25

7 2 0
                                    

*A RASHI SANI...*

     *25*

"Mommy"! daka mata tsawa yayi  nan da nan ta rikice ta rasa Inda Zata nufa shar! Yaga hawaye na bin kuncin ta  Riko Hannun ta yayi kawai yayi ya fita yabar office din Dr Tanko ko kuwa binsu da kallo yayi har suka fita "shege Dr Ahmed dama akwai irin wannan dankwaleliyar mai kama da larabawa ban taba ganin ta ba ya killace ta tashi ce shi daya yake nufi sai ya zauna yana tayima Mutane wa'azi ashe shima yana wadda yake hutawa  aikam dole nayi taste,  Dr Ahmed babu inda ya nufa da Zainab sai Room din su  "Mama Meyasa kike barin ta tana fitowa ne ita d'aya ne?".."wallahi yallabai bansan fitar ta nan suke wasa  da diyalle".. to don Allah Mama nasan kina Kokari don Allah A dinga kula da ita sosai," Insha Allah yallabai."

     *BAYAN WANI LOKACI...*

Jabeer kuwa yayi bincike sa yagano Mahaifan Zainab basu san tana gidan Mahaukata ba A tunanin kowa ta mutu a hadarin Mota inda hankalin sa ya kwanta yana ta bushashar shi yadda yaso,

Mammy kuwa ta d'an kwantar da hankalin ta sanadiyar rubutun da kuma safkar da Baffah keta mata amma ita a ranta fa Zainab bata mutu ba tanan da ranta kuma komin daren dadewq zata dawo gareta Daddy yana matukar tausayin ta inda intayi wani abun tamkar tasamu tab'uwa a tare da ita,

Zainab tana rayuwarta Dr Ahmed Ummin sa tasako shi gaba Akan Maganar Auren  sa da surry Amma haryanzu  taki samun goyon bayan sa in yaga ran ta ya b'aci yake cewa tayi hakuri akwai abinda yake shiryawa ne,...

    WANI DARE...

Asibitin tayi shiru tamkar babu kowa  duk sunyi bacci Ankashe fitulu sai duhu dif!...  A hankali ya lallabo  gadon da take kwance A hankali ya tada ta miqewa tayi kawai tabi bayan shi cikin farin ciki ganin yadda yasamu nasarar ta cikin sauqi  "Yaya yana ina?" Muje na gwada miki"..wani daki ya nufa da ita sai matsanacin duhu  "Shiga nan yana nan".. Zainab shigowa tayi tana Ambatar Yaya  dasauri Ya maida kofar ya rufe ya nufe ta riko ta yayi ya hada da jikin sa yana kokarin raba ta da rigar jikin ta Dasauri Zainab take kokarin raba jikin ta da nashi  Amma ta kasa kuka tasaka tare da samun nasara ta samu hannun sa duk da cikin duhu ne ta gantsara mishi cizo  dasauri ya sake ta Hanyar fita take nema ta rasa savoda duhu wajen fita ta kaima wani  karfe  karo sai bisa kanta  Qara tasaki  baki d'aya asibitin ya dauka da karar ta  Wani abu ne ya dinga mata yawo bisa kai tamkar A mafarki  tunanin ta da hankalin ta ke kokarin dawowa mata Mammyn ta kawai take hange a  idon ta Adaidai lokacin kuwa yakara kawo mata wata cafka "wallahi A yau sai na maida kwadayi na a kanki tamkar yadda Dr Ahmed ke mayarwa babu yadda zaayi ya hanani nima na d'ana  dora ta bisa gado yayi tare da yaga rigar jikin ta  kara tasaka mai mutukar firgita tare da wani karfi da Allah yabata babu inda yafada sau jikin bango sai jini kara ya saki daidai lokacin kuwa aka bud'e kofar dakin da karfi tare da kawo hasken wuta  hasken ya gauraye dakin   Wani dum Zainab taji daganan numfashin ta ya dauke  dasauri ya nufi wajen ta  dasauri "Mommy! gani yadda take dasauri ya yaye zanen gadon ya rufa mata dasauri ya nufi shi batare da ya dubi halin da yake ciki ba,... "Dama halin ka da ake ta fada a cikin asibtin nan hakane kana karyatawa halin akuyanci da kake kenan  duka ya dinga kai mishi ta ko ina jikin sa rike sa akayi hucin yake  jijiyon kansa duk sun fito bisa kansa  bisa wheel chair aka tura Zainab aka nufi wani dakin da ita..Inda Dr Ahmed yakasa aikata komai gani yake Dr Tanko ya cimma buri akan Zainab ... sai wasu ...ma'aikata akanta wadda haryanzu taki farfadowa duk irin taimakon da ake mata  amma tamkar gawa taki ko motsi, ji yayi andafa mishi "Am sorry Dr Ahmed"... d'agowa yayi kawai ya kalle shi  "munyi kokarin saita komai zata iya farfadowa kodayaushe  Amma Dr tanko babu babban maci amana kamar shi tabbas kuma zai kwashi abinda ya girba da hannun sa".. Dr Ahmed girgiza kai kawai yayi tare da miqewa ya nufi gadon da Zainab ke bisa tayi sambal! sai numfashin datake ja A hankali da taimakon Oxgen dake tare da ita,..

Naso yafi hakan yawa Wallahi ban lafiya ulcer+ Fever😭 Allah yabani lfy na ida muku na huta nima..🥺😞

#Hafsat Musa💖

A RASHIN SANI.. Where stories live. Discover now