ta in tayi niyyar tafiyar ta Kauye sai ta tuno sharadin Baffah duk da tana zuwa amma bata taba nuna mishi tana da matsalar gidan Miji ba...  A hakan ta cigaba da rainon cikin ta har ya tsufa Malam yace bashi da abinda zai siya  baida kudi irin hakan yake gudu  dama takura ma rayuwa da tsohon cikin ta ta shirya ta tafi rumaaa inda yan gida suka dinga yima Mairo dariya da Allah ya kara maganin ta kenan ta dage sai d'an binni ai kowa ya ganta yaga  tana cikin damuwa ko bata furta ba A hakan suka shiga d'aki itada da innon ta tana kuka take cemata haihuwar ta yazo gashi kuma malam bashi da kudi (ta boye bata fada ma inno ba gudu kada inno ta tsani malam..mata ku koyi rike sirrin gidan Auren ki  bawai ke da miji yayi miki abu ba  kizo kifada zaku shirya da mijinki Amma kuma iyayenki na kallon mijin da Abinda yayi miki sunajin haushin sa)  "Mairo kin tabbata Abinda ke faruwa kenan dubi yadda kika rame fa tamkar mai ciwo ki fadamin danuwar ki ni mahaifiyar ki ce baki da wata sama dani"  "Inno  Abinda nafada miki kenan"  Inno girgiza kai kawai tayi  batare da ta amince da hakan ba... Allah sarki Uwa Uwa mai dadi Mahaifiya sanyi idaniya  uwa farin cikin rayuwa duk wadda ya rasa mahaifiya dole yayi kuka domin kuwa wani babba rashi ne yayi rayuwar sa Allah kajikan wadda suka rasu yagafarta musu.. mukuma da namu ke raye yakara musu lafiya da nisan kwana yabamu ikon gamawa dasu lafiya... inno saida  tumakin ta  tayi  tahada da wasu kud'in ta  taba mairo akan tayi siyayyar kayan haihuwa batare da kowa ya sani ba... kwanan mairo 2 ta dawo ta shiga kasuwa ta siyo duk abinda zata bukata kudin suka isheta har ta rage inda malam ko kallon inda take bayayi,dare daya nakuda ta kama mairo inda dama ta kwana 2 tanayin ta tsaitsaiye inda tafara zubar da jini sosai tamkar famfo ta fita hayyacin ta inda aka rungud'a sai asibiti... harda malam domin ya tsorata da yanayin dayaga mairo inda yasha wani Alwashi cikin ranshi shi kad'ai...


naso na ida labarin nan a wannan page d'in Allah bai nufa ba karku manta haryanzu muna cikin labarin Asalin Zainab ne..

A Rashin fans daga wannan page d'in bazan kara post ba kudinga samu  wani gun sai  anjiman ku🖖🏻duk inda ba amin comments nagama post...🚶🏻‍♀️

A RASHIN SANI.. Where stories live. Discover now